Advertisements
A MATSAYIN MU NA MARUBUTA ‘YAN BAIWA, MASU ISAR DA SAƘO WA AL’UMMA, YA KAMATA MUSAN ME MUKE YI, ME KUMA MUKE RUBUTAWA, MU KASANCE MASU KAWO GYARA BA MASU WARGAZA TARBIYA BA.
Sharriyar marubuciyar nan Nabeela Dikko tayi kira da babban murya ga marubuta dasu san mutuncin alkaluman su, bari muji daga gare ta.
Advertisements
Assalamu Alaikum, wa rahmatullahi wa barakatuhu ‘ƴan uwa musulmi, Sunana Nabeela Al-ameen Adam, wacce aka fi sani da NABEELA DIKKO.
Tb 1 Kafin mu shiga cikin tattaunawa za musu muji shin wacece Nabeela Dikko a takaice.
Nabeela Dikko: An haifeni a jihar Kebbi, a garin Argungu, anan na tashi, nayi karatu tun daga matakin firamare, sakandare har zuwa ƙwaleji, haka a ɓangaran addini nayi nasarar sauke al-ƙurani mai girma, da sauran littafan sani wanda har ila yau ana ci gaba da neman ilimin.
Advertisements
Tb2. Ko Nabeela tana da Aure.
Nabeela Dikko; eh akwai Aure
Tb3. A wacce shekara kika fara rubutu.
Nabeela Dikko; Na fara rubutu a shekarar dubu biyu da goma sha biyar (2015)
Tb4. Me yaja hankalin ki kika fara rubutu.
Nabeela Dikko: Abubuwa da dama zan iya cewa sun ja hankalina akan rubutu, amma mafi girma daga cikin su shi ne, ina sha’awar rubutu da karatu, sannan ni ma’abociyar bincike ce, bayan nan ina son nima na fara isar da nawa saƙonni da kuma ra’ayi ta hanyar rubutu.
Bugu da ƙari ganin irin abubuwan da ke faruwa a yau, yasa na fara isar da nawa muhamman saƙo da tallafi ta hanyar rubutu.
Kuma Alhamdulillah zuwa yanzu muna tura saƙo ta ko’ina ta hanyar rubutun kuma mutane da dama suna amfana har ma suna sa albarka.
Tb5. Masha Allah, Zuwa yanzun littafi guda nawa kika rubuta.
Nabeela Dikko; Na rubuta littafai goma sha huɗu zuwa sha biyar, banda gajerun labarai, dama labaran gasa hakan.
Tb6. Wai, Sannu da kokari, ko zaki iya lissafo mana sunayen su.
Nabeela Dikko; A ƙwai,
TSAN-TSAR SO
MATAN AURE
BUTULCI!
HAƘƘI!
AUREN DOLE!
ALMAJIRANCHI KO AIKATAU?
TARBIYYA
BAƘAR AƘIDA
DANGIN MIJI…
IDAN AN CIZA…
LAIFIN WAYE…?
SANIN GAIBU…
DUK ABIN DA KA SHUKA…
UWAR ƳAN MATA
KOWA YA CI BASHIN KURA…
Tb7. Dakyau, yanzun duk cikin wannan litattafan da kika rubuta, wanni littafi ne ya fito dake ko kuma ince wanne makaranta sukafi sanin ki dashi
Nabeela Dikko; Zan iya cewa mutane sunfi sanina da TARBIYYA, amma daga bayan nan sai UWAR ƳAN MAATA yay fintikau yay shura a duniyar makaranta ta yadda banyi zato ba.
Tb8. Masha Allah, kin taba saida littafin ki koko kina bawa masoya ne kawai
Nabeela Dikko: Hahhh Ina sayarwa sosai, don idan ba zan manta ba SANIN GAIBU, DUK ABINDA KA SHUKA, AUREN DOLE, KOWA YA CI BASHIN KURA duk na kuɗi ne.
Tb9. Kin taba fuskantar wani kalubalai abangaren abun da ya shafi rubutu.
Nabeela Dikko; Kowacce rayuwa bata tafiya ba tare da ƙalubale ba, ba za’a rasa ba a baya, amma yanzu sai godiya komai na tafiya daidai sai hamdala.
Tb10. Wacece tauraruwar ki.
Nabeela Dikko; Tauraruwa ɗaya ce acikin taurari wato mahaifiya mai haskaka zuciyar ƴaƴanta.
Tb11. Wanni kira zakiyi ga ‘yan uwanki marubuta.
Nabeela Dikko; Ina kira ga ƴan uwa marubuta da muji tsoron ALLAH, muyi shuka ta gari wacce zatayi yabanya mai kyau, wacce zuwa gaba zamu girbi alheri, a dinga cire ƙyashi, da hassada, da son abin duniya don komai mai ƙarawa ne, sannan komai yana da lokaci, haka in yau mune gobe ba mu bane.
A matsayin mu na marubuta ƴan baiwa, masu isar da saƙo wa al’umma, ya kamata mu san me mukeyi, me kuma muke rubutawa, mu kasance masu kawo gyara, ba masu wargaza tarbiyya ba.
Don haka mu gyara alƙalumman mu, ta hanyar rubutu me kyau, sannan mu guji rubutu marasa amfani, don shi rubutu wani kundin tarihi ne mai zaman kan shi, wanda ko bamu ƴaƴanmu da jikoki zasu ɗauko su karanta, don haka muji tsoron ALLAH a duk yadda muka tsinci kan mu.
Tb12; A karshe ko kina da wani sakon da zaki aika wa makaranta a takaice.
Nabeela Dikko; Saƙo na shi ne ina miƙa gaisuwa da godiya zuwa ga masoyan mu, madubin dubawar mu, kuma tudun dafawar mu, haƙiƙa muna jin daɗin yadda su ke nuna tsantsar ƙaunar su garemu
A ƙarshe ina kira garesu da su zamo mabiya nagari, wanda idan sun ga anyi kuskure zasu iya kawo gyara, bawai su ba da gudummuwa ba.
Sannan su kasance masu uzuri da fahimta mai kyau, idan anga marubuci yayi ba daidai a neme shi a bashi shawara ba adinga zagin shi ba, sannan masu sayen littafan nan na batsa don ALLAH suji tsoron ALLAH su daina saye, don suma suna ba da gudummuwa wurin lalata tarbiyar yaran su ta hanyar sayen da sukeyi. ina yiwa ɗaukacin makaranta fatan alheri, mu da su ALLAH ya tseratar da mu yasa mudace AMEEN.
Ton Ameen, Mungode sosai, furuci novel suna miki fatan Alheri, Allah ya kara basira
Nabeela Dikko; Ameen nima Ina yiwa furuci novels da mabiyan su fatan alheri.
Mungode sosai!
Tambayoyi da Gabatarwa; Fadeela Lamiɗo
9 comments