Advertisements

BUGUN ZUCIYA PAGE 2

BUGUN ZUCIYA PAGE 2

Posted by

BUGUN ZUCIYA PAGE 2

BUGUN ZUCIYA

Advertisements

(Heartbeat)

Fadeela Lamido*

 

Advertisements

4 to 6

 

Bakaramin firgita ma’u tayi ba lokacin da taga duna ya bude hannun shi ya cabe dutsen, cikin sauri ta sunkuyar da kanta dan gudun kar ya hangota”

Advertisements

Shiru taji dan haka ta sake lekawa, baccinshi taga yaci gaba kamar ma bashi aka jefa ba, tintserewa ma’u tayi da dariya tare da fadin ashema magagi yake, katon banza baccin rana harda magagi, dariya ta kara sannan ta sake daukan wani ta jefa mishi”

Wannan karon ahancin shi ya sauka amman ko motsawa beyi ba”

Bakaramin dariya ma’u ke kwasa ba saida tayi me isarta sannan tace kash馃槵 ina ma na taho da waya dana mai photo nakaiwa su zee suga mutumin da sukejin tsoron sa ashema nauyin bacci gare sa harda su magagi”

Wani dutsen ta sake dagawa, jin kiran sallah yasata zabura ta yarda dutse ta fito cikin takun kasaita ta wuce deeni tana kwambare kafada”

Sai karfe 1:15 ma’u ta shiga gida, da fada mamata taryeta tana fadin”

Asma’u wanne irin kunne gareki dazun2 nan abban Ki yace kidaina biyawa gidan dada amman dayake kunnen ki na kashi ne saida kikaje ko?

Muryanta dauke da shagwaba tace, mama nifa bacan naje ba, tun dazun fah muna makaranta baba idi ne yasamu sharan masallaci”

Fuskan mama dauke da rashin yadda tace sharan masallaci? Tsohowa bansan karya inace maza keyi?

Tun yaushe aka daina basu, ai basu iyaba duk ranan da maxa sukayi baya sharuwa muko namu yayi kyau sosai malamai nata samana albarkan Allah ya bamu miji nagari”

‘Da da mahaifi sai Allah, nan danan mama ta saki murmushi tana ameen tsohowa Allah ya mike albarka”

Cikin kunya tace amin sannan ta nufi dakinta”

Kai tsaye toilet ta shige, wanka tayi sannan ta fito rike da kayan da ta cire tana kwalah kira goggo tani2

Da saurinta ta shigo dakin tare da fadin Asmau lfy kuwa?

Kayan ta mika mata tana fadin lfy lau goggo kayan mkrnt na zaki wanke min”

Toh kuma gashi yanzun bani nake wanki ba, bala ne keyi amman bari nakai masa”

Yar karamar riga ta saka tare da siket daidai guiwar ta, fitowa tayi tana tafe tana raira karatun al Qur’ani, afalo ta samu mama, cak ta tsaya lokacin da ta hango kayan makarantar ta agefen mama”

Agogo ta daga kai ta kalla 2:10pm cikin fushi tace mama kinga goggo tani nabata kayan…..

Dakatar da ita mama tayi da fadin nina hanata takaiwa bala kayan, goggon sa’arki ce ita dazaki dinga kwala mata kira kina danga daki, saikace sabowar mejego?

Shiru tayi tana cigaba da zonburo baki”

Mama taci gaba da cewa toh maza ki dauki kayanki kije ki wanke dan goggo tunda tayi ciwon hannu abban ki ya hanata wanki, bala ne keyi, kuma ma bandan rashin hankali irin naki ya zaki hado harda bra dinki kice wai akwaiwa bala, yanzun ke bazaki iya wankewa ba acikin toilet”

Mama nifa wlh abani duk wani aiki amman banda wanki” ni ban ma iya ba wlh”

Toh aiko zaki koya maza ki kwashe kayan ki kije ki wanke babu me wanke miki agidan nan”

Buga kafa ta fara akasa tare da kara kallon agogo cikin kuka tace”

Mama nifah inason ne naje mkrntn yamma Kuma gashi yanzun lokaci ya kure, kuma idan banje yau ba duka na za’yi gobe”

Karfe nawa kika shigo gidan nan?, ai suma malaman sunsan yau bazaku samu zuwa ba, tun da su suka saku aiki”

Juyawa kawai tayi ta koma daki, dan bata da bakin mgn, kan gadonta ta fada, murmushi ta sake lokacin da ta tuna baccin duna, tare da wassafa fuskanshi a idon ta, mutun ne kyakyawa sai dai yaya akayi ya saka kanshi adaba, gashi duk anji mishi ciwo ajiki, da alama ma bashi da karfi tunda yake bari na jimai ciwo, tsaki taja tare da fadin katon banza kana Yawo da wukake amman kana bacci atiti badole ayanyanke ka ba”

Washegari tun karfe 7:30 ta nufi mkrnt bata biyawa zainab ba dan tasan bazata barta tai abinda tayi niyya yadda ya kamata ba”

Tafe take cikin kayan mkrnt idan ka ganta gwanin ban sha’awa, ita ba dugowa ba ita ba gajera ba, fara ce tas, ga wani siririn hanci da bakin ta madaidai ci shekarunta basu wuce 16 zuwa 17 ba amman kirjinta cike yake kai kace wata cikkakiya budurwa ce”

Lokacin da ta isa kofar gidan da taga duna dubawa tayi ko ina babushi babu alamar sa, azuciyar ta taji babu dadi dan taso ace ta ganshi”

Kad’a kai tayi ta wuce mkrt har aka tashi bata cikin natsuwar ta, Allah2 take atashi tabi hanya”

Tana ganin akusan tashi ta tsiri rubutu, dan haka su rahama basu tsaya jiranta ba sukayi
tafiyan su”

Saida ta dainajin hayaniyan yan mkrntr sannan ta dauki littafinta ta fito”

Dakalin ta da ta ganshi akai jiya yauma yauma kwace yake agurin ya daura kafarsa daya kan daya, ya daura hula kan fuskar”

Babu kowa alayin dan unguwa ce ta masu hali kowa yana cikin gidan sa babu ruwan wani da wani, hakan ne yaba ma’u daman isa gaban duna cikin sanda”

Cikin siririyar muryanta ta rangada sallama taji shiru babu amsa dan haka ta gara matsawa daf dashi tare da tabbacin yauma baccin shi yayi nisa kaman jiya, ahankali ta daga hannuta ta dafa hular dake kanshi, jitayi be motsaba dan haka ta daga hular fuskan ta bai yana”

Idon shi rufe dan haka ma’u ta bude baki da hanci tana karemai kallo”

Deeni wankan tarwada ne dan baza akirashi baki ba yana da duguwar fuska tare da dogon hanci daidai gwargwado, sakko da idonta tayi kan kirjishi da tat bai su kai kaca kaca dashi, yatsa ta cija sannan tace afili, meyasa kake bacci atiti bayan kuma ka sani sarai nauyin baccin gare ka, koni danake mace zan iya kashe ka ma ba jimaka ciwo ba, kallo ta kara masa sannan ta saka hannu ajakar makaranta ta dau waya ta daukeshi hoto har guda biyar sannan ta kwashe da dariya tare da fadin kai gskiya ni jaruma ce, agogo cikin wayar ta duba sannan ta nufi gida cikin sauri”

Washegari ko ta nuna ma kawayen ta hotunan duna kaman yadda tayi niyya, mamaki ne ya kamasu tun daga ranan zee bata kara yadda ta jera da ma’u ba, dasu rahama take jerawa su jirata daga can gefe ta gama tsokanan duna tazo su tafi suna kyalkyalketa dariya”

Ahankali wannan dabi’a tazama jiki agun ma’u kullum idan aka tashi mkrnt saita sameshi agurin yana bacci, haka zata gama surutun ta akan duna ta wuce gida”

Haka har aka samu tsawon wata biyu ,wannan lokacin ma’u intaje gaban deeni bata sanda ko mgn ahankali dan tasan idan har yayi bacci idan kaso zaka iya daukan shi ka gudu”

Abu ya zaman ma ma’u jiki harta kai alhamis da juma’a da babu makaran ta tana shiga damuwa dan haka yau juma’a da wuri ta isa dakin abban ta”

Bayan ta gaida shi ta zauna daf dashi”

Kallonta yayi da murmushi akan fuskanshi yace mamana ya akayi? duk yadda akayi akwai abin da kike so”

Cikin shagwa ba tace abba na tuna Dada ne”

Dada tana nan lfy mamana kulum tana cewa nagaishe mata da takwararta, ba inagaya miki ba?

Eh abba amman ni inason ne naje naganta”

Shiru yayi zuwa can ya dago yana share zufa yace, to naji amman kibari nasamu lokaci zan kaiki da kaina”

Shiru tayi badan ranta yaso ba, tana fitowa ta fara matso hawaye, karo sukaci da mama zata shiga dakin, ganin ma’u cikin hawaye yasa tabita da kallo”

Alhaji yau kuma fada kukayi kaida maman taka?, naga ta fita tana share hawaye”

Au kuka takeyi? Allah sarki, wlh ina matukar jin dadin yadda Asmau take nuna soyayyarta ga dada, amman kash bazan iya barinta ta zauna acan ba, sabo da gudun kar abinda ya faru shekarun baya yasa ke faruwa, shi yasa bana son na nuna mata gida biyu, kuma nacewa dada ta dawo ta zauna tare damu tace a,a bazan iya bari Asmau ta dinga zirga zirga atiti ba yau tana gida gobe tana gidan dada, dan gudun haduwa da gurba tattun samari”

Mamace ta dago da kanta bayan ta gama sauraren shi ahankali tace alhaji Allah ne fah yake tsarewa, kuma ai be kamata ace anhanata zuwa gidan dada ba itama dadan ai bazataji dadi ba”

Mikewa yayi fuskan shi babu annuri yana kokarin fita yace kice mata idan shirye take ta fito na sauke ta”

Dagudu ma’u ta fito fuskanta cike da fara’a ta shiga motar ta zauna har suka isa bece mata komai ba”

Akofar gidan ya sauketa sannan yace ki jirani idan nata so zanzo na dauke ki, ranta be soba, amsawa tayi ta shige gidan”

Bakaramin dadi dada tajiba dataga ma’u, aikace2 gidan sukayi tare sannan suka zauna suna hira, suna cikin haka dada ta fara gyangyadi, ma’u naganin haka ta kalli agogo 11:15 tagani, zama tayi har taga 11:20 dan haka ta mike ta dauki bakin gyalenta agefen gadon dada sadaf2 ta fice”

Da sauri take ta fiya dan taje ta dawo kafin dada ta tashi, tun daga nesa ta gane baya nan, dan gurin da yake kwanciya babu komai awajen, ja tayi ta tsaya domin taso ace ta ganshi”

Gajiya tayi da tsayowa dan haka ta juya ta fara tafiya da nufin komawa gida, kaman ance ta juya ta hango shi kwace, kai yaya akayi haka? Ma’u ta tambayi zuciyarta, juyawa tayi cikin sauri ta isa gurin tare da sallama, jin babu amsa ya tabbatar mata da bacci ya wuce dashi daf dashi taje ta cire hular dake fuskanshi, idonshi rufe yake kamar kulum, fuskanta takai saitin tashi sannan ta huramai iska ahankali”

Wani gwaron ajiyan zuciya ya Saki, da sauri ma,u taja baya”

Ganin yaci gaba da baccin yasa ta sake matsawa ta bude baki ta sake hura mai fuska akaro na biyu, karaf taji anrike ahannunta”

Subuhanallah yau nashiga uku na lalace, wayyo abba na waiyo dadata kuzo ku ceceni, dan Allah kayi hakuri

wlh takalmi nane ya tsinke na tsuguna zan dauka bansan akwai mutum agurin ba

 

 

 

Heartbeat
Mmn Yazeed

9 comments

  1. Pingback: Herbalife member
  2. Pingback: coupons
  3. Pingback: pg168
  4. Pingback: 1win apk
  5. Pingback: 1win

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *