
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 14
Dada ce tai saurin biyo bayan ta, tana dafe da ita harta gama kwara aman sannan ta debo ruwa ta wanke mata fuska, sannan ta d’aga ta zuwa d’aki.
Can kuyar dakin ta nufa da ita akan gado ta kwanta, sannan Dada ta fito ta gyara wajen tana cike da damuwa.
Itako Unaisa Koda ta kwanta tunani ne barkatai suka rufar mata, Wai Modibo aure zai kuma kenan, duk da cewa tasan babu wani alaka atsakanin su taji abun ya dameta sosai, duniyar ce taji duk babu dadi, wata zuciyar ce tace toh ke son shi kike ne?, idan ba sonshi kike ba mezai dame ki?
Yin wannan tunanin yasata tashi zaune, saidai duk da hakan jikinta babu dad’i, wayar ta ta dauko tana dannawa cikin rasa abunyi, kawai dan batason Dada ta ganta cikin damuwa.
Zuwa can Dada ta dawo ta zauna, ganin haka Unaisa ta shiga Kiran Ammi bayan sun gaisa ta Kira Afnan.
Hira suka taba sannan ta kashe wayar tare da fadin, ” Dada kibani key din can gidan intafi kafin Baba ya dawo.
Baba ai yazun ba wannan mgnr kuma, bazai koreki ba, duk ya sakko tunda yaga Modibo tsaye akan mu ya fara yan kame kame.
Sosai Unaisa taji haushin Baban ya kamata, dan haka ta dago tace nidai Duk da haka gara naje can Dada.
Toh ai mijin ki yace kar inbarki kije ko Ina, banda abun ki me zakije can ki yi?
Yamutsa fuska Unaisa tayi kokarin kawar da kanta ta fara dan Bata son Dada ta fahimci halin da take ciki.
Shiru sukayi tsayon lokaci sannan Dada tace, ” toh ya jikin naki?”
Dada Lafiyata lau
Toh yayi, dazon muna mgn amai ya taso miki, Unaisa ni ban dauka cewa wannan mgnr zata daga miki hankali ba, na dauka ko cikin mata uku yasaki kizo da hadu zaki gode ma Allah.
Nifa Dada Ba komai.
A’a, Unaisa da komai, aiba yau nake nake ba, idan Kika tada hankalin ki ita koma waccen uwargidan tasa tace me?
Kara kulewa Unaisa tayi saidai Bata son Dada ta gane dan haka ta sake cewa Dada nifa ba komai, Allah ya sanya aheri.
Ameen Dada ta fada.
Waya Unaisa ta cigaba da dannawa tsayon lokaci Dada na Satan kallon ta, itako Unaisa ta’ba wayar kawai take badan tanajin Dadin hakan ba.
Aje wayar tayi ta kwanta daga can taji wayarta nakara, hannu ta Mika ta dauka ganin sunan da Ke kan wayar taji wani sabon haushi ya kamata, sau uku ya Kira Bata dauka ba, sannan ya barshi hakan.
Misalin 08:00pm zazzabi ya rufe Unaisa, sosai take rawan sanyi saidai bata son Dada ta sani, dan haka ta rufa cikin Bargon Dada me laushi, daga cikin Bargon take hira da Dada har bacci ya dauke ta.
Can cikin baccin ta taji Dada na tashin ta tare da fadin, Ke!! zazzabi ne haka ajikin ki haka?
Cikin sauri Unaisa ta tashi ta zauna tare da taba jikin nata tana fadin, eh Dada Da Daddare ne yamin haka.
Kawar dakai Dada tayi sannan tace Modibo ne yana waje, yace da rana yata kira baki dauka ba.
Ban gani ba ta fad’a a takai ce.
Toh lallaba kije nace ya shigo yace a’a.
Dada kice nayi bacci.
A’a tashi maza.
Dada banda lafiya sanyi nake ji.
Idan kinje ki gaya masa saiya nemo miki magani.
Jimmm tayi zuwa can ta sakko da kafarta, batazo da hijab ba dan haka gyalen ta ta dauka ta fito.
Acikin motar ta hangesa, Yana zaune tare da kunna fitilar motar, wannan karon shi yada yazo, domin a mazaunin driver ta sameshi, gaban motar ta tsaya kallon ta yayi tare da fadin zagayo ki shigo.
Yadda yace din tayi, tana shiga motar kamshi ya daki hancin ta, wata leda ce agefen sa tare da lemo ahanun sa Yana kubar.
Zaman kusan minti 5 sannan yace Aunty Ina wuni.
Lafiya lau ta fada ahankali.
ledan gefen sa ya nuna mata tare da cewa bismilla.
Nakoshi.
Yadda tai saurin bashi amsa yasashi kallon ta, akwai alamar rawar sanyi a tattare da ita, kallonta yayi sosai sannan yace, naga kamar kina rawan sanyi ne Yaya dai.
Kawar dakai tayi can gefe.
meke damun ki?
Babu, ta fada a takaice.
Akwai, meyasa d’azon dana Kira baki dauka ba?
Ban gane bane.
Jimmm yayi sannan yace, amman Afnan tace min kunyi waya da Daren nan Ammi ma haka.
Shiru tayi tare da sunkuyar dakai tana wasa da hannun ta.
meye ke faru ne Umuhum kimin mgn Mana.
Babu ta fada idon ta akasa.
Akwai. ya fada ya fada Yana gyara zaman sa.
shiru gorin ya sake yi tsayon lakaci yana kallon ta zuwa can yace, ” Baxaki gaya min abun dake faruwa ba?
Babu nace.
Shiru ya sake yi tsayon lokaci, sannan yace toh shike nan Ina ke miki ciwo yanxun?
Batace kala ba tsayon lokaci, kawar da Kai yayi daga kallon ta tare da fadin shikenan, ga leda nan gaban ki dauka kije abun ki.
Cikin sauri ta bude motar tare da fadin nagode.
Zo Nan, ai baki dauka ba.
Tana d’an kwasa hannun ta tace ai nace nagode.
Wani irin kallo ya mata sama da kasa har ta shige gida.
Menene haka? ya tambayi kanshi Yana cigaba da kallon gidan sannan ya tashi motar yabar gurin.
Unaisa na shiga dakin gadon ta koma sosai takejin haushin Modibo akarkashin zuciyar ta.
Zuwa can Kiran waya ya shigo wayar Dada, dauka tayi tare da fadin toh acikin wayar.
Mikewa tayi ta bude kofa Modibo ne ya shigo dakin da Sallama abakin sa.
Cikin sauri Unaisa ta runtse Ido jin sallamar sa, ledojin hannun sa ya aje falon sannan ya mikawa Dada maganin Yana fadin, ga maganin ta nan naga kamar batajin dad’i.
Eh jikin ta da Zazzabi.
Toh ga magani nizan koma, har ya juya ya dawo da baya tare da fadin, amman Mama kinyi mgnr da ita ne ko?
Cikin daburcewa Dada tace a’a zatadai muyi ne.
Sanyi yaji cikin ransa, sosai yaji ya samu nutsuwa, inda ya fara tunanin kila canzawar tata nufinta bazata bishi bane goben, acikin ransa yake tunanin meye acikin wannan garin da har take nacewa zaman sa.
Besan yanayin nata ya dameshi ba saida yazo kwanciya bacci, Kiri Kiri baccin ya gagare sa, tashi yayi ya zauna, yadda take amsa masa daker kawai yake tunawa be ankaraba yaga ya dauki tsayon lokaci a zaune.
******
Unaisa ce zaune Kan sallaya bayan ta idar da sallah asubahi, Dada ma zaune gefenta da hijjabi jikin ta, waigawa tayi ta kalli Unaisa dake kokarin daura tagumi tace, ” Unaisa karki daura tagumin nan.
Cikin sauri ta gyara zamanta tare da kallon Dada tana fadin, ” ba tagumi nayi ba fah”
Toh naji, wai yau ni kike kokarin boyewa damuwar ki Unaisa?, wlh kinban Mamaki.
Dada me nayi?
Yanxun kawai dan Modibo zai yi aure saiki tada hankalin ki?, Ni ba tsammaci haka ba daga gare ki, idan kikama yaron nan haka baki masa adalci ba, domin tsananin kauna ya nuna miki, yaso tafiya dake Koda besan wacece keba, dana sa rigima kuma nace aure ne zai rabani dake, yace yaji ya gani, kawai sabo da Yana son yaga rayuwar ki ta inganta, besan kiba, ko fuskar ki be taba gani ba fa Unaisa, cikin gidan nan agaban ki na nemi na bude masa fuskar ki yace a’a, burin shi kawai kitashi ku tafi kawai, haba Unaisa tunda lokacin nafahimci kaunar kice kawai Allah ya saka masa.
Hawaye ne ya zubo ma Unaisa layi biyu tai saurin sa hannun ta ta share tare da kawar da fuskarta gefe tana fadin, ” nifa ba haka bane Dada”
Toh Yaya ne?, ai tun jiya dana gaya miki sakon shi hankalin ki ya tashi, ba laifi bane dan kinyi kishin sa, amman banda na tashin hankali, komai ya miki na bacin rai saiki duba baya.
Hawaye ta kuma Sharewa Dada nifa ba kishi bane, ba ruwana dashi, ina dad’ewa mani ban ganshi ba, kowa harkar shi yake.
Cike da Mamaki Dada tace, lallai Unaisa, ashe da Biri yasan ashana da mutanen kauye sun sha wuta, koda ba agidan sa kike ba, kina da mutunci a idon sa, ai jiya aikin sa ya kashe ya dauko ki musamman ya kawo ki nan, ki saki ranki, karki nuna mishi komai kijij na gaya miki.
Amsawa tayi sannan ta mike ta wanke fuskarta ta dawo ta zauna, ahankali ta fara sakin jikin ta har suka shiga hira ita da Dada.
Tsarabar da zata taho dashi Dada taita hadawa, sai misalin shabiyu na rana Modibo yazo, tuni Unaisa ta shirya cikin dogowar riga ta atamfa tayi kyau sosai, har cikin gidan ya shigo cikin shigan ta manyan kaya, tsunwa yayi ya gaida Dada sannan ya mike yana fadin, ta shirya kuwa?
Eh, Kai take jira tun dazon, juyawa tayi ta shiga kiran Unaisa, fitowa tayi suka hada Ido tai saurin gaidashi sannan ta dauki Jakarta, ficewa Modibo yayi ya zauna cikin motar.
Unaisa da Dada ne suka fito, cikin motar Unaisa ta zauna yayin da Dada da Modibo suke Kara yin sallama daga karshe taji Yana cewa Dada saikin iso mama.
Cikin sauri ta juya ta kalli Dada tace, zakizo ne Dada?
En kawai Dada tace mata, ahankali take cewa yaushe?
Insha Allahu nan da kwana 10.
Take taji bacin ranta ya dawo sabo kenan auren Modibon zatazo.
Dagowa tayi ta window motar tace Dada karkixo.
Ciki da takaici Dada tace toh naji, Allah ya tsare hanya.
Maida hankalin ta tayi cikin motar lokacin da taji motar ta fara tafiya, ajikin ta taji kallon ta yake dan haka tai saurin juyowa ta dube sa.
Wani irin kallo yake binta dashi wadda yazam mata bako agurin sa, betaba mata irin wannan kallon ba, dan haka ta shiga fargaba kodai Magaji ne.
Wannan dalilin yasata itama binsa da Ido.
Meyasa kikace mata karta zo?
Maido da nutsuwarta tayi sannan kawar da Fuskanta daga gare shi, kokari tausar zuciyarta take tare da gyara fuskan ta.
Ke!! Ji Mana, kina bude baki kina min mgn, nafi son ana fafatawa bana son shirun nan.
Wasa ta fara da hannun ta yayin da motar su ta hau Babban hanya tana kowarara gudu.
Ko baki gane ba, idan nace fafatawa Ina nufin Ina tambayan ki kina amsa min, ta hakan saina gane inda Kika dosa, In mutum yafika gona sai ka fishi da taki.
Lankwasa hannunta taitayi Bata ce komai ba, idon ta akan hannun ta, shima hannun nata yabi da kallo, tsayon lokaci.
Meye a hannun kike ta fama dankawasa shi?
Bakomai.
Be dauke idon sa akan hannun ba yace, nabama Mama sako ta gaya miki ta gaya miki ko?
Cikin sauri ta kawar da kanta gefe tare da fadin, ” eh Allah ya sanya alheri”
Amin, ya fada Yana cigaba da kallon ta, zuwa can taji ya sake cewa, me kike so Ina nufin me zan saya miki.
Bakomai.
Hannun ta ya kalla da hanr yanzun take lankwasa idon ta kasa yace bar lankwasa hannun Nan, gaya min me kike so, ko mene ki gaya min ?
Ni babu komai.
kallon ta yayi tsayon lokaci, itako Safna wani abu keta mata soya akirji, yayin da aduk lokacin da Modibo yai mata mgr take cen Yana Kara murdawa, sosai ta kosa ya daina mata mgn domin wani abu takeji Yana taso mata, tuni idonta ya kada yai jah, duk da tasan cewa baby soyayya a tsakanin su Bata san meyasa takejin kunan auren acikin ranta ba.
Bata ankara ba taga ya daga da inda take zaune ya dawo daf da ita har yana gogan jikin ta, karam taji ya rike hannun nata da har yanzun take lankawasawa, Rahma gaya min me kike so?, Safna tace mota take so ke kuma fah?
Kamar jira hawayenta suke suka kangaro kokarin kwace hannun take tare da fashewa da kuka, nika sakar min hannu na.
Sakinta yayi da saurin sa, tare da fadin, shikenan na sake miki hannun, me hannu, mgn ta kare, mata tacewa mijin ta shege, bakomai ai karamin goro yafi babban dutse.
Yanzun gaya min me kike so?
Cikin sauri ta kawar da kanta tare da fadin, abun da nake so?
Eh, abun da kike so?
Kasa kasa tace karka sake min mgn.
Jimmm yayi, tuni ya gama nazarin ta, tashi yayi tsama ya sake komawa dafda ita akaro na biyu tare da fadin, ” karna sake miki mgn shine abun da kike so d’in?
7 comments
Comments are closed.