Advertisements
💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
Story
&
Written
Fadeela Lamido
MmnYazeed📝
Advertisements
22-24
Akan wani dalili kika mare shi ?
ciki sanyi murya ummi tace alhj mun shirya zamu fita da safna har nashiga mota amman jalal yasa hannun shi yarike safna wai bazata shiga ba dan ya raina ni.
Jalal ya bude baki yace ai shigar da tayi ne be kamata ta fita dashi ba.
Advertisements
Cikin fada ummi tace kasan shigan da tayi be dace bane kai kasa hannun ka ka taba ta, ko muharramar kace ita.
shiru yayi ya juyar da kansa gefe
alhj yace to ya isa ke zaliha daga yau karki kara dukan jalal, inbanda ma abinki ya za,ai ki mareshi gaban safna, kanwar sace fah.
haushi ya bani alhj.
to shikenan kisan yanzun me zai faru, daga yau kar safna ta kara fita gidan nan inhar ba makaranta zata ba, ya juya yace jalal magana ta kare ko ?
shiru jalal yayi alhj ya sake cewa ko akwai saura ne halal
eh daddy, da sauri ummi ta harareshi dan haka yayi shiru.
sai da alhj yasake cewa ina jinka abduljalal meye kuma?
daddy kuma fa har samari zuwa gurin safna suke kuma ai karatu take.
alhaji dariya yayi yace abduljalal kai duk matsalan ka agurin safna take, toh jalal kodai son safna kake ne?
sai da ya kalli ummi san nan yace a,a.
itama ummi kallon sa take.
alhj yace ya hausan a,a jalal karfa kai kwauron baki wani yama kafa ya sake yin dariya, san nan yace ke zaliha kina fah shige mana hanci, kuma daga yau kar safna ta kara fita wajen wani.
haba alhj wai me yasa kakeyin haka jalal ne zai rinka juyamu agidan nan duk abinda ya fada kawai sai ka yan ke hukunci.
murmushi yayi yace naga kamar yana son ya fiki hankali ne, be jira me ummi zata ceba ya fita adakin itama bayansa tabi.
************
suna fita yaji zuciyar sa tamai fes tare da mamakin ya akai daddy ya dago shi ai lokaci beyi ba, ba yan zun ya kamata su sani ba sai ya samu soyayar safna neman zazzabin yayi ya rasa.
washe gari ana kiran sallan subahi ummi ta nufi dakin jalal yana kwance yana bacci ummi ta fara tashin shi yaro tashi kayi sallah, tashi yayi ya zauna, ummi tace yajiki ko asibiti zamu, da saurin sa yace naji sauki ummi nama warke.
bayan ya dawo daga masallaci be koma barci ba kamar yadda yake yi ada sai ya fara shirye shiyen fita kananan kaya ya saka yayi kyau matuka ya fito falo ya zauna babu kowa afalon ya nan zaune safna ta fito da gudu bata san cewa da mutun afalon ba taci karo da kafar jalal har ta fadin kasa kara ta sake dan taji zafi sosai.
da sauri jalal yamike yazo gaban ta ya tsuguna yace
sorry safna kawo na duba miki.
cikin kuka tace bana so bakai bane kasamin kafa, badu baki yayi cikin mamki yace yazanyi nasa miki kafa bake kika fito da gudu ba, be jira me zata ceba ya kama kafar ya matsa, fashewa tayi da kuka sai da su ummi da alhj suka fito suna fadin lfy.
ganin jalal sukayi rike da kafar safna itoko kuka take cikin daga murya ummi tace me ya faru?
Jalal yace faduwa tayi ina tunani kamar buguwa tayi .
ummi tace alhj wai wannan ne kake cewa yana da hankali ji inda ya ke taba ta .
mikewa yayi yana fadin ummi wani irin magana kikeyi, safna tashi muje asibiti
ummi bata so jalal yakai safna asibiti ba, domin bata son sultan yagan su tare dan suyi da hajiya baturiya yau zasu turo mata makudan kudi, tayiwa safna sayayya duk da cewa hajiya baturiya tasan halin danta ba aure ne agaban saba, amman duk yarinyar da ya nuna yana so sai taita kashe kudi dan ta faran ta mai rai.
Jalal kuwa tundaga ranar ya kasa ya tsare safna bata fita ko ina dan ummi na tsoron mijinta kwarai.
jalal ko jan safna yake ajiki sosai harta fara sakin jiki dashi kullum daddare zai aika kairat takira safna suyi ta hira suna dariya.
ummi na kwance adakin ta taji sai dariyar jalal da safna take ji ta daga kai ta kalli agogo 11:38 gaban ta ya fadi karfa ace jallal soyayya yake da yarinyar nan wani bangare na zuciyar ta nacewa ai kwanakin baya baban sa ya tambaye shi yace a,a to amma kuma wannan wani irin sabon salon ne, koma dai menene bazata taba bari jalal ya aure safna ba, yarinyar da sultan yayi soyayya da ita kilama yanzun tana dauke da cuta da wannan tunani ta zabura, tana fadi baza ta sabu ba
cikin sauri ta fito jalal naganin ta yace ummi bakiyi bacci ba.
eh banyi ba, tashi ka wuce daki tun daga ranar ummi ta hana safna fitowa hira jalal na zuwa falo saidai yaga ummi har tsawo sati daya besa safna a idon saba hankalin jalal ya tashi, itama safna kewan jalal take sosai.
washe gari da safe jalal ya fito cikin shirin shi na tafiya office bayan ya gaida ummi yamike ya nufe dakin safna, ummi ta kirashi ya dawo ina kuma zaka, inace office zaka tafi?
eh fita zanyi amman ina son naga safna kafin na fita.
Me zaka mata?
ummi na dade bansa ta a idona na ba fah ,ganinta kawai zanyi na wuce
wai yaro ni zaka munafunta karka mance kamin alkawarin bazaka aure safna ba inma ka fara tunanin aure ne sai kaje gida yayata ka auri yarta aliya dan tun tana karamar ta take sonka.
toh ummi naji munyi waya da daddy yace yau zai dawo inya dawo sai muyi maganar
adawo lfy, jalal yasake cewa ummi naje naganta kona minti biyu ne?
Kiri kiri ummi ta hana haka ya tafi jiki babu kwari
yamma likis jalal ya nufu gida yana shiga falon yaje jikin alhaji ya kwanta ummi bata gurin sai safna da kairat dan alhaji fira yake sosai da su safna ta juya takalli jalal taga yayi dare dare jikin daddy ta kwashe da dariya tace daddy kace ya daina hawa maka jiki karya karya ka.
daddy ma dariya yayi yace safna ai ke bakiga komi ba sai in beda lafiya zakiga har kuka yakeyi.
Kairat da safna sukara saka dariya.
jalal yatashi ya zauna yakali safna yaga sai dariya take yace ke ya isheki, daddy kaga zakasa suraina ni.
suna cikin haka ummi ta fito tana fadin ai jalal ya girma ne besan ya girma ba dazun nace mai yaje gurin aliya su daidai ta.
alhj yace wacce aliya yar wajan Rabi?
eh ita kuwa ashe baka manta suba.
au yanzun kuma kintuna dasu, inace zuwan su gidan nan nawa kina musu korar kare, to waima bari na tambaye ki, kisan inda su baffa suke yanzun,
ummi mikewa tayi zata bar wajan, alhaji yace dan dakata zaliha na samar wa jalal yarinyar da zai aura safna ma na mata miji.
Jalal zabura yayi yamike ya rike kafan daddy yace daddy karka min haka dan Allah
4 comments