WATA FITSARA
Advertisements
By
Fadila Lamiɗo
Page 26
Yadda take tafiya ahankali kafin takai gurin yayi tafiyarsa”
Advertisements
Wani iri taji cikin zuciyarta jikinta yayi sanyi gaba daya Dan haka ta koma gida”
Yaya Fatima?, Ya wuce ne? ko Zaki bishi ku tafi??
Ai Hajjah kafin naje ya tafi”
Advertisements
Ikon Allah, wani irin fushi ne wannan Yaro keyi🤔, Fatima ko kin masa wani abu ne?
A’a banyi komai ba”
Anya kuwa??
Ni ba abun da namasa Hajjah”
Jimmm Hajjah tayi zuwa can tace”
Toko Zaki bishi ne kuje can gidan ku….
Ni Hajjah anan zan zauna”
Shikenan Hajjah ta fada sannan ta nufi dakin baccinta”
Tun daga ranar, tsayon sati biyu bata sake Saka Ahmad a idonta ba, ko zuwa gaida Hajjah baya yi, kuma da alama ko waya basayi da Hajjah dan Bata taba gani ba”
************
Khadija kuwa sosai ta cire hankalinta akan wannan auren, dazaran ta tuna Ahmad ne mijin Samha ranta ke baci, dan haka take saurin kawar da tunanin duk wani abu dazai dameta”
Misalin 8:40pn taji Karan wayarta, ganin number Usman abun ya Bata Mamaki, kin dauka tayi harta katse amman nan take ya sake Kira”
Wannan karon dauka tayi batare datace komai ba takara akunnenta”
Shima shiru yayi zuwa can yayi sallama”
Amsawa tayi ahankali sannan yace”
Kedai zanga ranar dazaki canza halin ki”
Meya dameka da halina?, Ina ruwanka Dani?
Niko nake da ruwa dake Khadija, ko albarkacin Ummee ai ya isa nai ruwa dake?
Wacece haka??, nikuma a irin nawa zuciyar Banga abun daya dameni dakaiba, dazaka gane dakabar kirana, dan banga dalilin ba, babu wata alaka tsakanina dakai, toh meye na kiran?? Kaje kayi rayuwarka kabarni inyi tawa, wlh natsane ka, wlh banson jin wani abu daya dangance ka”
Murmushi yayi ahankali sannan yace”
Saboda na haramta miki abun da kike so ko??, Hmmm taurin kanki nabani Mamaki, Ina baki shawara ki gaggauta yiwa zuciyarki abun da take so, zuciyarki ni taso tun farko, kuma nasan ni kikeso har yanzun, wani rashin dibara ne ya sameki har kika bari mukai nesa da juna yanzun…….
Rashin dibara harta wuce wadda ta sameka??, Akwai wadda rashin dibara ta sameshi kamar Kai da sakeni akan bakin kishin ka natsiya, ai akan ka rashin dibara ya kare Usman”
Hmmm kedai kika sani nidai yanzun hankalina ya kwanta, kuma Ina nan Ina addu’a wata rana Zaki dawo dakin ki”
Bani da daki agidan ka, bazan taba dawowa gareka ba, har zakace wani dakina?, Mata nawa kasa aciki??
Murmushi yayi ni bantaba bawa kowa dakin ki ba, matsayin ki daban azuciyata na waddan da kike mgn daban, kuma haryau babu wacce ta maye min gurbin ki azuciyata”
Aikuwa wlh ka makara Usman dan ni babu digon ka azuciyata”
Jimmm yayi ji yayi kamar ta jefeshi da katon dutse cikin dakiya yace”
Wlh karya kikeyi, indai kinason kwanciyar hankali kibawa zuciyarki abun da take so, ni kenan”
Tsaki taja tare da fadin nima na tsaya Ina sauraron……
Karki kashe min waya Khadija, domin zancen dana Kira muyi har yanzun banyi Shiba kuma yana da Mahimmanci sosai”
Jimmm tayi tana sauraron sa”
Nasamu labarin Har yanzun Mamana Bata dakin ta, ko meye dalili??
Bani da alaka da wannan lbrn Usman, wannan kaita shafa”
Kema ta shafeki Khadija, dan Allah awannan gabar ki ajiye makaman ki muyi mgn in yaso idan mun magance wannan matsala saiki daura daga inda kika tsaya, lokacin Nima na shirya nawa kayan yakin, me kika sani akan Fatima da mijinta dan Allah Khadija?👏🏻
Ni bansan komai ba akai”
Ance min tana gidan su Hajjar ku, acen take zaune, shikuma mijinta yana rayuwa agidansa, kwanaki yakawo min karanta namata fada kenan bata bari ba, kiyi wani abu akai dan Allah……
Ni??, Allah ya kyauta, ka manta abubuwan da suka faru kenan??
Yanzun ke kinfi son takasa zama gidan mijinta, kina son ‘yarki ta zama karamar bazawara ne?, Ina son kisan aduk lokacin da kikaga namiji ya tsoro da wani abu mara kyau an gaza masa ne ta wani gurin, yanzun tana wani guri daban shima yana guri daban meye kike tunani nufinsa??
Oho muku, can ku karata, ni abun da nasani babu ruwana da wannan auren, dan haka ko kala bazance ba, intaga zata zauna Allah yabata sa’a ni yanzun daga su harkai bakwa gabana, hannuna ne dai babu acikin zancen su kuma bana son ka sake sa’kani aciki, daka Kai harsu ba sa’arku bace ni, Kai kamata aure babu sa hannuna aciki, bayi shawara Dani ba danbe zaka dauko matsala ka kawo min, daga rana irin ta yau karka Kara kawo min matsalarsu Ina Mata fatan Alheri aduk inda take amman ni banson ko ita ingani ahalin yanzun”
Kashe wayarta tayi gaba daya ta aje agefe, zuciyarta ce ta ayyyanu mata Ahmad da Samha, afili tace ni babu ruwana dasu yanzun, aure ne dai Allah yasani banso akayi ba, kuma tunda anriga anyi meye nawa?? Yanzun Samha tana gidan Ahmad kusan wata na biyu ake nema, nasan aikin gama yariga ya gama a yadda Ahmad yake, kuma Ina da tabbacin kalamar FITSARA babu irin wacce me karanta Mata ba dan shi vaka zama dashi na awa daya beyi zancen rashin kunya ba”
Tunawa tayi ance yakai karanta, jimmm tayi azuciyarta tace, wata kila gudunsa take, toh tayaya bazata gujesa ba?, Ahmad ba sa’an auren Samha bane kwara kwata, kalamansa ma sunfi karfin kunnen Samha bare aje gashi kanshi, gara ta gujeshi😭😭😭😭😭😭”
Kuka taitayi tsayon wani lokaci bakomai ke damunta ba ayanzun sai kankantar Samha idan ta nuna yanayin jikin Samha saita tuna na Ahmad wannan karon afili tace, Ahmad yabi son zuciyarsa ne kawai, Allah kataimakeni karya lalata min yariya ita kadai gareni
Airin wannan matakin da Samha take dagaji muryan mijin ma gabanka faduwa yake, har wani rama na musamman mutum keyi lokacin amarci, kama aure daidai kai kenan, Ina ga Samha data aure tuzuro, tuzurun ma mara kunya fitsararre”
😭😭😭😭😭, tsayon lokaci ta dauka tana kuka ganin babu sarki sai Allah ta mike tayo alwala daki ta dawo tana fadin cikin ranta cewa”
Aure zanyi inyi nesa, inbar garin gaba daya, inbar komai in Mata da kowa”
Tsayon wata biyu kenan Samha batasa Ahmad cikin idonta ba, kuma Babu abun daya dameta harkokinta kawai take take Yi, sosai idonta ya sake budewa dan tasaki jikinta sosai amakaranta tayi kawaye da dama, Hira sosai takeyi cikin hawayenta, gaba daya cikin wata buyu makarantar ta santa gaba daya, kowa sonyin mgn da ita yake har cikin malamai maza, domin zaiyi wuya kayi mgn da ita ta minti 15 vata saka dariya ba ba, haka kuma maza dayawa cikin malaman nason yin mgn da itane kawai sobo da kyaunta, duk da cewa akwai matan aure amakarantar Amman taki barin kowa yasan tana da aure har Aisha da suke shiri sosai”
Zama cikin mata ana Hira yasa takara sanin wasu abubuwa sosai akan aure yayin da take fin matan auren zakewa idan ana mgnr auren”
Dayawa daga acikin kawayenta dasunji irin kalamanta suke rike baki, tare da cewa wannan idan Babanki beyi sauri ya auren dake ba akwai matsala”
Tana cikin wata na uku amakaranta rashin kudi yafara damunta dan Hajjah ba kullum take bata kudiba kuma baya wuce 500, garama Daddy indai yana gari 2k yake bata kuma be cika zama agida ranar da akwai makaranta ba, dan haka kudin yake mata kadan, saidai taga kawayenta nata kashe kudi dan haka yau bayan sun dau Hanya tace da driver sa kace mishi yabaka kudi ka kawo min”
**********
Washegari taga shiya yadda zata kashe kudinta tsaf dan tasa rai zai Bata da yawa tunda rabon daya bata kudi tun tana zuwa makaranta, lisafin taitayi iri iri, koda tafito zatawa Hajjah Sallama ta Bata kudi cewa tayi tabarshi”
Bayan driver ya sauketa amakaranta tace baka bani sakon danace ka amsan min ba??
Cikin shafa kansa yace”
Hajiya yace wai nacce miki shi ba bawan garin ku ba ne”
Jimmm tayi, sannan ta juya afusace ta shiga makaranta, sosai abun yabata haushi gaba daya yau kawayenta rasa gane kanta sukayi, cikin baccin rai ta koma gida, Hajjah na kallonta tace yaya akayi kuma”
Kamar jira take tace, Hajjah kinga Uncle Ahmad ko??
Cikin Mamaki tace Ina kika ganshi??
Driver nacewa yace mishi yaban kudi shine yace Wai shi bawan garin mu ne???
Dariya Hajjah tayi sosai sannan tace”
Kema dai Fatima baki da wayau Ashe?, Ahmad nafushi dake yayi fushi ya tafi tsayon wannan lokacin daidai da rana daya baki taba tambayan sa ba sai yanzun ki aika ya baki kudi?🤔 Kenan ke bakisan zuru ba ko???”
Bayan wata 5, shirye shiryen bikin wata kawarta ake dan haka hankalin ta ya tashi sosai, anko kala 4 suka fito dashi dashi, gashi bikin yarage saura sati daya yau duk kawayenta sunyi ita ta gagara har yanzun gashi kwana uku ya rage afara biki”
Daddare ta samu Hajjah adaki tace”
Hajjah kibani aron wayar ki in kira Abbana”
Lafiya dai ko?
Lafiya lau so nake ince masa yamin ankon bikin Zainab saura kwana 3 afara bikin fah”
Cikin Mamaki Hajjah tace toh ai indai Hakane Ahmad yakamata ki Kira”
Jimmm tayi sannan tace ai Hajjah kema ai kinsan bazai saya min ba Abba kuwa Ina mishi mgn zai saya min”
Kinaji Fatima idan Abban naki ya saya miki Ahmad kuma ya hana fita fah??
Cikin sauri ta dago ta kalli Hajjah sannan tace”
Hajjah zai hanani ne? Kawata ce fah?
Amman dai ai kinsan Saida izinin sa zaki fita dan haka indai kinason ayi bakin dake kibi driver yakai ki gidan sa ki gaya masa, to in kikai haka har anko saiya sai miki
Shiru tayi tana Mamakin yadda zata haddu da Uncle Ahmad bayan tsayon kusan wata 7 bata ganshi ba, bawai Bata son ganin sa bane kawai zancen Auren ne tsakanin su batason ji, duk kuwa da tsananin son auren da take ji musamman yanzun da kanta ya Kara wankewa akan aure, sosai take son auren amman akan Ahmad kwata kwata batason Jin zancen aure tsakanin su, idan akwai abun da ta tsana be wuce zancen auren Ahmad ba dake kanta”
Ganin inda tai shiru cikin tunani Hajjah tace”
Kinga Fatima?, Jiki shirya cikin sauri dan kiyi maza ki dawo, idan ya ganki shima zaiji dadi”
Mikewa tayi jikinta duk sanyi tariga da tai wanka kaya kawai ta canza sannan ta sanya babban hijjabi ta fesa turare”
Tuni Hajjah ta gayawa Driver dan haka acikin motar ta same sa”
Sannun ahankali yake Jan motar yayin da Samha keta kallon garin da duhun dare ya hadu da fitulu, sosai garin ya burgeta domin ko da tana gidan Abbanta Bata fitan dare”
Yanayin ne yai Mata dadi sosai tare da burgeta taitai kalle kalle, zuwa can ta tuna gidan Uncle Ahmad fah zata, hankalin tane ya tashi sosai wata kusan 7 rabon data kanshi ko gaida Hajjah baya zuwa, wata zuciyar ce tace kika sani ko in kintafi makaranta yana zuwa?
Hakane idan natafi makaranta kila yana zuwa gurin Hajjah, wata kila shima yanzun ya tsaneni kamar yadda Nima natsani auren”
Gidan taka sunsa Kai, kusan zata iya cewa wannan shine zuwanta nafarko gidan Dan waccen lokacin bata cikin hayyacin ta, sosai yanayin gidan ma ya burgeta madaidaicin gida ne wadda aka kashewa naira”
Motocin Ahmad ta hanga guda biyu daga can gefe ma wasu motucine wadda take kyautata zaton daya ta Galadima ce, dayar ta kurawa ido tarasa gane kota waye
Sakkowa tayi ta kalli driver tace toh kafa jirani tare zamu koma”
Hajiya tagaya min Ina jiran ki”
Juyawa tayi ta nufi gidan da hasken fitulu ya haske ko Ina tare da fadi cikin zuciyarta kenan suna tare da Galadima, hakan yayi daidai da isarta kofar da zata sadata falon da take tunanin tanan din zata shiga ahankali tasa hannun ta ta kwankwasa kofar………..
Mmn Yazeed
5 comments