
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
PAGE 5
Nasan zaka iya abokina, sai dai kabi ahankali karka zura jiki”
Akwai wani abu azuciyarka kenan, nibana fargaban komai🤷🏽♂️
Akofar gidan su Galadima ya ajeshi sannan sukayi sallama ya nufi Babban gida kamar yadda ya fada”
Saidai abun mamakin be samu Khadija adikinta ba kamar yadda ya zata, wayarta ya Kira sau uku bata dagaba dan haka ransa ya bacci sosai domin yasan ba mancewa tayi ba wani dai abun ta shirya”
Adakin Inna yalwa ya sameta zaune tana yanken farce, tsaye yayi bayan gaida Innar tasu sannan yace”
Meyasa nakira wayarki baki dauka ba??
Bana kusa da wayar ne”
Jimmm yayi sannan yace ya mgn da mukayi dake ranar nan ko kin fasa ne?
Eh Kai nake jira bacewa kayi zaka bani kunya cikin bainar jama’a ba, shiyasa nazo nan na shirya Bismillah”
Murmushi yayi kadan tare da zama gefen gadon yace”
Meyasa kika cika tsiwa ne?, Kefa kika Nima sulhu bani ba”
Duk abon da suke Inna najin su”
Bana nima sulhu abun dake ranka kawai nace ka gayamin”
Mikewa yayi ya dawo daf da ita ya zauna har sunajin dumin juna”
Ahmad cikin tsananin Mamaki ta Kira sunan sa”
Kallonta yayi yayin data farajin saukan numfashin sa afuskan ta”
Mikewa tayi da sauri tana fadin”
Bantaba sanin rikakken Dan iskan bane Kai sai yau”
Dagowa Inna tayi ta kalli Khadija tace”
Hadiza ya haka kuma?
Hannu Ahmad ya daga mata a’a barta Inna tana wasa Dani ne”
Cikin tsanin fada Khadija tace”
Inna baki ganin me yake min ne doba fah inna, ni wlh nagaji da abun da yaron ke min Inna”
Ahmad cikin dakiya yace
Basai kiyi maganin abun ba, mikewa yayi yayin da Khadija ta bishida Harara haryai kofa tace”
Mara kunya kawai wawa dakai kawai”
Dawowa yayi ya tsaya yayin da Inna ta rike baki tana fadin baki ta mutunci Khadija”
Shima kallon yabita dashi, zuwa can yayi kwafa tare da fadin zan baki amsa ranar da kika tare agidana, juyawa yayi batare da yaji amsan da zata badaba, itama cikin fushi ta mike zata fita Inna ta tare ta tana fadin”
Zaki bishine ku ida lalacewa awaje??
Inna take taken Ahmad fa waishi adole sona yake”
Toh saime Hadiza?? Wani abu ne aciki?
Haba Inna ta yaya za’ayi in aure Ahmad?, Wlh wlh ko maza sun kare aduniya bazan auri Ahmad ba”
Toh meye dashi Hadiza??
Inna kimfasan komai wlh daga yau ko mgn bazan sakeyi dashi ba bani bashi”
Bazai yiyuba kuwa ki sake tunani, tare kuka taso da Ahmad kamar ‘yan biyu, har kika isa aure kuna tare, haka bayan kimyi aure yana zuwa har gidan ki, idan kina cikin damuwa yafi kowa shiga tashin hankali, ko iyayenki da suka kawoki duniya bazasu kaishi shiga damuwa ba idan har ya fahimci kina da matsala, bazan manceba akwai ranar da yadawo nan ya kwanta yaita kuka nayi nayi ya Gaya min menene yaki fadin, kuma daga gidan ki yake, dan haka Inna baki shawara idan har ya nuna yana son ki, ki saurare shi”
Kuka Khadija ta fara Haba Inna komai yake min nadauka ne dan uwanane naji, ni bansan cewa badan Allah yake ba, ni wlh bazan taba aurin Shiba, niba yariya bace da za’a min auren dole ko aurena nafarko wadda nake so akabani dan haka yanzun ma bazan aure wadda banso ba😭
Lallai Khadija dan Adam butulu, yanzun ke har Zaki bude baki kice baki son Ahmad?🤔
Inason shi Inna, Amman so irin na zumuncin bana aure ba, wlh natsane shi, haushi mani yake bani, gaba daya besan kanshi ba, rashin kunya da fitsara tafi yawa akalaman sa”
Shikenan Khadija ai daman babu wadda zai hadaki dashi dole, amman kibar cewa baki son shi, amatsayina na kanwar iyayen ku nabaki sharawa akoda yaushe kalaman ki su zama masu sauki wannan fadace fadacen banaki bane”
Hawaye Hadiza ta share sannan tace”
Nidai Inna kuce mishi ya daina min mgn kawai, idan kuma kudin sa ne daya Kashi min yamin lissafi nabiya shi”
Murmushi Inna tayi tana fadin hmmm Yaro besan wutaba saiya taka, idan kikai wasa nan gaba zakiyi kukan danasani da idanun ki”
Kofa ta nufa tare da saka Hijjabinta”
Inna kuma Zaki”
Ni gidan Alhaji zane”
Kankat kenan, toh Allah ya baki sa’a Allah ya kuma shirye ki”
*******
Khadija zaune gaban wan mahaifinta bayan tagama karanta masa abun dake tafe da ita ya daga waya ya Kira Ahmad”
Dakon zuwanshi suke, yayin da Alhaji ya shiga kwantar mata da hankali, tare da nuna Mata cewa ai ana irin wannan auren ba wani abu bane ba, misali ya shiga bata wance da wane, ganin kamar shima yana goyon bayan abun ta fara kuka”
Ganin tana kuka Alhaji yace”
Wannan fah bawani abun tada hankali bane Khadija indai kince baki so ai shikenan…..
Shigowan Ahmad yasata yin shiru, ganin Khadija agidan sosai abun yabashi Mamaki, zama yayi sosai, ko tantama bayayi zancen ta kawowa Alhaji, tunaninta yana da zafi zaiyi maganin shi, lankwaaa kansa yayi ya gaidasa”
Bayan ya amsa yace”
Wani lbr naji bakin Khadija, Ahmad kaida nake ganin nutsuwarka?, Idan kana son Khadija ai saika same daya cikin mu ka fadamawa mukuma zamusan ta yadda zamu fito da zancen”
Jimmm yayi zuwa can yace”
Ni bansan wannan mgnr ba Alhaji bantaba jinta ba”
Kallon Khadija Alhaji yayi tare da fadin, a’a🤔 ke Khadija daman bashi ne ya Gaya miki ba??
Shine Alhaji”
Juyawa yayi ya kalli Ahmad sannan yace karku maidani karamin yaro waye sa’a ku nan?
Alhaji ai gani gata ta fadi ranar dana bude baki nace Ina son ta zan aureta”
Hadiza Alhaji ya tsurawa ido, daker ta iya bude baki tace Alhaji ai irin kalamin daya gaya min yasa na lura da haka”
Jimmm Alhaji yayi ya kalli Ahmad ya kalli Khadija sannan yace”
Kai Ahmad wanni irin kalami kake Gaya mata?
Ita ya kamata ka tambaya Alhaji ni bazan iya rikewa ba, bance banai ba, Amman ta maimaita”
Shiru tayi ta kasa mgn yayin da Alhaji yace Ina jinki Khadija”
Nidai kawai Alhaji arabani dashi, bani bashi kawai kalamansa sun isheni”
Shikenan ya isa Hadiza Alhaji ya fadi bayan yaga Hadiza nashirin kuka, juyawa yayi ya kalli Ahmad yace Kai idan kana Mata wani kalami kabari bataso, zancen wani aure idan ma kanadashi cikin zuciyarka karka furta ta, wai ba ance Baban ka yaima Mata bane??
Jinjina Kai yayi ahankali yayin da Alhaji yaci gaba da cewa”
Abar mgnr, kar ku bari wannan zancen ya kawo rashin jituwa atsakanin ku, mgnr da bataso kabar Mata shikenan ku tashi ku tafi”
Alhaji ni so nake yabar yimin mgn”
Cikin Mamaki yace kwata kwata?🤔, ai bazai yiyuba Hadiza, ni bansan Ahmad da wata matsala ba kema haka Amman tunda kin kawo karansa zansa asamin ido akan shi, tashi kijirashi amota zamuyi mgn dashi”
Ba yadda ta iya, bakin motar tasa ta tsaya saidai ko ganinsa batasan yi, datasan inda yariyar da za’a bashi take data zuge uwarta karta yadda, domin idon Ahmad afeke yake duk kuwa mutumin da bashi data ido biyi ba arayuwa, kunya ado ce, duk da cewa yana da kyau Amman kyaunshi yazama na
Banza da alama yasan Mata, wata Kila fitansa waje karatu yasan Mata sosai
*********
Ahmad da akwai alamar Khadija tafika gaskiya, Kai namijine kana da wayau fiye da ita, abun da nakeso dakai shine, kamaida hankalin ka akan yariyar da Mahaifin ka ya zaba maka, baza mu baka Khadija ba”
Dagowa yayi da sauri ya kalle wan mahaifiyar tasa sannan yamaida kansa kasa”
Ina fatan kaji abin da nagaya maka?
Naji, mikewa yayi jikinsa asanyaye ya fita kofar gida
Ko kallon inda Khadija take biyi ba ya bude motarsa ya shiga, kusan atare suka shiga, figan motar yayi ba tare daya kalleta ba”
Hanyar gidan Hajjah ya nufa duk tana kallon sa takasa cemasa komai”
Suna isa ya fice cikin motar sai faman huci yake, tsintan kanta tayi da rashin Jin dadin hakan, cikin sanyin jiki tabi bayan sa”
Tsaye ta samu Hajjah rike da baki tanabin bayan Ahmad da kallo sallamar Khadija yasa ta waigo a’a tare kuke Ashe?
Eh”
Meya sameshi?, Wani abu ne ya faru??
A’a
Toh Allah ya kyauta, zama tayi kusan awa be fito ba, dare ne ya farayi dan haka hankalin ta ya soma tashi bata gayawa kowa fitowanta ba sai Inna yalwa, dole zatasha fada wajen Baba”
Zaman jiransa har dare, misalin 8:30pm tace Hajjah kodai Ahmad ya manta dani ne?
Ai na dauka dama kunyi sai dare zaku tafine?
A’a gidan Alhaji naje acan ya sameni kuma Alhaji da kansa yace ya kaini gida”
Toh🤔 ko wani yabata masa rai?, Halan kuma kunyi fada ko”
Cikin sauri ta kada Kai”
Mikewa Hajjah tayi ta nufi dakin, zaune ta samesa ya daura kada daya Kan daya yana karkadawa”
Yaro?, Wai me yake faruwa ne?, Kadawo cikin fushi kabar Khadija tanata jira”
Bakomai Hajjah”
A’a dakomai fah, koma meye kabi ahankali, kadai San matsalar ka ko?
Nasani Hajjah zan kiyaye”
Toh daure ka kaita gida kaji”
Hajjah anan zata kwana munyi waya da Baba yanzun”
Toh ai shikenan idan Allah ya kaimu gobe saika kaita”
Zaman tayi tana danjansa da hira amman hankalin sa baya gurin ta Dan haka ta sake tambayan sa meke damun sa”
Bakomai Hajjah ya sake maimaitawa, mikewa tayi badan ta yadda ba Sai dan tabarshi ya kebe kamar yadda yake so”
********
Khadija Ashe yayi waya da yaya anan Zaki kwana gobe saiku tafi, Ina tunanin bejin Dadi da alamar akwai abun dake damun sa”
Mikewa tayi tare da fadin”
Anan gidan zan kwana Hajjah??
Meye aciki Khadija nan din ba gidan ku bane?, Wucewa tayi bata jira cewar cewarta ba yayin da Khadija ta fada kujera tana fadin”
Me hakan ke nufi, meye kuma Ahmad yake shiryawa da zaice wai nakwana anan gidan??, Yanzun nikuma kwanan zan yi?
9 comments