WATA FITSARA
Advertisements
By
Fadeela Lamido
PAGE 30
Mamakii abun yaita bashi Wai shine yau gabansa ke faduwa dan zai hadu da Khadija
Advertisements
Saida yayi sallar la’asar alayin tukuna ya shiga gidan”
Yana saka kafa agidan yara suka fara kawo masa gaisuwa Dan sun jima basu jishi ba”
Dakin Inna yalwa yafara shiga ya gaidata sannan suka Dan taba Hira, yawancin hirar tasu fada taita masa akan ya dan rika leko su, daga bisani ya nufi dakin Inna wato mahaifiyar Khadija”
Advertisements
Sallama yayi Khadija dake zaune bakin gadon Inna tanajin sallamar sa ta hade fuska”
Atabarmar dake shinfide tsakar dakin ya zauna yashiga gaida inna”
Cikin sakin fuska Inna take amsawa sannan takara da cewa wannan zuwan naka dai ba zuwan mu bane”
Kansa akasa yadanyi murmushi sannan ya juya kansa yace Ina wuni”
Mikewa Khadija tayi cikin sauri tabar dakin yayin da Ahmad din yabi kafafunta da kallo dan ya kasa Dagowa ya kalleta”
Sai wannan lokacin ya iya kallon Inna tare da gyara zaman sa sosai yace Inna ina Fatima fah”
Fatima nadakin uwarta Ahmad inajin bacci take”
Jimmm yayi sannan ya dauko wayarsa daga cikin aljihunsa yafara kokarin kiranta”
Ahmad kaje dakin mana gaka acikin gida kuma saikace bakon”
Jimmm, yayi sannan ya mike ya ya fito dakin”
********
Ke!!! Samha tashi ki fita”
Cikin yanayi irin na me bacci tace Ina zani Umma bacci nake ji fah”
Eh tashi kije dakin Inna kiyi baccin acan kin tare min gado Ina son na kwanta”
Matsawa tayi ta koma can gefe tace ga guri ki kwanta”
Nace dai ki tashi ko?? Tashi tayi zaune tana ya mutsa fuska yayin da Khadija ta nufi kan gadon da niyar kwanciya Ahmad ya rangada sallama abakin kofar yayin da Samha tai saurin tsallake Khadija ta kwanta abayanta”
Ganin irin gigicewan da Samha tayi kuma tasan lallai Ahmad din shigowa zaiyi yasa Khadija saurin tashi ta sauka agadon tare da bige hannun Samha data rike ta dasu ta nufi fita, abakin kofar Ahmad ne tsaye ahankali ya sake cewa Inna wuni”
Lafiya ta fada tare da wucewa abun ta”
Dakin ya shiga yayin daya zauna kujerar daya saba zama idan ya shiga dakin ahankali yace Fatima”
Shiru tayi ta rufe ido kamar me bacci, nasan ba bacci kike yi ba, zo sako ”
Shiru tayi dan haka ya mike yayin da yana nufar gadon Samha ta saki Kara, dariya yayi tare da fadin”
Tsorona kike Wai, ni ba abun da zan miki zuwa kawai nayi in duba ki sannan in miki kashedi karki Kara fita koma inane batare da izzinina ba, idan Kuma kinkiji zakiga abun da zan miki”
Ahankali tace naji”
Yayi kyau yanzun yajikin naki”
Ninaji sauki Uncle kawai jikina ne yake min ciwo”
Har yanzun??
Eh”
Kuma kinashan maganin dana baki?
Ai nagama Shan su ma”
Toh sannu Kona maki tausa”
Sosai ranta keson tausan saidai tsoronsa take”
Bakice komai ba, nace in matsa miki jikin?? ya sake maimaitawa”
Eh indai bazaka min komai ba”
Murmushi yayi sannan yace ni ba abun da zan miki, mikewa yayi ya nade hannun rikarsa ya fara matsata ahankali yayin data shiga lumshe ido”
Kinajin dadin ko?
Ummm”
Murmushi yayi sannan yace”
Kinga dakin zauna acan gidan mu dakin fi Jin dadin ki, indai Ina gida bazan gaji da tausaki ba, harsai jikin ki yabar ciwo”
Umm’umm ni bazan zauna ba, nafi son gidan Hajjah”
Baki da wayau yariya, dakin bini muje gidan duk abi da kike so zan miki, kudi kuma da kanki Zaki dauki abun da kike so”
Banaso kudin Uncle, ni Ina da kudina basai kabani ba”
Ina kika same su??
Wadda kabani ne da zani bakin kawata”
Meyasa baki kashe ba?
Aina zan kashe bayan banje makaranta ba har yau ko in ara maka idan nafara zuwa makaranta saika bani”
Murmushi yayi sannan yace eh ara min”
To dauka ajakata”
Kinsan menene??
A’a
Zan Kara miki wani akai kibawa Maman ki, nasan Kona Bata bazata amsa ba sai kice Mata kece kika bata”
Toh tace adaidai lokacin da Bacci ya fara daukanta”
Tabbatarwa dayayi tayi bacci, ya tsuguna Ya sunbaceta sannan ya fice”
*********
Tsaye Khadija tayi akan Samha dake bacci da alama tajima dayin baccin, to me ya zauna yayi adakin alhalin tayi bacci”
Tunawa tayi da yadda take sawa amtsa mata jiki sannan take iya bacci tsaki tayi sannan ta kwanta akasa”
Sai can ta tashi wanka tayi ta sauya kaya, duk abun da take Khadija nabinta da kallo bayan tagama tace”
Yaushe Zaki tafi??
Cikin yamutsa fuska tace nima bansani ba”
Be gayaiki ba??
Umma ni nayi bacci bamma sam lokacin da ya tafi ba”
Jimmm Khadija tayi cikin ranta take fadin kodai ciki gareta, wannan wanni irin bacci ne??.
Juyawa tayi ta sake kallon Samha sannan tace, to kidai shirya anjima ki wuce gida, ninagaji Zaki takura min”
Jimmm Samha tayi tare da runtse Ido kawai gani take Ummanta ta rage sonta
Cikin kuka tace Umma korata kike yi”
Toh me zaki zauna nan kimin”
Hawaye tacigaba da sharewa duk da tausayin ta da fara ji dole ta kora ta dan ko sunan Ahmad batason akira bare Kuma ganin sa”
Ganin kukan da Samha take yayi yawa tausayinta ya kamata sosai tashi tayi ta koma kusa da ita ta zauna sannan ta jawota jikinta tana fadin”
Wai kuka kikeyi Dan kwai nace kije gidan ku?
Hawaye ta share sannan tace”
Umma yanzun bakya sona”
Eh naji, indai akan nace kije gidan ku kikecewa banson ki aje ahaka, salon ki zauna nan aita min sintiri da iskanci iri iri”
Jimmm tayi domin tafara gano inda Ummanta ta nufa, zuwa can tace”
Nidai Umma kibar cewa intafi, Hajjah tace kwana uku zanyi yau kuma kwana na daya”
Ai kwana uku?, Toh Amman ba’anan dakin ba kuwa, saiki tattara ki koma dakin Inna”
Toh zan koma Amman Umma dan Allah kidan dannan min nan gurin ciwo yake min”
Kallon gurin tayi bayanta take nunawa ahankali ta shiga matsa mata tare da fadin”
Yaushe kika fara ciwon gabobin jiki ne?, Daman can kinayi ko daga baya ne??
Ni bantabayi ba Umma yau kwana biyar kenan”
To faduwa kikayi ko hakan nan??
Ba Uncle bane……..🤭
Rutse idon Khadija tayi Jin ta anbaci Uncle, hannunta tasa ta tureta tare da fadin”
Matsa kiban waje”
*********
Misalin 9:12pm Ahmad ya sake dawowa akaro na biyu”
Dakin Inna Yalwa duk ya same su kusan kowa na dakin yara da manya”
Khadija naganin shigowan Ahmad ta maida hankalinta Kan wayarta, shikuwa Ahmad yara ya hango bisa bayan Fatima sai takata suke, cikin tsawa yace miye haka??
Sosai yaran dake wajen suka firgice, ahankali Khadija ta dago ta kalleshi yadda ya maida hankalinsa gabaya inda Samha take yana fadin”
Baki da Hankali ne zaki zauna ana taka ki?
Kallonta ta maida gurin Samha data shagwabe tana fadin”
Toh ai ciwo nake ji kuma kasani ai😫
Kansa ya shafa, sannan ya yace, yi hakuri to ki tashi”
Cikin sauri Khadija tamaida hankalinta gunsa cikin yanayi irin na tashin hankali taga ya karasa Gaban Samha yasa hannunsa ya dagata yana fadin”
Dan nasani bashi zai hana ni fada idan kinsa adannaki ba, anya ma kuwa kin shanye maganin ki?
Nina gama shan su fa😔”
Amman be daina miki ciwon ba??
Yadai rago’
Daidai inane??
Kwankasonta ta nuna masa sannan tace nan yafi min ciwo”
Hannunsa ya mika fari tass me daure da bakin agogo wadda ya kara fito da farin fatan sa ya rike kugunta tare da dannanwa kome ya tuna kuma saiyai saurin waigawa hada idon da sukayi da Khadija yasashi saurin zame hannunsa”
Itama Khadija cikin sauri ta kawar da idonta”
Shima Ahmad hannunsa yasa ya dafa guiwansa tare da mikewa tsaye ya kalli Inna yalwa yace Inna aiki ya sameki
Dan Allah ki danna mata”
Dariya sukayi gaba daya daki, Amman Banda Khadija data daure fuskanta tamau”
Mikewa yayi yana fidin barin je indawo mu wuce gida”
Yana fita Inna yalwa tace to ko gasa jikin za’ayi ne?, Taso mugani”
Cikin daure fuska Khadija tace dan Allah Inna rabu dasu ta tashi ta bishi, wannan ai iskanci ne”
A’a Khadija lalura ce fah”
Samha ta kalla sannan tace Dan Ubanki ki tashi ki bishi”
Ba inda zata ai zai dawo su tafi yace, haba Khadija kika sani ko rabo ne yazo da hakan?
Itako Samha fadi take niko yadawo ba yanzun zan koma ba Hajjah tace kwana uku zanyi”
Tsaki Khadija taja sannan ta mike tabar dakin”
Koda takoma dakinta tunani ta shigayi Ahmad bashi da kunya har yanzun sannan wato so yake ya nuna min wani abu ya shiga tsanin su, tirrr gashinan duk ta kasa sukuni sai faman ciwon jiki”
Har kusan sha daya nadare tana zaune tana tunanin dan kulawa tasan zai bawa Samha kulawa amman tana tausayawa Samha akan auren Ahmad”
Vaccine ya dauketa batare data shirya ba, yayin da tana tsaka da baccin taji Muryan Ahmad yana Sallama abakin kofarta”
Tashi tayi zaune tare da fadin nashiga uku, Samha tagani kwance gefenta da alama baccinta yayi nisa duka takai Mata yayin data tashi zaune”
Ana Sallama”
Cikin yanayi irin na me bacci tace”
Ni? Waye”
Kije ki gani mgn”
Sakkowa tayi ganin Uncle dinta tace uncle baka tafi ba??
Inje Ina?, bayan gaki anan, dauko mayafin ki kizo mutafi”
Ni Hajjah cewa tayi kwana uku zanyi”
Keni bawata Hajjah, Hajjah ce ke auren ki??
Duk da cewa kasa kasa suke mgnr Khadija najin su kasancewa dare ne lokacin kusan Sha daya da rabi ne”
Muryan Samha taji tace, nidai ita tace na kwana uku”
Ke!! Wai Ina wasa dake ne?
Uncle dare fa yayi Hajjah ma tayi bacci yanzun?
Aiba gidanta zamuba, dare ya riga yayi can gida zamu dasafe saina kaiki”
Cafdi, wlh Uncle har yanzun jikina bebar ciwo ba”
Kara kasa kasa da murya yayi sannan yace”
Na lura dake, kin fiye son jikin ki da yawa, cikin kwanakin nan duk inda kika zauna sai kinsa an danna ki, banzaci haka daga gareki ba, waima me akayi ne da kike nuna jikin ki ya zama gyanbo??
Kuka ta fara tare da juyawa cikin dakin shikuma fadi yake Ina jiran ki?
Runtse Ido Khadija tayi ji tayi kukan Samha namata zafi a cikin zuciyarta, bataso Ahmad yaji muryanta dan haka tai mata alama da hannunta cewa ta wuce ta tafi”
Kuka ta Kara sakawa tare da zama akasa, ahankali Ahmad yace”
Fatima inajiran ki fah”
Kofar ta kallah sannan takarai Mata mgn”
Dauki ido Samha tayi daga gurin Khadija tana cigaba da kuka”
Yana daga bakin kofar yace”
Kimata mgn tazo mutafi
Lumshe ido Khadija tayi domin tasan Ita yake nufi, bargo ta jawo ta rufe kanta tare da toshe kunnenta Amman duk da haka tana jiyo yadda yaita fama da ita taki fita, takon tafiyansa dataji yasa Khadija saurin mikewa, tace da Samha tashi maza ki bishi ko tafi”
Cikin kuka tace Umma wlh bafah gidan Hajjah zai kaini ba gidansa fah zashi dani kuma ni jikina bebar ciwo ba…..
Ni ban tambayeki ba ko lahira zai kaiki dole ki bishi tashi tashi tukan na mike”
Mikewan Khadija tayi yayin da Samha tai saurin mikewa sosai take kuka har Inna tajiyo kukanta ta fito”
Yaya akayi?? Inna ta tambaya”
Cikin kuka Samha tace Wai dole sainabi Uncle”
Eh kwarai dole kibi Uncle tunda Uncle be yadda ki kwana nan ba, Khadija da gaskiyarki neme madoki ki hada Mata dashi”
Komawa Khadija tayi ta zauna yayin da Samha ta dauki Hijjabinta tasa tare da zafgawa Inna harara menayi da za’a dakeni😏
Dole dai kibi mijin ki maza muje”
Gaba Inna tayi ta tsaida Ahmad dahar yayi kwana Samha ta fito tana kunbure kunbure yayin da Inna taga shinata mota take cigaba da fadin”
Wawiya kawai, intamaka rashin kunya ka bata kashi”
Motar ya tada yayin da Samha ke share hawaye take fadin ko Ina ruwanki oho”
Cikin murmushi yacewa Inna nagode Inna, sannan ya juya ya kalli Samha adaidai lokacin da take fadin
Ni banson shishigi……
Ya isheki haka, Ahmad ya fada sannan ya figi motar yana me sauke ajiyan zuciya”
Sunyi nisa sosai tace Uncle dan Allah gidan Hajjah zaka kaini”
Ke!!! Karki raina min hankali gida zamu tafi, yau kwana nawa, haba ai nayi hakuri”
🙄 Ai jikina beyi sauki ba uncle”
Jikin ki naga alamar bazai warke va, nagaji da jiran shi, inaga rashin sabo ne ahankali Zaki saba”
Uncle wlh…….
Ke!!!, Shiiii🤫 banson ko kadan inji kina kirana Uncle da daddare, ki danashi sai kuma gobe da Safe……..
5 comments