Advertisements

Screenshot 20220315 200221 1

GWARZUWAN GASAR TSIBIRIN GOBIR HASSANA ƊANLARABAWA

Posted by

GWARZUWAN GASAR TSIBIRIN GOBIR HASSANA ƊANLARABAWA

GWARZUWAN GASAR TSIBIRIN GOBIR HASSANA LABARAN ƊAN LARABAWA NA MIKA SAKON GODIYA.

Advertisements

Assalamu alaikum.

Haƙiƙa dukkan yabo da godiya da kirari su tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa da gafararSa. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad (S A W), da alayensa da sahabbansa.

Iyayena; ‘yan’uwana; masoyana; da kuma ‘yan’uwana marubuta, tare da dukkan ‘yan’uwa da abokan arziƙi. Ina miƙo gaisuwa da fatan alheri a gare ku, a bisa murna da fatan alheri da kuke ta yi bisa ga wannan nasara da Allah Ya ba ni, wadda ba ta ta’allaƙa ga iyawata ko ɗan ƙaramin sanina ba. Sai don, idan rabon ya tsago da kai to fa tabbas sai da kai ɗin! Idan kuma babu kai duk duniya babu wanda ya isa ya sa da kai. (Naziru sarkin waƙa😅).

Advertisements

Dubun gaisuwa da jinjina ga Sarkin ɗiyan gobir Alhaji Aminu(Alan waƙa), bisa damar da ya ba mu domin gwada fasaharmu. Fatan alheri da jinjina ga ‘yan kwamitin shirya wannan gasa, kuma malamanmu: Kabiru Yusuf Fagge (Anka), da malam Ibrahim Indabawa. Mun gode ƙwarai da jajircewarku don ganin mun hau dokin nasara.

Ina taya ɗaukacin marubutan da suka shiga wannan gasa murna. Da waɗanda suka samu nasara. Allah Ya riƙa; Ya sa matakin nasarar kenan.

Godiya ga ‘yan ƙungiyata EXQUISITE WRITERS FORUM, da suke ta murnar samun nasarata, haƙiƙa nasarar taku ce! Ina roƙon Ubangiji Ya ci gaba da buɗa mana hanyoyin da za mu bi domin cimma nasara a rayuwa.

Advertisements

Godiya ga ƙungiyar da ta zamo tushen farinciki, wato GAMJIK. Allah Ya ɗaukaka ƙungiyar da mazauna cikinta.

Na gode sosai. Allah Ya bar zumunci; Ya ƙara wa marubutanmu maza da mata basira da hazaƙa da ɗumbun nasarori.

Daga ‘yar’uwarku marubuciya:
Hassana Ɗanlarabawa.

FURUCI NOVEL suna kara jinjinawa wannan jajirtacciyar marubuciya Hassana Ɗan Larabawa, wannan nasara tamuce baki daya.

4 comments

  1. Pingback: Gifts
  2. Pingback: Pharmaceutics1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *