Advertisements

Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 41

Posted by

BA LABARI BOOK

 

Advertisements

BA LABARI BOOK 2
BY
Fadeela Lamido

Page 41

Kutsawa Ammi tayi zuwa cikin dakin har gaban gadon da Yadikko take yayin da ta samu tsohowar rike da hannun Yadikko yayin da yadikkon ke kwance hawaye nabin gefen idon ta.

Advertisements

  Bayan tsohowar tasake hannun Yadikko ne suka kalli juna da Ammi cikin sauri tsohowar ta sake fuskan ta tare da fadin, Hajiya Halima?

   Hade fuska Ammi tayi wajen fadin ina Moh’d?

Moh’d baya nan, amman idan ya dawo zamuzo tare.

Advertisements

    Ai Hajiya baza mu jira shi sai yazo ba, muna son musan inda yake, shekara da shekaru ya tafi ya barmu jikin jimami da tashim hankali, shine Sanadin ciwon ta, tunda ya dauki yaron ya tafi yau ciwo gobe lafiya, idan ya bari muka rasa ta wlh bazamu yafe mishi ba, ba itama mu kanmu  kullum cikin zullumi muke, Bama mu ba har ya’yan mu ya dauki alhakin su, Suraj ta nuna tare da Modibo taci gaba da fadin, ” wa dan nan yaran gantali sukaita yi cikin Sudan da kewayen ta, amman basu samu Moh’d ba, daker sukace sun samu ki, kin kuma ce be kai miki yaro ba, sannan kuma babban tashin hankalin da ya kara baibaye mu kenan, jin ku kanku baku san ina yakai yaron ba.

    Dan danan tsohowar ta hade rai, tare da fadin, “Kuyi hakuri, Hajiya Halima, Moh’d murdade ne, ya fita daban cikin ‘ya’yana, ga ‘yan uwan shi nan gaban ku, hakuri kawai muke dashi, befi shekara biyar ba da ya fara waiwayen gida, shima saida na tsayo wajen rokon Allah ya karkato min da hankalin shi ya dawo gida sannan ya fara waiwayen mu, bansan ina ma yaron yake ba bantaba ganin shi ba, Allah shine shaida ta, lokacin da ya tashi zuwa ya taho da iyalin shi gaba daya, na tambaye shi ina Fatima, yace min Fatima babu, nace bangane babu ba, yace min rabuwa muka yi, lokacin nakira Allah sannan na kalli Moh’d nace kayi arasar matar kirki, ashe shiyasa kabar zuwa gida, tunda ya tafi kuma be sake zuwa ba saidai muna waya kuma awaccen lokacin fushi yasani nabarshi shida ‘ya’yan shi banne mi su ba, sai lokacin da yaran nan suka zo, nata kiran shi babu shi a iska, sai daga baya na same shi nace Ina yaron Fatima?  wlh saikiyi mamaki amsan da ya bani, inda yake shiga banan yake fita ba, daker na iya daurewa na tambayi sunan shi yace min sunan sa Umar tundaga ranar ban sake mgn ba domin na kula baya neman albarka ta, amman ina saka mishi albarkacin ya’yan shi.

    Cike da takaici Ammi tace toh wai mu memukawa Moh’d da har muka cancanci wannan hukuncin daga gareshi, akan shi aka fara rabuwan aure?

   Son zuciya ne kawai Hajiya Halima irin nashi.

  Modibo ne yace toh mudai yanxun a bamu no tasa zamu nemesa da kanmu.

  Number tsowar tabawa Modibo tare da fadin a yadda yace min yanxun yana Sudan mukuma yanxun muna Kano da zama ne.

     Dahaka matar tayi sallama sannan suka fito yayin da Ammi ma ta amsa Tata number tare da biyo bayan su tana fadin mungode.

   Wani daga cikin samarin ne yaja baya cikin tsananin Mamaki yake tsaye cak, Suraj ne yabishi da kallo yana kallon Abun da yake kallo tare fadin Malam yaya ne?

   A daidai lokacin mutumin ya waigo cikin daga murya yace Mamman!

    Juyowa tayi tsohuwar tayi tare da amsawa.

   Zo ki gani, ya fada yana komawa da baya.

   Itama Tsohowar tahowa tayi yayin da saurayin  ya isa gaban Unaisa yana fadin kallah.

   Ido tsohowar ta zubawa Unaisa tana fadin, ikon Allah, wannan yariyar tana tsanani  kama da Fanan.

   Cikin murmushi Ammi tace haka daman Allah yake ikon shi wannan ‘yata ce sunan ta Rahma.

   Masha Allah tshowar ta fada sannan ta dafa kan Rahma tace Allah ya miki albarka.

   Saurayin ne ya taho Yana gyara waya cikin shirin yin hoto da Unaisa bayan ya tsaya a gefenta.

   Murya sukaji Kamar daga sama ana fadin, karka soma.

   Dagowa yayi ya kalli Modibo dake tsaye hannun sa cikin aljihu yace, Ina son ne in nunawa Kanwata.

   Eh shine nikuma nace maka matar Aure ce.

   Cikin sauri ya matsa agurin tare da Bama Modibo hakuri sannan suka wuce yayin da Ammi ta bisu.

    Modibo kuwa Hararan Unaisa yayi sannan ya koma cikin daki dama ita Safna bakin na fita ta koma kusa da Mijin ta.

  Itako Unaisa tsaye tayi ita daya a gurin saida Ammi ta dawo ta miki mata hannu yayin da tai saurin saka nata suka shiga cikin dakin.

    Su Ammi na shigowa dakin ran Safna ya ɓaci, domin ta kulawa da irin kulawa da Ammi take bawa Unaisa.

   Shikuwa Modibo dadi yaji sosai ganin kamar ta saki jikin ta duk inda Ammi ta cire kafarta nan take maida tata yayin da jakar Ammi ke rike a hannun ta.

     Suraj da Modibo basu jima ba suka wuce aiki, yayi  da Ammi taita rarrashin Yadikko tare da ce mata tayi kwari da jikin ta insha Allahu ta kusa ganin d’an ta, yayin da Ammi ta kara da cewa idan kin kwantar da hankali ki ne kawai zaki iya ganin d’a ki, idan ko kinki ciwo ya kashe ki.

   Wannan mgnr ta Ammi sosai take karawa Yadikko karfim hali.

     Sai Yamma Modibo ya dawo gaidasu Ammi yayi sannan yacewa Safna tazo suje gida.

  Mikewa tayi ta bishi har yakai kofar ya juyo yacewa Unaisa, kema kizo muje gida mana.

     Cikin sauri ta sunkuyar da kanta kasa dan haka ya kara cewa kinji?

   Ai ni da Ammi mukazo, zamu taho tare.

   Shikenan ya fada sannan ya juya ya fita.

   Sai dare suka dawo gida ita da Ammi washegari da Ammi ta shirya zata koma Asibitin tacewa Unaisa ke kuma saiki koma dakin ki.

   Ammi bayau zan koma ba.

Banson musu Rahma, ki koma dakin ki karki zama sauna mara wayau, yau kwanan ki biyu anan kece da girki kije tun wuri ki fara shiri.

   Amma toh ai fita suke tare ai nima muje tare gidan shiru yake min.

  Yau bazai fita da itaba nasani, ki koyi zama adakin ki, idan kin gaji da rana haka kina iya zuwa nan kiyi hirar ki.

       Amsawa tayi badan ranta yaso ba .

  Atare suka fito da Ammi yayin da Ammi ta shiga Mota ita kuma ta bude party dinta ta shiga, ko zama batayi ba ta fara gyare gare bayan ta gama ta koma part din Modibo gyarawa tayi tsasss sannan ta fita ta koma nata.

     Wanka tayi ta kwanta.

                ********

Ana yin Sallah Mangariba Modibo ya dawo gida, afalon shi ya same ta dan haka wani farin ciki ya baibaye shi hannun shi ya ware mata dan haka ta mike ahankali ta shiga jikin sa yayin da ya maida hannun ya rufe, tsayon lokaci ya dauka yana rungume da ita zuwa can ya sunbace ta sannan ya kwantar da ita a ƙafan sa tare da fara takawa zuwa cikin dakin.

   Kara rungume ta yayi bayan sun shiga sannan ya shiga shafa jikin ta tare da tsotse bakin ta kamar wadda ya dawo da matsanancin yunwa.

   Tsayon lokaci suka dauka yayin da ƙafafuwan su ya gaza daukan su, tsintan kansu sukayi kawai a Gado cikin rububin junana su kamar wad’anda suka shekara basu hadu ba, da alama duk basa cikin hayyacin su, sosai suke cikin farin ciki da nishadi mara misaltuwa, saidai yana zuwa gare ta ta fara koke koke wadda ke karawa Modibo karsashi dan haka be saketa ba har saida ya nutsu.

    Ya dade kwance ajikin ta yana maida ajiyan zuciya, jin kiran Sallah isha’i yasashi mekewa cikin sauri yayi wanka ya fito gudu gudu ya shirya ya wuce masallaci.

     Lokacin da ya wuce Unaisa na wanka koda ta fito taga baya nan tasan masallaci ya wuce, gaba daya ji tayi kunyan sa takeji kamar ta boye kafin ya dawo, batasan meya d’ebeta ba harta dinga taya shi, sallah tayi bayan ta idar ta koma bakin gadon ta zauna tana tuna Modibo alokacin data fara ganin sa rike da Sandan karfe sa guda biyu wadda da suke sakale a hakarKarin shi mutum kamilallae jajurtace ashe duk ya iya irin wadann abubuwan, ashe shima bashi da d’abi’a.

   Idan ka Ganshi da farko saika dauka bazai iya ma rugumar mace ba sabo da tsare gida tare da kame mutuncin sa, amman yanzun saikaji shi ya rikice yana zuba sambatu, murmushi tayi sabo da irin sabatun da tajisa yanayi yau, yanzun kuma idan ya dawo sai kaga kamar bashi bane ba.

     Jin Turo kofar sa yasata saurin dauke kanta, zama yayi a gefen ta tare da aje wata leda a tsakiyar su yana fadin”

   Gashi ki adana, hijjabai ne ki ringa sawa in zaki fita, naga wani yana son ya maidani wawa, kawai yaga yar kyakkyawar yariya waiwani dan ya raina min hankali zaice wani kinyi kama da yar uwan shi.

  Dariya ne ya kwace mata sabo da yadda yake furta mgnr.

   Au dariya ma na baki, rainin hankali ne bana, dan haka gashi nan harda irin wannan abun da kike boye fuskan ki dashi ada kicigaba da sawa kijin.

   Kaita daga sannan tace nagode.

Yana kallon fukanta yace, babu godiya tsakanin mu, sannan nakira Afnan jiya munyi mgn da ita, naji abun da ya fata miki rai, abun da nake so dake shine dan Allah ki ringa kokari kina tattauna matsalar ki dani, ki daina yin irin wannan abun ta yadda kowa sai yaji mu, kowa sai yasan halin da Muke ciki, bazan boye miki ba raina ya bacci sosai musamman da naji wai gidan Afnan kikaje, Haba Rahma, saikace baki da hankali, Afnan ba Kanwata ce, shekaru ne masu yawa a tsakanin mu, sai dai nagode ma Allah da mijin ta beji wannan mgnr ba, karamin yaro ne Kabir, sai yaga ko sati biyu baki hada ba kin fara yaji, shikuma yana rike da tasa.

  Aini bafa yaji nayi ba.

  Toh gaya min meye sunan sa, ?

   Ni kawai haushi naji naje gurin ta muyi mgn.

  Kin tabayi fita ne na miki izzani?

   a’a.

  Shiru yayi yana kallon ta zuwa can yace, ki dinga kokari kina dausan zuciyar ki idan ta bijuro miki, laifin nan bani na miki ba, ai saiki bari idan na dawo ni ki gaya min ba kisa kafa ki fita ba.

  Can kasa kasa tace kayi hakuri to.

  Nayi ai, kuma kema kiyi hakuri tunda naji harda nawa laifin zan gyara kinji?

    Kanta ta daga yayin da ya sake cewa itama Safna nace mata karta sake daga min waya  kuma wanene zai kirani kuwa abarmin innazo nagani kawai ko?

   kanta ta daga tare da kawar da kanta, kanta na kasa taji yace, ” ina wayar ki?

    Gata nan, hannun ta ta dago tana nuna masa, kallon wayar yayi sannan yace toh ki kirani.

     Kamar yadda yace haka tayi, wayar sa na fara kara ya dago ta yana fadin toh kalla ki gani.

    Fuskan wayar ta kalla inda Taga sunan daya sa mata na yawo akan wayar *_Maganin zugi❤️_* dan haka tai saurin lumshe ido.

   Muryasa taji yana fadin, da Rahma ne akai amman tun washegari ranar da kika tare na maidashi haka, ki sani kina da mahimmanci sosai a rayuwata ina ganin banyi kuskure ba idan nace ke rabi nace.

      Iri wannan kalamin yaita gaya mata dan haka taji ta samu nutsuwa sosai, tundaga wannan ranar mawuyacin abu ne ya kira sunan Safna idan suna zaune tare sa’anan kuma suna dadewa ma basu hado da Safna ba, kwanan Ammi shidda aka sallame ta a asibiti, bayan sati Daya kuma aka daura auren Suraj da Sumayya yariyar da taita masa yawo da hankali.

     Duk hidima bikin da akayi Unaisa suna tare da Afnan yayin da Modibo yaki yadda ya tafi da ko ɗaya, cewa yayi ai duk sunsan hanya, dan haka Rahma suke tafiya dare da Ammi, da su je gidan Yadikko kuma sai su hadu da Afnan, itako Safna da motar ta take tafiya.

            Bayan wata Uku

  Sosai Rahma suke shiri da Sumayya matar Suraj, dalilin hakan yasa Suraj din yabar kyaran ta kamar yadda yake yi ada, sosai Suraj din ke kawo Sumayya haka itama Modibo na yawan kaita gidan, saidai bayan sun cika wata Uku Suraj din ya tsoro da wasu halaye na wulakanta Sumayya koda yaushe cikin masifa, ga rashin dawowa gida da wuri.

    Duk wani shawara nata da Unaisa take tattaunawa dan yanzun ma duk halin da ake ciki Unaisa ta sani daurewa take kawai tana bata shawarwari duk da cewa ranta na abaci da abun Suraj din kema Sumayya.

     Yauma kamar kullum Sumayya ce tazo bayan fita Modibo, zama tayi yayin da Unaisa ta shiga yi mata sannu da zuwa saidai bata iya amsawa illa hawaye kawai da take sharewa.

   Cikin tausaya wa Unaisa ta zauna a gefen ta tare da tambaye ta me ya faru.

  Hawaye Sumayya ta share tare da fadin, ” Rahma ashe Suraj duk wannan wulakancin da yake min aure zai kara har an gama komai yana gaya min wai sati Uku.

   Daukewa  numshi ne ya samu Unaisa na tsayon lokaci, kafin ya dawo, zufa ya fara keto mata cikin tsanin tashi hankali tace wasa yake miki?

   Bawasa bane Rahma wlh da gaske ne, jibini Rahma wataba Uku da aure duk na lalace na fita hayyaci na, inda kikasan auren kiyayya mukayi bana soyayya ba.

    Amman kuwa indai aure Suraj zaiyi kuwa shikenan na tsane shi menene haka?

   Hmmm nidai banyi dacen miji ba, ki gode ma Allah Rahma kina zaune da mijin ki kullum kara kau kike yi, miki ina dad’a jemewa.

    Hawaye Rahma ta fara sharewa cikin tsananin takaici, ganin inda Rahma ke kuka yasa Sumayya ta shiga bata hakuri har amman harta tashi tafiya bata bari ba.

                        *****

   Abba gani, Ammi tace min kana son gani na.

   Eh inason zamuyi mgn, gefen da ya nuna masa tare da fadin matso nan kusa dani.

     Daf da Abba ya zauna sannan Abba ya dube shi yace, ” Yau zan isar da sakon  Baba, tun bayan auren ka wata wata biyu Baba ke bani sako ina kin sanar wa sabo da ganin rashin dacewar hakan da nake yi, Amman jiya ya kirani cikin fushi yana ta fada, kuyi hakuri dashi kunsan wani lokacin harda girma da ya kamashi, kuma na zauna agaban shi bayan gaisuwa mgn ta gaba takace kullum yana tambaya wai shiru har yanzun cikin iyalin ka babu wadda ya samu karuwa, kullum amsa daya nake bashi cewa bani da wani labari akan hakan toh yanzun dai a takaice yace ka kwashi matan ka da kai kanka kuke gurin likitan sa gobe gobe nan.

    Murmushi Modibo yayi tare da kallon Abba yana fadin,  Abba ka share shi kawai.

      A’a baza’ayi haka ba, Gara kaje din ai ba wani abu bane, nina baka Umarni.

     Amsawa kawai yayi badan ransa yaso ba sannan ya mike ya fita.

      Yana tafe yana jinjina karfin hali irin na tsohon kakan nasu, kai tsaye part dinsa ya nufa saidai Baba Unaisa aciki kamar yadda yasa rai zai ganta adakin sa.

    Abinci kawai ya gani dan haka ya fara kiranta a waya ganin bata dauka ba ya nufi dakin ta.

       Can tsakiyar gadon ya hangeta tayi rufda ciki, dan haka ya tsaya bakin gadon ya kira sunan ta, can kasa ta amsa dan haka yace taso.

   Tasowa tayi idonta jawur kallo ya bita dashi tare da fadi, ” menene ya faru?

     Bakomai.

   Zama yayi agefen gadon can kasa yajiyo muryanta tana fadin, wai da gaske Suraj zai kara aure?

   Batare da yajuyo ya kalleta ba yace,  “eh har ta gaya miki kenan?

   Amman shine kabar shi duka fa wata Sumayya uku shine har ya gaji da ita.

  Injiwa ya gaya miki ya gaji da ita?, au wato tazo ta gaya miki ke kuma da kika fita hauka kika zauna kina kuka ke za’ama kishiyar ne!!?

   Yadda yai mgnr cikin fushi yasata fara share hawaye, kallon ya gama kare mata sannan yace wuce muje ki bani abinci.

    Da saurin ta ta wuce dan haka yai tsaye yana kallon ta harta kule.

   Kafin ya shigo harta aje masa komai ta wuce dakin sa ta kwanta.

   Zama yayi yaci abincin sa sannan ya wuce dakin inda ya sameta ta cure guri daya, sanin halin ta da yayi yasashi yaki tanka mata kwanciya kawai yayi yana jinya har gari ya waye batayi wani baccin kirki ba.

       Washegari tun da Asuba ya gaya mata ta shirya zasu asibiti amsawa kawai tayi yayin data shiya cikin dogon hijjabi da ni’kabi kamar yadda yake so.

     Shiga yayi cikin mayyan kaya da hular da aka zagayeta ta karamin rawani sannan ya juya yana fadin muje.

    Bayan sa ta biyo saidai tana fitowa ta hangi Suraj zaune agaban motar yayin da ta hangi Safna abayan mota.

   Cikin ranta tace kenan dasu zamu asibitin, yau zamuyi irin zaman da bamu tabayi ba nida Safna, domin tunda take basu taba shiga motar Modibo tare da Safna ba.

   Ahankali ta fara takawa zuwa gurin motar idonta cikin ni’kabi saidai kana iya hankan inda kawar idonta yai jawur  ta gefe kuma ya ɗan tasa…

9 comments

  1. Pingback: my profile
  2. You’re so awesome! I don’t suppose I’ve read through anything like this before.
    So nice to discover someone with a few unique
    thoughts on this subject matter. Really.. thanks for starting
    this up. This site is one thing that is required on the web, someone with a bit
    of originality!

  3. First of all I want to say awesome blog!
    I had a quick question which I’d like to ask if
    you do not mind. I was interested to find out how you center yourself and
    clear your mind before writing. I’ve had a hard time clearing my thoughts in getting my ideas out there.

    I do take pleasure in writing however it just
    seems like the first 10 to 15 minutes are usually wasted just trying to figure out how to begin. Any ideas or hints?
    Cheers!

  4. Awesome blog! Do you have any suggestions for aspiring writers?
    I’m planning to start my own website soon but I’m a little lost on everything.
    Would you suggest starting with a free platform like WordPress or go for
    a paid option? There are so many options out there that I’m completely confused ..
    Any tips? Kudos!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *