Advertisements
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
Tsuntsu Me Wayo
🕊🕊🕊🕊🕊
Storry & written
By
Fadeela Lamido
PAGE 9
Advertisements
Da sauri ya farajan yariyar yana kokarin barin gidan da ita ummi ce taji hayaniya yayi yawa da sauri ta fito, ganin haydar najan yariyar ta fara dakamai tsawa cikin sauri ya saki yariyar yana mazurai, ummi takalli dadtijuwar matar da suke tare da yariyar tace sannu da zuwa hajiya shigo ki zauna.
ba musu tahau kujjera ta zauna fatima da salis ko kallo sukabi yariyar dashi.
haydar ko yana jingine jikin bango sai aikawa yariyar harara take
Advertisements
ummi ce taji shirun yayi yawa tace baiyawar Allah ban fah ganeki ba.
kamar jira matar take tace dama ai bazaki gane ni ba amman ai d’aki haydar bazai ce be gane mu ba, atakai ce dai hajiya Nazo ne na shaida miki ‘yata zinat ta dauke da cikin danku haydar
wani zufa me dumi ya karyo ma ummi take ta Fara fadin innalillahi wa Inna ilaihir raju,un maimaitawa taitayi zuwa cen ta daga jajayen idonta ta kalli haydar kanshi akasa yace ummi nifa karya suke min.
bata ce komaiba ta mayar da kanta kasa wasu hawaye ne masu dumi suka zubu mata zuwa cen ta miki ta nufi falon alhj salis ne yabi bayan ta yana fadin ummi karki gayamai Dan Allah .
waigowa tayi tace salis wannan ba abun da za,abuye bane , dole ne yasan halin da haydar yake ciki dan ni yanzon ban san yadda zanyi da wad’an nan mutane ba, tana fadin haka ta shige dakin.
bata dade ba saiga su sunfito tare da daddy yana huce.
fatima naganin fitowan daddy tamike ta nufi dakin su cike da tsananin tsanar haydar azuciyar ta.
daddy ko kallon haydar yayi cike da bacin rai sannan ya juya ya kalli bakin nasu sannan yace kai haydar fita kabar min gida, ku kuma kutashi ku bishi karku kara gigin nufumin gida da nufin Ku kawo min shege bazan taba karba ba.
haydar ne ya bude baki yace daddy nifa karya suke min.
idan kasakemin Wata mgn zan illataka ka fita kabar min gida wai gawa yayi barayin matar cikin tsawa yace kutashi ku bishi, cikin rawar jiki suka mike suka fita dan tuni haydar ya fita salis ma mikewa yayi zaibi bayan su
daddy yace karka fita tsayawa yayi ya jingina kanshi ajikin bango.
ummi ko kuka take yi tana fadin alhj wannan hukunci beyi ba, matar tabani tausayi be kamata amata hakaba ,yanzon yaya zatayi kenan?
Oho nidai bazan karbi shegeba d’an karamin shi dashi ya lalata rayuwuwar shi, yace na mashi aure ne ban mashi ba? wacce irin jaraba ce wannan yariyar nan ma ai inbanda jaraba ta girmeshi haka daddy yayita fada wata mgnr ma besanin sanda ta fito bakin shi.
ummi ko kuka take sosai yayin DA salis ke tsaye jikin bango
haydar ko yana fita ko waiwaye babu ya nufi motar shi shiga yayi ya zauna daidai lokacin zinat da mamarta suka fito harara ya wurgawa Zinat itama ta mayar da nata hararan motar shi yaja yabar wajen.
yana fita agidan ya fara kuka hawaye ne yake zubomai kaman karamin yaro yana bakin cikin batawa iyayen shi rai da yakeyi amman ya kasa cen zawa, tsawa yayi bakin hanya yayi kuka sosai sannan ya kama hanyar gidan alhj yusuf.
alhj yusuf naganin haydar gabanshi ya fadi sakamako idanuwan shi dasuka kunbura tahowa yayi ya kamashi ya zaunar dashi ya fara tambayan shi me ya faru amman ina haydar babu baki domin kuwa ya kasa cewa komai illah hawaye dake bin kuncin shi.
alhj yusuf ne ya lura haydar bazaiyi mgn ba, dan haka ya daga waya ya kira daddy.
daddy na daukan waya yace au gurin ka ya taho, toh maza ka ko reshi karka sake kabar shi a gidan ka mazinaci ne dan iska .
takaicine ya kama alhj yusuf yace yanzo yaya dan daka haifa kake kira da wad’an nan mugayan kalamen.
ba d’ana bane ayan zun tunda yace shi d’an iskane na barma duniya kuma kaima karka kuskura ka tareni da mgnr haydar yana fadan haka ya katse wayar.
alhj yusuf ya sauke wayar ya kalli haydar yaga har yanzon hawaye ne a idon sa kamar anbude fanfu
ya mayar da kanshi kasa zuwa cen ya d’ago ya kalli haydar sannan yace haydar aure za,amaka kuma ba ina neman amincewan ka bane za ayi auren ne ko kana so ko baka so.
🕊🕊
7 comments