Advertisements
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 46
Hawaye ya fara sharewa sabo da rasa inda zaisa kansa.
Advertisements
Modibo ne yace baka fara kuka ba munafuki zakaga yadda zamu yi dakai.
Ammi ko wannan lakacin kuka take yi haka ma Yaddiko numfarfashi ta shiga saukewa, Daddy Suraj ne yace”
Yanzun kana nufin kai tunda ka fita da jaririn nan baka sake sakashi a idon ka ba?, lallai kai azzalumi ne, kuma sam baka da hankali, ɗan ka na cikin ka da ka haifa kama wannan abun, wanda kuma ba naka ba sai kisa.
Advertisements
Ammi ce tace wannan ɗin ma waya san me yayi masa, yanzun dai ya faɗa mana abun da yaga dama, waye yake da tabbacin abun da ya faru kenan.
Suraj ne yace, ” ai babu inda zashi saiya fito da yaron nan wlh, duk gidan uwar da yakai shi yana sane.
Modibo ne yace wannan ma ai rainin hankali ne, yazo muje ya kaimu rufar mutumin zamu nemo shi….
Katse Modibo yayi da fadin, ” ai yanzun ma wajen anyi gine gine ba kasuwa bace a yanzun, duk zuwa saina je na duba.
Suraj ne yace Modibo tsinka mishi mari, yayin da su Ammi suka haɗa baki wajen fadin, ” a’a Sam wai ko wasu irin marasa hankali ne.
Juyawa Ammi tayi ta kalli mahaifiyar Moh’d sannan ta juya ta kalli Mahaifin Suraj ɗin tace, “Alhaji meye abun yi a yanzun ?
Lumshe idon shi yayi tare da fadin, su tashi su tafi kawai.
Da sauri Suraj da Modibo suka kalli Daddy, kusan haɗa baki sukayi wajen faɗin, abarshi ya tafi kuma?, me laifi ne fa, dole akaishi wajen hukuma su hukunta shi.
Ammi ce tace ni kuma da tunani na akai shi wajen me martaba.
Daddy ne yace, a’a ku barshi yai tafiyar sa, ɗan dai ai babu shi, da ace In kaishi za’a samu ɗan ne, toh da alama dan sai wani tsananin rabo, dan haka ina ganin mubarshi kawai yai tafiyar sa babu wani hukunci da yafi na Allah, duk inda za’aje dai dole za’a sake shi kuma sai yayi yawo munaji muna gani, toh mubarshi mujira hukuncin Ubangiji dan ba Maryam ba harmu da muke tare da ita ya zalince mu, bacin ran yau daban na gabe daban.
Mahaifiyar Moh’d ce ta share hawaye sannan tace, ni zan wuce nacika alkawari na kawo muku shi, juyawa tayi ta kalli Modibo sannan tace, kai kuma Nagode da abun da kamin arayuwa, Ni bani da amfani gurin ka tunda na gama nawa, na kawo ka duniya, banson in maka baki sabo da ‘ya’yan ka, amman zan gargade ka, karka sake takowa inda nake, nacire ka daga cikin ‘ya’yana ko lahira ban fatan Allah ya hadani da azzalumin mutum irin ka, daga haka tsohuwar ta mike ta fita babu wadda yace kalla har ta fice.
Daddy ne ya kalli Moh’d yace me kake jira ne?
Mikewa yayi da sauri yayin da Modibo ma ya mike Moh’d ɗin na takawa yana bin bayan sa.
Ammi ce tace Modibo dawo ka zauna.
Ina zuwa Ammi.
Kadawa ka zauna nace.
Ammi yanzun zan dawo.
Karka fita Modibo.
Kai! Ammi, dan Allah ki barni, zuciya ta zata fashe, kokarin fita yake dan haka Ammi tace, idan ka fita daga falon nan ban yafe maka ba Modibo.
Cak ya tsaya tsayon lokaci sannan ya dawo ya zauna tare da kwantar da kansa ajikin kujera yayin da ya kalmashi hannun sa a kirjin sa, tsintan kanshi yayi da zubar da hawaye dan haka ya shiga sa hannun sa yana sharewa amman duk da haka zobowa suke yi.
Ammi da Daddy kuwa Yadikko suka shiga kwantar ma da hankali tare da nuna mata tasa azuciyarta dan ya mutu kawai, kuma ta zama musulma ta kwarai me karban jarabawa duk a yadda tazo mata, yayin da Daddy ya kara da cewa, Allah yasan zalin ci da Moh’d yai miki kuma zaki ga sakayya.
Hawaye Yaddiko ta share sannan tace nasani ƙaddara ce, ana haihuwar dan ma ya ko nan take, kuma ka hakura, ɗan kama da ka haifa ya girma dakai yana mutuwa ya Barka kuma ka hakura, amman abun da Moh’d yamin yana min ciwo, konayi kokarin nashare kasawa nake, nikadai nai hawala da cikin, inda kuka san ba nashi ba haka yake nuna min, ko sau daya banje asibiti ba kuma yana da kudin sa bawai babu ba, nima kuma ya hana ni fita, sannan tsinke be saya ba na haihuwa kayan Suraj da nai goyon shi dashi na wanke na goge amman sabo da tsabar zalunci ina haihuwa ya dauki ɗan da ya jefar, Ni ina ga ma so yayi na mutu wajen haihur.
Ammi da Daddy ne sukace duk kiyi hakuri da ciwo dan ciwo, tabass abun akwai zafi, Amman kibarsa da Allah, shikuma ɗan idan yana raye Allah ya sada fuskokin ku da alheri.
Ganin yadda su Ammi keta rarrashin Yaddiko kuma da alama ta fara nutsuwa yasa Modibo ya mike yace, ni zan tafi .
Amsa masa sukayi dan haka ya fito cikin sauri yabar gidan yana tafe yana share hawayen bakin ciki.
****
Ashe ka dawo?
Dagowa yayi ya kalle Unaisa sannan ya mika hannun sa alamar tazo.
Tahowa tayi ta zauna ajikin sa, hankali yasa hannun shi yana shafa bayanta cikin yanayin tunani.
Wai lafiya kuwa yau?, Unaisa ta fada tana kwance ajikin shi.
Bankin dadi ne Rahma.
Ya jikin Yadikko?
Alhamdulillah.
Badai jikin bane ya dashi ko?
A’a
Ka gaya min mana, naga kun fita kai da Ammi, harna gaji da jira da dawo baku dawo ba.
Dagowa yayi ya daura idon sa anata tare da fadin, ” bakomai wani bako ne yazo.
Batare data yadda ba tace toh me ya samu idon ka?
Murmushi yayi kadan sannan yace, me kika gani?
Sunyi jah da yawa.
Faɗaɗa murmushin sa yayi tare da fadin, ” wani abu ne ya faɗa min.
Kuma aduk idon guda biyu?
Eh ya dafa tare da fadin, tashi muje mu kwanta.
Zaro ido tayi tare da saurin tashi daga jikin shi take fadin, ” bafa anan kake ba ko ka manta ne?
Ina sane, bata nanne tayi tafiya.
Dan jimmm Unaisa tayi sannan, tare dajin wani irin sanyi ciki ransa saidai taki bari ya gane hakan.
Toh me zakaci ko inje in ma girki?
A’a na koshi muje daki kawai.
Dakin suka shiga tana rungume ajikin shi saidai rashin walwalar shi tayi yawa daina da suka kwanta.
Gaba daya ya kasa bacci yanajin yadda Unaisa keta sauke numfashi, tashi yayi ya zauna yana mejin tsananin sonta cikin ransa, tunanin rayuwarta ada da ta yanzun ya tuna, goshin ta ya shafa tare da fadin, Allah ya albarkacin rayuwar mu, Allah kuma ya barmu tare, ina tsananin son ki, sunbatan ta yayi ya goshi sannan ya gyara zaman shi tare da maida idon shi kanta, acikin zuciyar shi ya fara fadin, ” kema nakusa fara bincike akan iyayen ki, akwai alamar tambaya akan haihuwar ki Rahma, wata zuciyar ce tace toh kai me kake tunani?
Shiru yayi tsayon lokaci sannan ya maida hankalin sa sosai ga Rahma yacigaba da fadi cikin ransa, ina tunanin wata kila gidan marayu suka dauko ta, wata zuciyar ce tace, a’a agidan marayun ne zasu basu dan daba’a yanke masa cibi ba, Dada ta gaya min taga mahaifa da kuma jinin haihu akan zanin Innawuro, wani irin mummunan faduwan gaba yaji lokacin da ya tuna yadda Moh’d ya dauki ɗan da Yadikko ta haifa, shima ance babu komai daya bari, goshin sa ya dafa tare da fadin, hakan na iya faruwa gidan da yakai jaririn, dole da mahaifa da komai zai kaishi, cikin tsananin mamaki yace labarin yazo daya fa, toh Amman Ita Yadikko namiji ta haifa.
Shiru yayi tsayon lokaci zuwa can ya sake fadin, kuma ance a Yobe suka zauna kuma itama Rahma a Yobe komai ya faru, toh ko Rahma ‘yar ya dikko ce?
Ganin babu me bashi amsa ya sauke kafar sa kasa tare da fadin, toh ai shima Moh’d ɗin yace namiji ne hakama Yadikko, ido ya zubawa Rahma babu wani alamar ta kamanceceniya ita da Yaddiko haka ma da Moh’d dan haka ya fara kokarin goge wannan tunanin cikin ranshi.
Daurewa yayi ya kwanta, tare son yin bacci amman baccin ya gagari idon sa, wasu kalmomi ne yaji suna masa yawo akan sa, dan haka zunbur ya mike zaune, yana kara tuna kalmar, tana kama da Fanan.
Mikewa yayi tayi tare da fadin cikin ransa, inda ace Yadikko tace mace ta haifa toh dako tantama babu zaice yarta ce, tsintan kansa yayi da tashin Unaisa.
Yadda yake tashin ta yasa ta tashi a firgice tare da tambayan menene?
Nutsu kijin ko?, ba wani abu bane tambayan ki zanyi.
Mene?
Menene sana’ar Baffan?
Baffah na?
Eh.
Mai yake saidawa idan ya dauka daga gida sai yakai cikin gari.
Rahma banda wannan fa?
Nidai shinasan yanayi menene kake tambaya?
Bakomai, kwanta abun ki.
Komawa tayi ta kwanta saidai shi ya kasa bacci, dan haka ta juya ta kalli shi tare da fadin, wai menene?
Babu ki kwanta abun ki.
******
Washegari tundaga masallaci gidan yadikko ya wuce, beson ya bude zargin sa sai ya gama tabbatar wa.
Tsit ya samu gidan, yanayin sallama kofar Yadikko ta amsa tare da fadin, Modibo lafiya?, shigo
8 comments