
BAYA BA ZANI🥥🥥🥥🥥🥥🥥
By
Fadeela Lamido
Page 5
___________________________________
……….Jimm Abdullahi yayi cikin wani irin yanayi na rashin jin dadi, sannan yace toh, insha Allah zan kirata”
Sallama sukayi yayin da Dattijo ya dauki hanyar Lagos kamar yadda ya saba ko wanne lokaci”
Mamaki abun ke bashi waishi ne aka daurawa aure da Asma’u yariyar da ko kanta bata gama sani ba bare ta kulla da wani”
**************
Wayar Dattijo na sauka, ta Asma’u na shigowa wayar Abdullahi, haddace number sa take cikin kanta, besan kowaye ba dan haka yai sau dagawa”
Yaya Abdullahi?
Na’am Asma’u ” wayar waye kike kirana da ita?
Saida ta hadeye yawo masu dumin sannan tace Wai Anne ne ya kawo min waya harda kudi dan munafunci, cikin gida ya aiki dashi gaban Inna Kuma halin awaje zagi ya dinga dura min, Wai Alhaji Babban ne yace ya rareashe ni”
Hmmm kinaji ko Asma’u ba munafunci bane, iska ya fesar daga bakin sa sannan yace”
Ya kirani yanzun nan dashi na gama waya, cemin yayi in rareasheki in baki hakuri kibar kukan, Asma’u yayana mutun ne me saukin Kai ta wani bangaren yana zafi yafi wuta kuna sannan yana da saukin kai indai baka shiga harkarsa ba, Asma’u, kinsa me?, Ina bakin cikin abun da yashiga tsanin mu, da aca komai be shiga tsakanin muba aka aurawa Dattijo ke dana zuba ruwa akasa nasha ko afuska bazanta nuna damuwata va Dan ni ban samu ba Dattijo ya samu, Asma’u narasa inda zanshiga wannan abun yamin girma da yawa”
Yaya Abdullahi abun da yafaru yariga ya faru, ni ayanzun yayanka ne banson gani wlh ban son shi da gaske nake ba wasa ba, natsane shi shima ya tsanene umarnin baba kawai yake bi, Yaya Abdullahi so yake ka kwatar dakai akaini gurin shi yaci uwata haka yake zagin shi kullun”
Asma’u, komai ya kwance min, nabi rudun shaidan nafada aikin dana sani, wannan abu yamin yawa zuciyata zata fashe nasan duk daren dadewa mgnr nan saita fito, Yaya Dattijo bazai yafe Miki ba Asma’u nasan halinsa kwarai”
Nika dai Kira min sunan sa, gidansa nake tsoron zuwa amman bazan taba bari yazo min ba ballatana har yasan ya nake ciki”
Hmmm bazai yiwuba Asma’u aiba haka ake aure ba”
Naji toh yanzun kana ina?
Bana gari Asma’u nakebe kaina waje guda domin bason hayaniya”
Ya Abdullahi kana nufin kabar Amaryar ka ka tafi wani gari???
Toh ya zanyi Asma’u, Baba bece zai bawa kowa keba bare insan abun yi ya shammace ni Asma’u, naji dadin da Dattijo beyiwa Baba musu ba domin nasan hukuncin dayai niyyar yanke masa dazaran ya bijire masa”
Ni babu ruwana da wannan Yaya yanzun yaushe zaka dawo kadawo gida mana”
Bazan dawoba Asma’u, Ina bakin cikin ranar da Dattijo zaigane komai, akwai abun da baki sani ba Asma’u tsakanina da Dattijo iajin kunyar sa sosai yamin komai arayuwa”
Yaya Abdullahi dan Allah ka dawo gida”
Na maka Alkawari bazan gayawa kowa ba, Kuma bazan taba barinsa yazo kusa daniba bare har ya fahimci wani abu, haka zai gaji ya maidoni gida, kaga lokacin sai muyi auren mu, nasani shi kansa Anne bazai zo yace Wai yazo neman wani Abu guna ba”
Wani irin sanyi yaji jin tace zata gayawa kowa ba, amman yasan mawuyacin Abu ne mutum lafiyayye ya zauna dakamar Asma’u beji komai ba, koma dai menene yana rokon Allah ya rufa masu wannan asirin domin ko yaci amanar kowa cikin ahalin nan”
Shike nan Asma’u nagode amman zan rokeki abu daya, daga yau karki Kara kiran Dattijjo Arne”
Hawayen gefen idonta ta shere wlh ya Abdullahi bazan bari ba, dakansa yamin gargadin inbar kiran sunan sa idan takama zan fada dole zance masa Anne”
Katse kiran yayi jin tafara irin tsiwarta wadda ko wanni irin hali take ciki bata barin sa, kallon wayar yayi tare dayin wani dan murmushi wadda bekai zuciya ba yace”
Allah sarki ‘yar cinliga”
***************
Tunda Abdullahi ya kira Dattijo yace masa Asma’u tabar kukan be sake bintakantaba bare yaji Yaya take”
Yau shida Mansir ne zaune afalon Mansir din”
Umar yaushe Amarya zata iso?
Dimm yaji gabansa ya fadin sannan ya tuna fuskan Asma’u, tsaki yaja sannan yace”
Ni Ina ruwana, inda zasu gane dasun barta can”
Haba inace yanzun da aka riga aka daura auren zaka riki matarka kafa dade babu aure”
Tsaki yaja nifa masir mace bata gabana, meye shi auren?”
Hmmm Lallai Umar naka wasa ne koda yake ba laifin ka bane baka tabayi bane bare kaji abun da akeji”
Bantabayin aureba mansir, amman kana fitarwa Ina fitarwa, dan haka Babu abun da zaka nuna min🤷🏽♂️”
Bangane ba”
Mikewa Dattijo yayi yana cire butirin rigarsa yake fadin, zaka gane indan har muna tare”
🤷🏽♂️Ai shike nan, niwai Ina kowa maka yadda zakaji dadi ne”
Yanzun ma nace maka banjin dadi ne?
Murmushi Mansir yayi sannan yace”
Harna tuna ranar da nakai matar taka gidansu, naci harara, kanbu yariyar akwai tsiwa dagani mafadaciya ce,
Aini bata min haka, kaima fuska tagani, duk iskancin ta bata yinshi gabana, saidai tayishi bayan idona, yariyar bata da kunya akwai wani abun dayafi ban haushi tatrare da ita, nidai bawani kallonta nake ba, kallona da ita befi biyu zuwa uku ba amman nakula bata da kamun Kai”
Ban gane kamon Kai ba?
Kai Dattijo ya dafe, Ina nufin tana da rashin kunya”
Hmmm koma dai menene ai kace dai mata basa gaban ka nikuma nace karya kake”
Wlh da gaske nake, ni banda wani damuwa karshenta dai duk abu daya ne ake mawa kumana gaya maka dazon”
Ni vabu wani Abu da zaka nuna min, yadda kakejin ka haka nake jina”
Hmmm Umar bana gane mgnr ka🤷🏽♂️ oho maka idan ka mutu baka haihuba kaika sani nina wuce”
Ficewa yayi abinsa yana motarsa akan hanyarsa ta zuwa gida yana tunanin Umar, da alama da gaske mata basa gabansa, yayin da ya shiga tunanin wani irin mutum be Umar🤔
*Bayan wata daya*
Ai da kin gama jarabawa zamu rakaki gidan ya Dattijo”
Insha Allahu ahaka mgnr auren zata barbade”
Umma ce ta waigo ta kalli Asma’u datai wannan zancen sannan ta maida kanta tare da girgiza kai”
Baki da hankali yariya kodan kinga fin wata ya Dattijo bezo ba kike tunanin auren zai wargaje”
Aina naji ajikina Babu inda zani indai Anne zaizo garin nan da nufin tafiya dani insha Allahu wuntsulawa zaiyi ta inda baza iya tantanceshi ba tsakanin shi da motar tasa……
Runtse ido Umma tayi tare da kallon Maryam tace Maryam dan Allah ki daina daka ta Asma’u……….
*Mmn Yazeed*🖊