
BA LABARI BOOK 2
BY
Fadeela Lamido
Page 37
Sauke hannun ta tayi daga kugun ta yayin da ta shiga gyara dakin, sannun ahankali take yin komai, harta tagama dakin ya dauki Kamshi ko Ina, falon ta fita nan ma gyara shi tayi sosai nan danan gurin ya dauki kamshi, bayan ta gama Zama tayi afalon tana jiran shigowan shi, ta dade zaune shiru babu ko alamar sa.
Tunani ne ya fara zuwar mata, da alama ransa ne ya faci, tunda har ya gayawa Ammi, dad’ewar da yayi din ma duk fushi ne, tunaninta Kara zurfi yayi domin basan yadda zatayi ba idan ya shigo mata da fushi, tana tsaka da tunanin taji ana bude kofar, ta cikin gida a alama daga gurin Safna yake, tun kafin su hada Ido wani Abu ya tsaya mata a wuya, saidai laifin da tasan ta mishi ya danne kishin ta.
Tanajin sa ya fara takowa cikin falon, kasa dago Ido tayi ta dube shi sabo da fargaban batasan wanin irin fushi yayi ba, kokarin hada kalmar hakurin da zata bashi take yi taji muryan sa ya daki kunnen ta Yana fadin, ” amarsu bakya laifi ko…… Unaiss dan karasa min.
Dagowa tayi ta kalleshi kad’an yayin da taga fuskan shi cike da murmushi dan haka tai saurin juya mashi baya sannan ta shiga wasa da hannun ta.
Zama yayi ata bayan ta yayin da yasa hannun sa ya dafa kafadan ta Yana kokarin leka fuskanta yace,”daga gurin Ammi nake, nazo nan naga babu ke, kuma baki aje abincin ba bayan na miki Umarni kiyi haka d’in, dan haka kawai nayi fushi na wuce dakin Ammi abu na.
Yadda yake furta kalmar yasa Unaisa tayi dariya batare data shirya ba, shikuwa Kara daure fuska yayi sannan yace, ” dan kinga na sakko batare da an lallasheni ba kike min dariya.
Fuskan ta cike da Murmushi tace a’a.
Toh menene?
Kawar da kanta tayi tare da fadin, ” Kaine kake mgn kamar wani Baby.
Baby ne mana, hannun sa yasa ya juyo da ita suka kuskanci juna sannan yace, ” ni Baby kine ai Unaiss, Ina tsananin son kulawar ki, yau ji nake Kamar daren sallah, anya kuwa yau akwai bacci?
Kawar da kanta tayi cikin tunanin tare da fasa zancen sa, muryansa taji Yana fadin, ” Dan haka ma Ina ganiin yau fa Unaiss yau atsaye zamu kwana.
Nan danan taji ranta ya soma bacci dan haka tace, a’a
Cikin Ido ya kalleta tare da fadin bangane a’a ba.
Binta da kallo yayi Yana kallon yadda ta sauya lokaci guda, cikin ranta take fadin, jebishi yaje ya gama tsotse matar shi zai dawo ya wani cemin yana son kulawata, launin idonta ne ya fara canzawa, duk abun da take yana binta da Ido ganin idon ta na Tara ruwa yace, ” Karki sake ki bari hawaye ya sakko Kan fuskan ki.
Yana fadin haka ya juyar da kansa can gefe, cikin sauri Unaisa tasa hannun ta ta cire kwallar data taru a fuskan ta.
Batare daya kalleta ba yace, ” narasa irin ki Rahma, ke baki saki jikin ki Dani kin nuna min tsananin kyaunata dake cikin ranki ba, sannan ni kuma kin hana min in nuna miki yadda kike azuciya ta, dan Allah zan roke ki, ki aje tunanin komai a gefe ki mayar da hankalin ki akaina kawai, ki girmama matsayina agurin ki kawai, kamar yadda nima cikin zuciyata kowa gefen shi daban.
Juyowa yayi ya kalle ta, sannan yace naga kamar kina da mgn?
Can kasa kasa tace, dama haka ake yi?
Haka ake yin me?, ban gane me kike nufi ba?
Nima mgnr da kayi ne ban gane ba.
Shiyasa kema Kika min wadda bazan gane va?
Kawar da kanta tayi can gefe batare da tace komai ba.
Toh shikenan, ki fad’a duk abun dake baki gane ba zan fahimtar dake.
Shiru tayi dan haka ya sake cewa Inajin ki, duk abun dake cikin ki fada hakan zaifi min dad’i.
Cewa kayi in maida hankalina akan ka kawai…
Shiru tayi Bata iya karasawa ba Dan haka yace inajin ki.
Kai kuma sai kace wai acikin zuciyar ka kowa gefen shi daban…
Tunda ta fara mgn yake son yin dariya daurewa yai tayi, amman zuwa yanzun ya kasa dannewa darawa yayi harta dago ta kalle shi sannan ya jawota jikin shi Yana sunbatan kanta tare da kara kankameta ajikin shi Kamar zai maidata cikin kirjin sa, sauke ajiyan zuciya yake tare da kara sunmbatanta yana Lumshe idon yace, I love you so much Unaisss , Ina tsananin kaunar ki har bansan iyaka ba, kiyi hakuri ki kwanatar da hankalin ki karki tunzurani inyi kalamin da vasu dace ba.
Kayi ta fada kasa kasa.
A’a bazanyi ba Rahma, akwai alamun dake nafara aure da rike min wuya zaki yi, ki dan bani hankalin ki, abun da yasa nace miki haka, ke macece, nikuma na miji ne wadda Allah yabawa daman aje mace sama da daya a karkashin sa, kuma kowacce matsayin ta daban…
Kowacce gefe ta daban?, wa kafi so to?
Cikin sauri ya kalleta Dan me tsammaci jin wannan tambayar daga bakin Unaisa ba.
Mikewa yayi tare da fadin, mubar wannan mgnr Rahma tashi ki bani abinci.
Badan tana son abar mgnr ba tace anan zan kawo?
Amsa mata yayi da eh, dan haka ta mike, bin bayanta yayi da kallo Yana me yaba surarta cikin zuciyar shi tare da gode ma Allah daya mallaka Masa ita amatsayin matar sa ta aure, hakika Allah me hikima ne, tunawa da irin rayuwar Unaisa ta baya sannan ya kalleta a yanzun yayi murmushi a daidai lokacin data ajiye abincin agaban shi yake fadin, Wai wacece wannan?
Cikin sauri ta kalleshi yayin da taga Yana mata kallon kasan Ido Yana murmushi.
Waigawa tayi ta kalli gefen ta dama da hagu sannan wace, ” wacce?
Ke! ya bata amsa yana kashe Ido.
Murmushi tayi da sauri tare da fadin, ” Wai ni?
Eh ke fah.
Fuskan ta dauke da Murmushi tana zuba abincin tace, Unaisa ce.
Unaisan wa?l
Unaisan Dada?
Jiki kawai, kod’an Kara babu, abincin data ajiye agaban shi ya kalla sannan ya dauki cukali tare da fadin, yau zanci jagwalgwalon ki….
Kamar jiransa take tace idan har aka iya cin ai ya wuce jagwalgwalon, kaci kaji, saidai ko kace magin baji maka ba?
Yana kallon cikin idon ta yace kinsan magin beji ba kenan?
A’a ni haka shine daidai agurina kaci kaji.
Diban Abincin yayi ya Kai bakin shi, taunawa ya farayi tare da lumshe Ido, zuwa can ya bude idon shi tare da liban wani yasa cikin bakin shi yana fadin aini komai yayi min daidai Unaisss, meyasa da kikace kila bazai ji min ba?
Can kasa kasa tace, naga ka saba cin me magin ne.
Kwarewa yaso yi, dan haka yai saurin daukan kofin dake gaban shi ya sha sannanyan lemun dake cikin sannan ya bude idon sa akanta yana gyaran murya tare da fadin, ” ke ko? haka kike ashe?
Kawar dakai tayi domin duk tunanin ta be gane inda ta nufa ba, jin sa tayi ya sake fadin, anya kuwa ba kishi bane ya rufe miki ido?
Kara kawar da kanta tayi Bata iya cewa komai ba, Modibo ma abincin sa yaitaci yayim da yake Satan kallon ta Yana murmushi.
Tas ya cinye abincin tare da yiwa Allah Godiya, bayan ya gama kwashe kayan tayi yayin da yake janta da hira.
Misalin Shadaya yace tashi muje daki inason inyi wanka.
Mikewa tayi hannun ta cikin nashi suka nufi dakin, cikin kankanin lokaci yayi wanka ya shirya cikin kayan bacci, itama Unaisa ji tayi tason yin wanka duk da cewa tayi kafin da shigo Amman aikin da tayi adakin yasa taji tason karawa dan haka ta nufi toilet.
Sosai ransa yai fari ganin ta dan saki jikin ta saidai yana ganin zafij kishin Unaisa sosai wadda yake hana Masa jin dadi domin ya kula tana yawan jin zafin Safna.
Wani irin tunani ne ya same shi inama ace ita nafara haduwa da ita, bansan wani soyayya ba sai akan ta, farin cikin da nake ciki ayanzun bana tunanin abaya na taba shigar sa, gani nake Kamar da ni rabi ne yanzun ne nacika daya, inajin cikakkiyar kwanciyar hankali tare dajin wani irin farinciki mara misaltuwa, ganin ta nake tamkar wata furen fulawar wadda kallonta yake haifar min da tarin tsuwa, hakika auren soyayya daban yake, da Ina da yadda zanyi in matar da Ita Safna domin ta kwantar da hankalin ta da nayi, tuna Safna yasa yaji wani karin tausayin ta ya darsu a ransa, musamma yadda ta kwantar da hankalin ta sai Dan kishi kadan wadda ba’a raba mace dashi, afili yace, Allah kabani ikon yin adalci a tsakanin, Allah Kaine ka kaddara min auren Safna sannan ka kaddara min soyayya Rahma acikin zuciyata fiye da kowacce ‘ya mace a dumiya, Allah Ina rokon ka da sunayen ka kyawawa kabani ikon yin adalci a tsakanin su.
Jin ana bude kofar yasa shi ya farga, shiru yayi da bakin shi Yana kallon ta ta shiga shiryawa sannan, mikewa yayi ya dauko wasu zafafan kayan bacci sabi fil ya Mika mata.
Akwai sanyi.
Idan kinsa saiki shiga bargo.
Kokarin yin mgn take yace raina zai bacci fa, idan kuma kinason in yi fushi dake ne to kiyi yadda kike so…
Daukan kayan tayi tasa batare da tace komai ba, bayan ta gama kasa zuwa gadon tayi, ahankali yace kizo ki kwanta Mana.
Takawa ta fara yi Kamar me sadan harta isa can gefen sa ta kwanta, bayan kusan minti 5 tajishi ya matso ya rungumeta ajiki tare da Kai mata sumba wadda tasa jikinta amsawa lokaci daya.
Cikin kunnenta yake rada mata, yau karatu zamu yi.
Wani sanyi taji dan haka ta fara kokarin tashi zaune gara akwana karatun da akwana yin wannan abun dan ta kula shi Moddibo ko gajiya bayayi.
Ina zaki ya fada yana kara shige mata.
Bagace karatu zamuyi ba?
Eh, amman basai kin tashi ba akwance zamu yi.
Komawa tayi ta kwanta tare da fadin to.
Yauwa kanwata, ki saki jikin ki, nasan ke sabon shiga ce a wannan harkar koba haka ba?
Kanta ta d’aga Masa batare data fahimci inda ya nufa ba.
Koda yake ma ai kin fara azama yar gari ko?
Wannan karon ma eh tace.
Dan haka yau zan dauraki a akan a bun da baki gane ba, amman saikin min alkawarin duk abun da nace kiyi Zaki yi.
Tureshi ta fara tare da fadin, nidai Allah a’a bazan yi ba wayo zaka min.
Kara rokota yayi Yana fadin, ba zancen wayo bani, karatu zamu yi, nasan kina tunanin zan tabaki ne, a’a yau ba wannan kawai zan koyar dake wani Abu ne.
Toh naji gaya min?
Ai Baki min alkawarin ba”
Nayi toh.
Duk abun da nace kiyi zakiyi?
Eh
Yauwa koke fa, kinsan menene?
9 comments