
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
🕊🕊🕊🕊🕊
_Storry & written_
By
Fadeela Lamido
4-5
✏Karfe 4:00pm suka isa gidan su salamatu dake cikin garin katsina, tana, rike da hannunn yarta Fatima,
salama tayi acikin rauna nanniyar murya.
wata dattijuwar mata ce ta amsa tare da fadin muryar wa nakeji kamar ta salame.
cikin sauri salamatu ta saki daniju ta rungume matar tana fadi nice dada.
itama matan kara matseta tayi cikin kuka tace
” yau Allah ya karbi addu,ar da na dade inayi shekara da shekaru, ta sake cewa me yasa kika tafi kika barmu haba salamatu baki kyauta min ba kin azaftar dani kinsamu cikin ma muyuyacin hali nida mahaifin Fatima, yasha wahala wajen neman ku.
kukan salamatu karuwa yayi, zamewa tayi ta duka kasa tace
” dada dan Allah ki yafemin ba ason
raina na aikata haka ba nayi ne dan na gujewa furucin yusuf dan idan na bashi fatima alokacin zan shiga wani hali kuma bansan ya rayuwar ta zata kasan ce a wajen dangin yusuf ba da suka dauki tsana suka daura min, sai kuma gashi wuyar da na gudar mata beyi tasiri ba dan ayanzu anlalata mata rayuwa cikin kuka ta zaiyanewa dada abinda ya faru.
lallashin ta dada ta shiga yi sannan ta mike ta dafa daniju dake zaune sai tsiyayar da hawaye take tace
” karki damu fatima insha Allahu Allah saiya saka miki kuma yabi miki hakkin ki da izinin allah”
itadai fatima batace komai ba illah share hawaye da take.
mikewa dada tayi ta hada ruwan zafi ta kai ban daki sannan ta dawo ta daga fatima da kanta tayiwa fatima wanka .
bayan sun fito dada ta kwance daurin kayan da suka taho dashi ta zabi me dan dama dama ta mikawa Fatima
sannan ta nemi guri ta zauna ta shiga tunanin lallai idan yusuf ya samu lbrn dawowar salame ba karamin farin ciki zaiyi ba domin kuwa ya dauki son duniya ya daura akan fatima.
*Tushen Labarin*
Alhj salisu asalin dan jahar katsina ne kuma shahararren dan kasuwa, zaiyi wuya alissafa yan kasuwa 5 ba asa sunan shi ba.
yana da mata 1 da yaranshi maza 2, kasancewan Allah be bashi haihuwa da yawa ba ya taso yana matukar kyaunan yaranshi 2 da Allah ya bashi kasim shine babba wanda ayanzon haka yana da aure yaranshi 3, sai yusuf wanda ya kasance mahaifin fatima.
itako salamatu mahaifiyar fatima, mahaifin ta ya kasance me gadi agidan alhj salisu dan haka lokacin da yasuf ya furta wa mahaifin shi yana son auren salame yaki amincewa.
acewarshi bazai taba bari dan shi ya auri yar me gadin gidan shi ba.
mahaiyar salamatu ta kasance bafulatana ce dan haka salamatu ta kwaso kamannin mahaifiyar ta.
shikuwa yusuf wani irin soyayya yake wa salame Wanda har takaiga kinjin maganar mahaifin shi
” lokacin da alhj salisu ya lura dan nashi yana da niyar nijire mishi sai ya yanke hukuncin koran baba megadi.
haka ko akayi malam bello ya shiga tashin hankali lokacin da me gidan nashi ya gayamai ya sallame shi.
kudi ya bashi masu yawa dan haka ya nemi wani dankaramin gida ya saya .
duk da haka yusuf be hakura ba saida ya bisu har gidan da suka koma
wasu mutane ya samu ya kaisu amatsayin yan uwan mahaifin shi suka nemar mai auren salamatu.
bayan an daura musu aure ta tare batare da sanin dagin shi ba.
bayan shekara daya ta haifiyar ta mace wadda yasa mata sunan mahaifiyar shi wato fatima fatima nada wata uku alhj salisu ya samu lbr dan haka ya dira gidan , yusuf yaji mamakin yadda akayi ya gano gidan
yayi mishi umarni da ya saki salame ko kuma ya sallama shi, cikin rawan baki yusuf ya saki salamatu yana kuka tana kuka suka rabu da goyon fatima abayan ta, gidan iyayenta ta nufa bayan wasu kwanaki alhj salisu da kansa yaje har gidan su ya jaddada musu dazaran Fatima ta isa yaye zasu karbeta dan haka salame ta daukki yar ta ta bar garin.
guduwa salamatu da ya tada hankalin family alhj salisu domin kuwa suna matukkar bukatan yara , shikowa yusuf yafi kowa gargiza dan haka har yanzo be kara maganar aure ba iyayen nashi ko sunyi mgn sungaji.
bayan salamatu ta isa kano acinkin wani akauye ana kiran sa mai giginya bata kara marmari komawa gida ba agidan me unguwa aka sauketa bayan wani lokaci ta samu mijin aure wato malam habu.
lokacin da ta aure malam habu tasame shi yana da uwar gidan shi me suna baraka tasha matukar wahala awajen baraka ita da yarta fatima zagi iri iri babu wanda ba,ayi musu ba ita ta Fara kira fatima da suna daniju saboda tsabar bakin cikin cikin da takeyi da ita kuma sai sunnan ya beta acikin kyauyen.
kazafi kuwa kullum cikinyin sa take
*Cigaban Labarin*
bayan fatima ta gama shiryawa direct gadon dada ta nufa ta kwanta tana mai bakin cikin abun da ya faru da ita.
sai dare malam ya shigo gida ya tararda abinda ya cire tsanmani woto salamatu da jikar shi fatima .
bayan kwana 2 dada ta kira salamatu bayan ta zauna tace
” nakiraki ne domin na fada miki shawaran da muka yanke da baban ki kuma dole ne ki daure ko ya miki dadi ko be miki ba”
baffan ki yace yau dinnan akai fatima gidan kakan ta, saboda idan suka samu lbrn dawowar ki batare da munfada musu ba zasu zargemu kuma dama kyawun da gidan uban sa.
ahankali ta bude baki tace shi kenan Allah yasa haka shine maffi alheri.
fitowa tayi ta leka dakin da fatima take taga sai hada kaya take, ahankali ta kira sunan ta ta dago ta kalleta tace
” karki dauke komai daya danganci kayan sakawa naga sai wani rawar jiki kikeyi”
turo baki fatima tayi sannan tace toh mama ba dole nayi rawar jiki ba, ban fah taba ganin babana ba kuma idan na tafi babu kaya wani kayan zan rinka sakawa.
murmushi mama tayi sannan tace fatima kenan ai wannan kayan naki ko goge kitchen din su bazasuyi dashi ba dan gida ne namasu hali, babanki kuwa harsai kingaji da ganin sa , dan nasan idan ya ganki bazai kuma bari kizo gurina ba, dan haka zanci gaba da miki andu,a Allah tsareki aduk inda kk
maganar dada sukaji dana fadin toh fatima fito mu tafi.
cikin sauri ta fito domin kuwa bakaramin kosawa tayi ba tana tafiya tana fadin mama na tafi
toh kawai salamatu ta iya furtawa zuwacen ta kira sunan fatima ta dawo ta tsaya tace gani
ahankali tace kicewa babanki inagaida shi
toh kwai tace tabi bayan dada aguje,
suna fita ta saki kuka me ban tausayi.
🕊🕊
Ummu Yazeed
9 comments