Ina marubuta ma su sha’awar shiga gasa domin gwada fasaharsu? To ku marmatso ga dama ta samu. Shahararriyar ƙungiyar nan Exquisite Writers Forum ta shirya tsaf domin gabatar da gasar rubutun labari a tsakanin marubuta. Gasar za ta zo da sabon tsari wanda ba a saba gani ba.
Advertisements
GASAR ƘUNGIYAR EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)
Jama’a Assalamu alaikum. Ina marubuta ma su sha’awar shiga gasa domin gwada fasaharsu? To ku marmatso ga dama ta samu. Shahararriyar ƙungiyar nan Exquisite Writers Forum ta shirya tsaf domin gabatar da gasar rubutun labari a tsakanin marubuta. Gasar za ta zo da sabon tsari wanda ba a saba gani ba.
Tsare-tsare da dokoki:
Advertisements
1- A wannan gasa muna neman marubuta guda talatin (30) ne kacal.
2- Za su tura da sunansu da lambar wayarsu ta nan; galadanchibalkisumusa@gmail.com
Daga yau Juma’a 21/ 01/2022, zuwa ranar Juma’a 28-01-2022
3- Marubuta guda 30 da suka fara turawa na farko; su ne za su samu shiga wannan gasa.
Advertisements
4- A ranar 10/02/2022 za mu tattara waɗannan marubuta guda talatin, inda za a gudanar da wannan gasa kai tsaye, ragowar abin da ya shafi tsarin za su ji shi a wannan ranar.
5- Bayan kammaluwar gasar; za a fidda zakarun da suka yi nasara guda uku; na ɗaya; na biyu; da na uku. Na farko na da kyautar dubu goma(10k) da satifket, na biyu na da kyautar dubu biyar(5k) da satifket, na uku na da kyautar dubu uku(3k) da satifket. Sannan duk wanda ya shiga gasar ko da bai yi nasara ba zai samu kyautar satifket na shaidar shigar shi gasar.
6- Ba a yarda members ɗin ƙungiyar Exquisite Writers Forum su shiga gasar ba.
7- Ga dukkan wanda ya amince da shiga zai yarda da dukkan wani tsari da zai biyo a gaba, har zuwa lokacin da za a kammala gasar a faɗi sakamako.
Sanarwa: Daga shugabannin ƙungiyar.
Mun gode.
3 comments