Advertisements
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 43
Toh duk naji abun da kikace, amman ai kinsan ina iyaka bakin kokarina ko?
Ni bawani nan Momy, dacen kinfi sona, yazun komai ya jagule banajin dadin rayuwa ta.
Advertisements
Au haka kikace, toh shikenan, nagode amman babu inda zanzo, idan kin mutun Allah yaji kanki, daman kowa ma ita yake jira.
Daga haka Momy ta katse kiran yayin da Safna taita kiranta taji shiru bata dauka ba, rasa inda zata saka ranta tayi, gashi da Momy kadai take shawara gashi zuciyarsa na mata radadi ta rasa wadda zata fadamawa.
Shigowa Modibo yasata saurin juyowa ta kalleshi, ganin shine ta fara share hawayen tare da kokarin gyara Fuskan ta.
Advertisements
Zama yayi gefen ta sannan yace, ” Kuka kike yi??
Kasa mgn tayi domin ji tayi kamar an sosa mata inda yake mata kaika yi, wani hawaye ne ya sake sakkowa layi biyu tasa hannun ta ta sake sharewa.
Safna me yayi zafi haka?
Bakomai Hamma kaina ne yake min ciwo.
Jimmm yayi tsayon lokaci sannan yace, nagane, amman banji dadin yadda da same ki ba, nasan Zaki iyajin wani iri shiyasa ma nabiyo ki dan in kara kwantar miki da hankali, amman abun da ya ban mamaki saina samu kina kuka, abun har yakai haka kenan?, Safnan wannan wacce irin soyayya ce da har abun farin ciki zai sake ni ki zauna kina kuka?.
Sunkuyar da kanta tayi yayin da wani hawayen ya sake zobo mata.
Safna ance fa lafiyar ki lau, baki da wata matsala, wannan ai abun muyi farin ciki ne tunda da wasu ma zato suke nine banda lafiya….
Ai yanzun tunda kasan kai lafiyar ka lau kaga nice da matsalar kenan, yanxun kawai ka sake ni ina ga zaifi, Safna ta fada tana share hawaye.
In sake ki?,
Eh”
Toh yanzun kuwa zamu samu matsala, dan ni banson iskanci kinji ko?, kina bakin ciki dayin Allah ne, da kike cewa ni banda matsala ke ɗin ma ai ance lafiyar ki lau, wata kila lokacin ne kawai beyi ba, kinsan komai da lokacin sa, kuma tunda muke dake nataba nuna miki rashin haihuwar ya dame ni ne?
A’a, shiyasa ma ka ban mamaki da naga kana murna.
Au karnayi murna Safna? lallai baki da hankali.
Nidai ka sakeni kawai bazan iya zama ba na hakura.
Ke! karki kawo min hauka kinji ko, wannan auren babu sake koda haihuwa ko babu, kin zama ni nazama ke, meye amfanin sakin?, idan kin fita zaki tabbata ba aure ne?, kina nan Safna idan har zaki haihu ‘ya’yana zaki haifa, kuma ko baki haihu ba muna nan tare, ballantana ma insha Allahu kema zaki haihu, ni banga abun tada hankali ba, dan dai ku mata haka kuke ne, dan Allah ki kwantar da hankalin ki…
Nifa nace maka kawai ka sakeni wlh bazan iya zama ba.
Mikewa yayi tare da jan tsaki sannan yace, wlh kinji na rantse duk lokacin da kika bude baki kikace in sake ki saina miki dukan tsiya, wannan ma ai raini ne ki dinga kallon idona kina cewa in sake ki, idan sakin a hannun ki yake sai ki yi, wawiya kawai, mara hankali, Abba ne me cewa in daina dukan ki zan gaya mishi abun da kike cemin dan lokacin da zaki fusata Ni ma in dake kin bansa ni ba…
Ficewa yayi batare da yajira jin me zatace ba.
*****
Banda abun ki Rahma menene na kuka, sufa maza haka suke, duk son da sukewa mace bashi zai hana su ganu wataba awaje, kuma babu komai abun duk daya ne, abun na banbanta ne kawai ta yanayin halaye da dabi’u, sannan soyayya ta gaskiya, wadda aka gina ta domin Allah, kuma rayuwa Allah ke shirya maka bakai ke shirya ma kanka ba, duk irin girman jarabawar da zatazo maka ka karfeta hannu bibbiyu sannan kayi addu’a Allah ya zaba maka abun da yafi alheri agare ka, dan haka duk lokacin da Sumayya tazo miki da matsala saiki bata hakuri sannan ki bata shawara tayi addu’a, sannan kema ki dinga kokarin zama jaruma ke daina barin abu ƙalilan yana saki kuka
Amsawa Ammi tayi tare dajin sanyi cikin ranta, zuwa can taji Ammin ta cigaba da cewa.
Sannan kuma mace me ciki ba, a son tana saka damuwa arai, idan kina da damuwa ki dinga fada, idan baxaki iya gaya min ba ki gaya ma Modibo, nasan yanxun dai ai kina iya hira sosai dashi ko?
Sunkuyar dakai Unaisa tayi tana wasa da hannun ta.
Murmushi Ammi tayi, sannan tace, ” Rahma dai akwai kunya, saikace ba yaran zamini ba, toh in ma baki sakin jikin ki ya kamata ki sake jinki, ayanzun baki da wadda ya fishi, akwana tare a tashi tare ya wuce wasa, mijin kine kuma abokin ki, ya cancanci ya tare miki kowanni matsayi dan Allah ku haɗe kanku.
Har yanzun wasa take da hannun ta ganin Haka Ammi tace, babu inda ke miki ciwo ?
Babu Ammi.
Toh kuma baki sha’awa cin wani abu?
A’a Ammi.
Duk ranar da kikaji kina soncin wani abu karki yi kwauron baki, kiyi mgn ko menene.
Amsawa mata Unaisa tayi sannan Ammi tace, an kira Sallah kitashi koyi sai kizo ki dan kwanta kiyi bacci.
*****
Kai Alhamdulillahi abu yayi kyau, waya ya daga yasa a kunnen sa sannan yace, Modibo toh ka kira Baba dai ko?
Sosa kansa yayi duk da basa tare sai yaji kunya ta rufeshi, Abba ban kira ba.
Ya kamata ka kirashi da kanka ka mishi Albishi ka sani ma ko ya baka tukuici.
Dariya sukayi gaba daya sannan yace toh shikenan Abba zan kira insha Allahu.
Bayan sun sauke wayar Abba kasa hakuri yayi ya kira mahaifin sa ya sanar masa, farin ciki sosai ya nuna sannan yai ma me cikin fatan rabuwa da cikin lafiya.
Shiko Modibo haka nan yaji beson kira mai martaba dan haka ya kira Magaji bayan gaisa yace, Ka kira Baba ka mishi albishir, ka tabbatar ya baka goron Albishir sannan ka gaya mishi Rahma nada ciki.
Jimmm Magaji yayi cikin rasa me yakeji cikin ransa, zuwa can yace toh kawai sannan ya kashe wayar.
Shiru ya zauna yayi cikin rasa wanni hali yake ciki, zuwa can kuma yai tunanin Mai martaba yana iya masa kyauta ban mamaki sabo da ya kala rai akan Modibo, wannan tunanin yai yasashi yai saurin danna masa kira bayan ya dauka yace, ” Barka da dare ranka ya dade.
Wanni ja’irin ne?
Ni dai Albishir na kira na maka.
Toh inajin ka?
Goro zaka bani.
goron lafiya, daman kaika fara gaya min sai na baka, Ubanku ya gaya min tun da ɗumi ɗimin sa, naji kun kusa zama iyaye ko bashi bane kiran naka.
Kashhh, amman banji daɗi ba, duk da haka dai kabani goro.
Babu goron da zan baka, dama wani ne bakai ba, yanzun abun da nake so dakai, gobe kayo asuba ci ka amsa dabinu kabawa me junan taci.
Bude baki Magaji yayi fuskanshi dauke da tarin mamaki sannan yace, ” haba Baba, in tashi tun daga nan inzo kawai dan In amsa dabinu?, kabari kawai asai mata anan.
Wannan dabinu na musamman ne Magaji.
Toh ka aiko dashi amman ni wlh bazan zo ba.
Ai daman baka da kunya, Modibo dake gaba dakai ko musu baya min, kaiko kafin karfin Ubanka ya zuba maka ido kawai.
Dariya Magaji yayi dan haka Kakan nasu yaci gaba da cewa, kayi dariya da kyau, ina nan ina maka shiri tunda ni ka iya bani amsa umarni zan bawa uban ku ya zaba maka mata cikin kwana uku a gama komai.
Wlh wlh karka soma, idan ku kuka fara shiru zan yi, ayi akawo yariyar, wlh yankan rago zan mata, sai dai da safe kazo ka dauki kan daban gangan jikin daban, niba Modibo bane fah.
Eh lallai za’a aika, tunda ba mutunci gare ka ba, akwai alamar ma kana shaye shaye, bari nasan maganin ka, sawa zanyi agama ka.
Dariya Magaji yayi tare da katse kiran batare da yabar dariyar ba, ya mike ya nufi dakin Ammi fuskan shi dauke da walwala, Ammi ce tace yadai?
Kallo Modibo yayi dake zaune kusa da Ammi yace, ” Kasa ni nakira Baba ya bani tukuici, amma sai yace wai sawa zaiyi a kama ni.
Dariya Ammi tayi yayin da Modibo yai murmushi tare da fadin, ” da abun da ka mishi”
Aure yace zai min nace yanka matar zan yi.
Dariya Ammi tayi haka ma Modibo, Unaisa ma kawar dakai tayi tai dariya yayin da Ammi ke fadin, ” dole yace zai sa akama ka tunda rashin jinka yayi kamari.
Mikewa Modibo yayi yana fadin, Ke tashi muje.
Mikewa tayi zaune sannan ta dauki hijjabi ta dake nike agefe tana kokarin sawa, Modibo ne yabita da kallo me cike da kauna, Ammi ce ta dibesu tai saurin kawar da ido, bayan Unaisa ta gama saka hijjabin taima Ammi sallama sannan suka fita.
Falon Ammi Modibo ya riƙe hannun Unaisa tare da faɗin rufe fuskan ki”
Cikin sauri ta daga kai ta kalleshi tace nan danan dinne saina rufe fuskana?
Eh kawai yace tare da daure fuska sosai, ganin haka tai saurin bin umarnin sa, sun riga da sunci abinci dan haka kai tsaye part din Modibo suka nufa, dare ya riga da yayi dan haka ya wayoyin sa kawai ya aje sannan ya kalli Unaisa yace ina zuwa.
Da alama gurin Safna zashi, yau daga tun bayan tarewan ta tasan cewa zashi gurin Safna batare da taji wani bacin rai cikin zuciyarta ba, ita kanta mamaki ta shiga yi meyasa banji haushi ba yau, cikin sauri tasa hannunta ta shafa maranta tare da fadin, cikin zuciyar ta, ko dan yau ina cikin farin ciki ne, yanzun kenan akwai dan mutum a wannan cikin nawa, ɗan ma wai ɗana tare da Modibo, baya ne ya dinga dawo mata, lokacin da Modibo ya dinga zuba mata nacin sa akan dole da nacin sa ya shige cikin rayuwarta, yai kane kane, duk da cewa yafi karfi na haka ya dauko ni ya maidani cikkayar mutum kuma ya bani ajiya mafi girma arayuwar shi, hawaye taji yana zubo mata, sosai ta tuna irin zaman kunci da bakin cikin da tayi abaya na rashin galihu, hawaye ne yake zobo mata tana sharewa har yanzu bata bar shafa maranta ba wanda sai ayanzun take jin sa kamar yayi mata nauyi kaɗan.
Wani irin Soyayyar cikin ne ke kara kwanciya cikin ranta tare da kosawa taga wanene acikin nata mace ko namiji Allah kadai ya sani.
*****
Momy nifa bazan iya zama dashi ba yanzun, ni nace ina son shi kuma yanzun nafasa auren ko dole ne?
Wannan kalma ita Modibo ya tsinkaya yana tura kofar dan haka ya daga murya yai sallama, dagowa tayi ta kalleshi sannan tace, ” Ni bazan yi irin wannan zaman ba, kisan ma duk yadda zakiyi ki rabani dashi.
Beji me ake cemata acikin wayar ba bayan shiru na dan lokaci tace”
Wlh kome nene ma karki kulani, ni da gaske nake yi, Mommy wlh ban son shi.
Gaba daya ji yayi ransa na masa tiririn dan haka ya mika hannu ya fizge wayar yai jifa da ita, tare da fadin, wai ke kina da hankali kuwa?
Da hankalina Hamma.
Waye kike cewa baki so?
Kai.
Ni?
Eh banson ka.
Me ya faru me aka miki?
Ai dole kace min me ya faru, zaka maidani mahaukaciya kaje ka dauko yariya ka mata ciki sabo dani baka kauna ta.
Ni kike gayawa irin wannan mgnr?
Toh bazan gaya maka ba Hamma so kake na zauna bakin ciki ya kashe ni?
dawa kike waya?, har kike gayan irin wannan kalamin?
Momy ce, tunda kace idan na sake mgnr zaka dake ni.
Shiru yayi yana kallonta tsayon lakaci sannan yace toh yanzun me kike so?
Ka sakeni ne kawai.
Mikewa yayi tare da fadin, toh yazun bari na baki shawara, tunda bakya sona kin faɗa kin nanata min, idan kin cika mara kunya ki kaini kotu ne, dan banga wadda ya isa yasani inyi abun da banyi niyayya ba, Alkalai da zai raba auren ma inason na Ganshi, karyar rashin wayo kike yi.
Bude baki tayi ta nufin mgn yai saurin daka mata tsawa tare da fadin,” idan kikace takkk sai na fasa miki baki wlh, karki fasa kije kiyi duk abun da kikai niyya, dan kinga Ina lallabaki Zaki kawo min iskanci, juyawa yayi ya fice tare da sakin kofar ta bada Wani kara garam.
Daki Unaisa ya koma idon shi jawur yayin da zuciyar shi ke cike da bacin rai
sosai yake son nunawa Unaisa farin cikin sa sannan yana son lallai shima yaga nata farin cikin amman Safna ta bata mishi rai, wanka yayi ya fito Yana gyara jikin sa tare da kokarin kawar da damuwar Safna, domin dai daren jiya be samu komai ba gurin Unaisa dan haka baya son ya rasa yau ma, turare ya fesa acikin sa sannan ya nufi Unaisa ya mikar da ita tsaye tare da rungumeta ajikin shi ya sunbace ta tare da lumshe ido, karan da wayar sa tayi yasa shi bude ido tare da kallon wayar, sunan Momy ya gani yana yawo akan wayar……