Advertisements
AFRICAN EGGS ROLL
1- 2 Cups Fulawa
2- 1 ‘Kwai
3- 1 Tbs Baking Powder
4- 1/2 Nutmeg
5- 2 Tbs Butter
6- 8-9 Tbs Ruwa
7- 5 Daffan ‘Kwai
8- 2 Tbs Sugar
9- 1/4 Gishiri
YANDA ZA A HADA ( METHODS )
Mataki Na – 1
– Za a hada a cikin mazubi mai dan fada haka. Fulawa, Gishiri, Nutmeg, Baking Powder da kuma Sugar, duk a wajen daya. Sannan sai a juya su su hade bakin daya.
Advertisements
Mataki N – 2
Za a sanya Butter din a cikin wannan hadin Fulawar, sai a saka hannu a nike Butter din a cikin wannan hadin Fulawar baki daya.
Mataki Na – 3
Sai a dauko wannan ‘Kwai din guda daya sai a fasa a cikin hadin Fulawar dai, sannan a kara juyawa sosai da sosai. Wanda har zuwa yanzu za a ga Fulawar dai tananan a fulawarta sai dai sauya launi da zata ta yi zuwa ruwan ‘Kwai haka.
Mataki N- 4
A wannan matakin kuma, za a zuba ruwa wanda ba mai yawa ba a cikin hadin Fulawar sannan sai a fara yin mix da hannu. Bayan dan lokaci sai a kara zuba ruwa kadan dai haka ana kuma yin mix din, har zuwa lokacin da za a ga Dough din yayi laushi kuma da kaurin sa. To daga nan sai barshi haka.
Advertisements
Mataki Na – 5
Za a rarraba Dough din har zuwa adadin yawan ‘Kwai din wato 5. Sannan sai a dunga dauka daya-bayan-daya ana bude cikin Dough din ana saka wannan ‘Kwai din a ciki ana rufewa tare da mulmulawa ya zamto ya lailaye haka.
Mataki N – 6
Daga nan idan an kammala gaba daya, za a dauka a saka a cikin Mai na Suya, sannan a Soya a zafin Mai takaitacce. Wato kada Mai din sai yayi zafi sosai da sosai kana a saka.
Mataki Na – 7
Idan ya sauya zuwa kalar Brown haka. To sai a sauke sannan a barshi ya tsane sosai… Ana iya hadawa da LEMON BIYAR ARAYE ( 5 ALIVE ) Kana a kaiwa mai HOUSE.
8 comments