WATA FITSARA
Advertisements
By
Fadeela Lamiɗo
Tashi yayi zaune yayin data da Samha ta shiga hada kayanta cikin karamin akwati yana kallonta hartayi ta gama fuskansa babu yabo babu fallasa”
Hajjabi ta saka yayin da tashiga Jan akwatin tana rike da karamin Jakarta ahannunta”
Advertisements
Tsayawa yayi ta shiga gabansa sannan yabita abaya, yana kallon yadda akwatin ke wahalar da ita
Hannunsa ya zuba cikin alhjihu yana kare Mata kallo”
Bayan ta isa gaban motar kuwa rasa inda zatayi tasata ciki tayi dan haka ta juyo ta kallesa Uncle dan daga min”
Advertisements
Wa?? Ni? Allah ya kyauta, zagayawa yayi ya shige motar daker ta iya saka wa yayin datazo hawa motar kayan dake cikin karamar Jakarta ya zube, kudi ya hanga watse akasa wadda baya tantama kudin da ya Kara matane cewa tabawa mamanta, tsintan kansa yayi da rashin Jin dadin hakan ko taki amsa ne🤔
Tattarawa tayi ta kwashe sannan ta shigo ta zauna, Hanya suka dauka bayan ya daidaita motarsa akan titi ya kauda kansa can gefe tare da fadin”
Wannan ba kudin da mukayi zakibawa maman ki bane??
Kallonsa tayi yayin dataga baya kallonta gyara zamanta tayi tana fadin ai kudina ne”
Inace kice ranta min zakiyi……
Fasawa nayi”
Jimmm yayi tare da kin kallonta zuwa can yace”
Toh meyasa baki Bata nawa wadda nakara miki akai ba”
Kona batama ba amsa zatayi ba fada ma zataita min”
Aida saiki dawo min da kayana ba ki tattara ki zuba ajaka ba ga uwar ‘yan son kudi”
Kallonsa tayi sosai yayin da shima sai wannan lokacin ya kalleta fuskansa daure”
Toh yanzun kai saika amsa, Abbana kuwa baya haka”
Me zai hanani karba nida hakkina”
Cikin fushi tasa hannunta ta fido kudin gaba daya ta zubashi jikin sa”
Hannunsa daya yasa ya tattara yazoba aljihu yana me kawar da fuskan sa dan kartaga murmushin sa”
Fushi tayi sosai yayin data maida hankalin ta wajen kallon tati”
Shima gaba daya mayar da hankalin sa yayi wajen tukin sa, yana daf da shiga layin wayarsa tafara gara, ahankali ya mika hannunsa ya dauki wayar aunty Saude ce, yana dauka tace”
Ahmad kuna Ina gani gidan ku”
Da gaske aunty??
Dagaske harma munfito daman unguwa mukaje nace barin biyo in ganku”
Ayya yi hakuri Aunty, gani ahanya yariyar nan ce ta kular dani gurin Mamanta zan kaita nahuta”
Subuhallahi, kayi hakuri mana Ahmad yariya ce dole saikayi hakuri da ita”
Ainayi Aunty Dan bakisan irin kalamin da take bane kuma ai tasan abun da take idan yariyace ai tana da wayaun ta”
Karkace haka Ahmad, yanzun meye amfanin kaita wajen Khadija?, Khadija fa bason auren nan take ba tayi shiru ne kawai dan taga anfi karfinta, kuma Mahaifinta bazai ji Dadi ba idan kayi haka kome yake faruwa shiya kamata ka fara sanarwa ni aganina baruwanka da Khadija tunda ba ita tabaka aurenta ba, ta inda aka hau tanan ake sauka Ahmad, dan Allah kayi hakuri ka maidata gida kana nusar da ita ahankali”
Jimmm yayi cikin nazari zuwa can yace”
Shikenan Aunty Amman yanzun barin kaita wajen Babanta yaga abun datayi, tana takura min da yawa Aunty ni fa har yanzun ban more angwancina ba kamar yadda kowanni ango keyi”
Karka damu da wanna Me tayi yanxun??
Kayanta ta hada akwati kuda”
Dariya Aunty saude tayi sosai yayin datasa shima murmusawa yana me Satan kallon Samha”
Shikenan kayi haka din da alama dai Samha danyen kai gareta”
Bayan sun gama waya da aunty Saude juya akalar sa yayi, yayin da cikin Samha ya duri ruwa”
Cikin rarraba Ido tace”
Karka kaini gurin Abbana”
Banza yayi da ita yana me sharara gudu”
Cikin Dan kankanin lokaci suka isa yayin da hankali Samha ya tashi sosai”
Sakowa yayi yayin data rigasa sauka ta nufin shiga ciki da saurin ta”
Dakata malama kin manta da akwatin ki”
Waigowa tayi ta hararesa tare dacigaba da tafiya, konawa yayi ya dauko akwatin sannan ya biyu bayan ta”
Kai tsaye falon Abbanta ta nufa yayin da yake binta abaya saidai Bata San ya dauko akwatin ba”
Tana shiga ta nufi Abbanta dake zaune sanye da Jallabiya takardu barbaje agabansa”
Dagowa yayi ya kalleta Mamana kedawa da daddaren nan??
Nida Uncle ne😔, hakan yayi daidai da shigowan Ahmad cikin Sallama dauke da akwatin Samha”
Gaban Alhaji Usman yankewa yayi ya fadi, bashi kadai bama hardana Samha, cikin faduwan gaba yake fadin”
Ahmad lafiya kuwa?
Cikin murmushi yace lafiya lau, ajiye akwatin yayi sannan ya karasa ya zauna akasa”
Cikin girmamawa suka gaisa yayin daya shiga masa wani irin kallo dan ya kosa yaji meya kawo su da daddaren nan kuma”
Kallon Ahmad yayi cikin kallon cikin idonsa yayi yace me yake faruwa ne Ahmad? Rigimar Bata karewa bane dazon Momy tace can gidan naku ai”
Eh mun hadu, gatanan rigimarta tayi yawa nayau daban na gobe daban ita burin ta kawai in saketa ne”
Juyawa yayi yawa Samha wani irin kallo sannan yace karka biye mata Ahmad, bawani abu bane ke damun ta rashin duka ne”
Kuka Samha tafara yayin da Abbanta ta yake Gaya masa yadda sukayi da ita da safe shima Ahmad nan yashiga gaya masa dalilin daransa ya bacci saidai cemsa kawai yayi tace yanaiwa Mamanta rashin kunya”
Bayan yagama Gaya masa Alhaji Usman yace aina Gaya maka rashin duka ke damuta”
Cikin kuka tace Abba ai yana dukana fah, dukan dataji abakinta yasata shiru batare data shirya ba”
Cikin fada yace wayasa bakinki anan gurin mara mutunci kawai, ban taba tunanin haka daga gareki ba kwata kwata, kinban Mamaki amman ba laifinki bane nasan maganin abun”
Cikin kuka sosai tace Abba dan Allah kayi hakuri😭
Idan nasakejin bakin ki nan gurin batare da ansa bakin nakiba ranki zaiyi mugun baci”
Kanta ta sukuyar kasa cikin kuka sosai yayin da kan Ahmad ma ke kasa”
Shiru Alhaji Usman yayi zuwa can yace”
Shiga ciki Ina zuwa”
Mikewa tayi ta shige ciki yayin da Alhaji Usman ya mike yabi bayanta yana fadin barin ganta Ina zuwa”
Jigum Ahmad ya zauna yana me addu’a Allah yasa daga yau komai yayi daidai👏🏻
Falon Aunty ta shiga tana me kwala kiran sunan Aunty Amman shiru, dakinta ta nufa tajishi rufe gam, juyowa tayi tana sake kwala kiran Aunty”
Alhaji Usman dake kokarin zama afalon yake fadin”
Batanan”
Ina taje Abba ??
Gidan su ya fada yana kokarin daura kafarsa daya akan daya”
Gabanta ne ya fadi sosai harma ta dafe domin tana zargin rabowa sukayi”
Cikin kausasarsiyar murya yace”
Zonan”
Gabansa ya nuna Mata saitin kafarsa dan haka ta isa gurin ta zauna”
Sakko da kafarsa yayi yasata atsakiya sannan ya rike kunnuwanta duk biyun yana fadin”
Idan kika min kuka ko ihu bazan sake ki ba, tambayan ki zanyi amsa kawai nake son ki bani”
Tushe bakinta tayi sabo da irin radadin da take Jin dalilin murde kunnenta da yayi gurnani kawai take yayin da yasake cewa idan kika kukura kikai kuka bazan sakeki ba nagaya miki, Ina jinki me kike nufi??
Cikin azabar radadi tace bakomai Abba”
Zafin be shigekiba kenan, inajin ki meyasa bazaki kwatar da hankali ki zauna gidan mijin ki ba???
Kara murde kunnen yayi Dan haka tace”
Abba shine yakewa Mamana rashin kunya Kuma tace min ya taba cewa yana sonta”
Hannunsa ya ciro akunnen daya ya make bakin ta dashi yayin da yake fadin”
Ai kinji kince ya taba, kina nufin yanzun baxaki zauna dashi ba kenan?? Ita Khadija ta iya bude baki ta Gaya miki wannan mgnr??
Hawaye take domin har yanzon yana rike da kunnenta yana gana Mata azaba”
Ainu tuntuni ne ta gaya min…..
Mari yakai mata akaro na farko yana kara fadin, wannan ce kadai hujjar ku keda Khadija???
Kuka take takasa mgn”
Bazakimin mgn ba??
Cikin matsanan cikin kuka tace a’a
Ina Jin ki??
Ai kuma yana da budurwa Abba”😭😭😭
Lumshe idonsa yayi sannan ya sake kunnenta yana fadin”
Ina jinki bani labari??
Cikin kuka sosai tace budurwa yake da ita a Office dinsu”
Waye ya gaya miki??
Abba ganinta nayi a Office din shi”
Hmmmm Fatima kenan daga ganin yariya saikice budurwarsa ce??
Ai Sweet heart yake ce mata 😭😭😭😭
Kawar dakai Alhaji Usman yayi zuwa can ya juyo yana fadin”
Kudai mata duk halin ku gudane, ba manyan ba bayaran ba, kinga nabargo dai Allah yabashi dablman ya Kara da Mata uku bayan ke dan haka Banga dalilin dakawai dan kin ganshi da wata ba zaki tada hankalin ki, ki nutsu ki rike auren ki”
Kuka take sosai yayin da Alhaji Usman yacigaba da cewa mgnr Mamanki Kuma wannan zancen tun lokacin kuruciya ne, kinsan da Mamanki dashi Ahmad tare suka tashi kansu daya kawarsa ce Mamanki tare sukayi wasa har dambe sunyi karewar rashin kunya, ada dan haka babu wani zancen rashin kunya dayai mata tunda kawarsa ce, inason daga yau ki cire wannan aranki, idan ma da da irin wannan ayanzun babushi Dan haka abar zance kawai”
Cikin kuka ta amsa sanan ya mike yana fadin karna sake ji”
Toh tace tana me share hawaye”
Komawa yayi ya same Ahmad yana murmushi ya zauna yana fadin”
Nagama da ita zata fito yanzun ku tafi, yadda ka fada din hakan ne abakinta saidai takara da cemin kana da budurwa”
Ni din??
Eh kaifa tace a Office din ku”
Shiru yayi yana nazari zuwa can ya dago yace gaskiya bani da wannan lbrn kawai…….
Aina Gaya Mata ma namiji mijin mace hudune, kawai dai sharawan da zan maka ka guje idonta har asamu komai ya tafi daidai”
Godiya yaitawa Abba aransa yana Mamakin Samha”
Lokacin da Samha ta fito yadda yaga fuskanta akunbure ya tabbatar da an mareta ne sosai kumatunta ya kunbura”
Bayan sun baro gidan Alhaji Usman Babu mema wani mgn, hawaye kawai Samha ke sharewa har suka isa gida”
Bece Mata kalaba ba haka suka kwana tana gefensa tana share hawaye”
Da asuba bayan yaje masallaci ya dawo samunta yayi tana share hawaye akan Sallaya zama yayi ganin taki tashi ya wuce toilet”
Wanka yayi ya fito har yagama shiryawa bata kallesa ba”
Bayan ya gama tsaf yace Nina fita”
Kamar da dutse yake mgn haka harya gaji ya fice”
Da Yamma ma baka ya dawo ya sameta kwance tayi runda ciki akan gado”
Fatima, bakibar kuka ba har yanzun”
Banza tayi masa”
Kinci abinci??
Nan ma Banza ta masa, zama yayi agefenta ahankali ya daura kansa agadon bayanta tare da kantowa Kadan, Fatima dan Allah ki kwantar da hankalin ki muyi zaman dadi”
Kamar jira take tace bakai bane kakaini gurin Abban na yamin duka kuma ya hanani kuka”
Yi hakuri, namiki alkawarin bazan sake ba, amman kema ki gyara halin ki”
Ni daman can halina agyare yake, to da akamin dukan kaji Dadi ko??
Banjiba, ni ba nufina adake ki ba, inaso ne kawai muyi zama me kyau”
Kaji mana, inda bakaji ba ba ai tun jiya nake kuka ko kallo na bakayi ba”
Murmushi yayi kansa na kwance agadon bayan sa yace”
Kina son in lallasheki ne??
Shiru tayi Dan haka ya saka hannun sa ya share hawayen fuskanta yana fadin Allah ya huci zuciyarki ginbiyata…….
Ginbiyar ka na Office”
Mirginota yayi, Yauwa inajin ki, kincewa Abban ki Ina da budurwa, kinsa narasa abun fada ya yadda dani, banda kuma kiyayyar da kike gwada min harda sharri Kuma??
Tana kallon cikin idonsa tace ban maka sharri ba ranar da kajeni asibitin ku aina ganta cikin Office din ka”
Nidin ?, Fatima kiji tsoron Allah”
Wlh kuwa harma kace mata Sweet heart”
Lumshe ido yayi lokaci daya ya saki murmushi sannan yace”
Ok na tuna ta yariyar da kike mgn”
Wato suna da yawa ‘yan matan naka”
Kirjin sa yasa ya danne nata yana me lushe Ido yake fadin A’a kwaya daya ce”
Aina take??
Gatanan Ina kwance ajikinta”
Wlh ba gaskiya bane Uncle Sweet heart din fah??
Kina son in gaya miki wacece Sweet heart din?, Sai kin min alkawarin kinbar dukana da yakushina”
Toh wai dukan ma dabaji kake ba”
Eh ni banason inajin dadi ana dukana, maimakon ki dinga huramin iska Ina Kara hawa sama, saiki dinga kanna min cizo Ina komawa baya, shiyasa kike Shan wahala Ina dadewa ban barki ba”
Kasa kasa tayi da murya Kai ma ne kamar wani maye??
Eh mayen ki ba”
Uncle😫 nikadaina min irin wannan mgnr, ka gaya min wacece ita”
Sai kin bar mintsini da cizo……
Nabari to”
Lumshe ido yayi Yauwa koke fah ita wannan yariyar bani da wata alaka da ita kawai sunanki gareta shiyasa ma har nake mata wasa nake kiranta da sunan”
Jimmm tayi sannan tace toh karka sake, ka kirata da Fatiman ta”
Angama ranki ya dade”
Lumshe ido tayi yayin da Ahmad ya koma ya kwanta agadon yana me lumshe ido”
Hannu yaji agemun sa yana yawo ahankali take shafa sajensa Kara lumshe ido yayi yana me Jin wani irin farin ciki”
Bakinta yaji tana sunbatan duk inda hannunta ya daba daga can yafarajin harcenta acikin gemun sa, wani irin yanayi ya shiga wadda ya kasa fassarashi aransa yake tunanin anya kuwa itace, sharkaf ta jika gemon sa da miwunta, yayin da hakan yasa gaba daya Ahmad ya fita daga hayyacin sa ahankali ya zagayeta da hannunsa yana me sunbatan fuskansa”
Yarigada ya gigice dan haka nan danan suka shiga kokawa”
Sosai take bashi hadin Kai koda daman haka take saidai wannan ranar yana tunanin ta hura masa iska”
Sunjuma suna cakuda juna kamar koda yaushe yana isa gareta tasa kuka kamar yadda ta saba dukan sa take tare da cizo”
Shima cikin yanayi irin na wadda ya rikece yake fadin”
Kinyi alkawarin kinbar cizona Fatima, cikin kuka kuka yake mgnr Dan itama kuka tasa ba ita ctabari ba Saida yabar jikinta”
Rungumeta yayi sosai ajikin yana me samata albarka nutsuwa ya samu sosai saidai har yanzun kuka take”
Saida hankalin sa yagama dawowa jikinsa ya shiga lallashinta”
Hakane yacigaba da kasancewa tsakanin su har suka dauki tsayon wata biyu agidan duk sadda yazo neman hakkin sa zata bada hadin Kai Amman da kuka ake karewa koda ace sau biyu ya nemeta arana duk saitayi kuka Kuma kukan da take jimawa Bata bari ba saiyaita lallashinta”
Ayanzun sun samu cikakken shekara kenan da aure yayin data Kara cika komai nata nata Kara bayyanuwa kirjinta nakara cika”
Tamaida hankalinta akan makaranta ajin karshe take tare da Ahmad suke fita idan ya kaita makaranta ya wuce Office ita kuma da antashi driver ke maidata gida”
Girki ko wanni iri tanayi masa Kan ya dawo takuma Gyara ko ina yana daukan Kamshi”
Sosai Ahmad ya saba da jikin Samha ko kadan baya gajiya, beki yayi kullum sau kaza ba, saidai yawan kukanta ke damun sa, wada ayanzun ya lura abun bana kare mabane”
Tadaina cewa Bata sonshi tun bayan da yakaita wajen Abbanta daidai gwargwado ta nutsu kawai anan gurin ne yake da matsala”
Magunguna babu irin wadda be kawo mataba tunanin sa ko wajen ne ke Mata zafi saidai ko kadan bata rage kukanta bare yasa ranzata daina, badan Allah yasa dabon yakushi baya zama da duk jikin sa tabo ne”
Wannan dalilin yasa yanxun ya rage kusantan ta, sai ya Tara sha’awarsa ya rasa yadda zaiyi da ita sannan yake zuwa gareta dan haka yanzun yake zama kamar mara lafiya, itako Samha sosai tai kiba duk abun da take so shi yake mata”
Damuwar Samha kuwa baya barinda zuwa gidan kowa, ko gidan Hajjah baya kaita datayi mgn saiyace saitayi hankali”
*********
Ahmad zaune cikin damuwa, yarasa hanyar da zai billowa Samha, Khadija ce tafado masa arai afili yace”
Waye zan iya tara da irin wannan matsalar?, Nasan da ace Ba Fatima nake aure ba Khadija zan fara kaiwa ita, Kuma ko yanzun ma Ina tunanin tana da abun Yi akai sai dai bansan ta yadda zan fara mgrn ba🤔
Shiru yayi yana nazari sannan ya juya ya kalli Samha daketa juyi akan gado yace”
Yaya ne?
Ni bani da lafiya😫
Meke damun ki??
Nima bansani ba”
Bakisan inda ke miki ciwo ba??
Sakkowa tayi ta iso gareshi zama tayi cinyanta tare da fadin”
Allah Banda lafiya kamarr jikina kemin ciwo kamar kuma zazzabi kadai taba jikina kaji zafin”
Hannunsa yasa yasa ya taba wuyanta sannan yace”
Ni banji zafi ba, bawani zazzabi ajikin ki”
Toh nidai bani da lafiya”
Shikenan jeki kwanta inje gidan Baba indawo sai muje Asibiti tare”
Zan bika?
Keda baki da lafiya??
Naji sauki muje Dan Allah
Toh jeki shirya”
Binta yayi da kallo yana murmushi daman yafison tafiya da ita zaifi Jin kwarin yin mgn da Khadija idan Samha tana gurin”
Cikin damuwa take sosai Dan haka koda suka dau hanya hankalin sa yana wajen tunanin tare da addu’a Allah yasa Khadija tamasa abun dazaije nema gareta domin itace damar shi ta karshe……….
One comment