Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 9

MIJIN MARAINIYA PAGE 9

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 9

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝

 

Advertisements

28-34

Dagowa yayi da sauri ya kalli daddy yaga daddy ko ajikin shi, abincin shi ma yaci gaba daci, ya mayar da kanshi kasa,
cikin murna ummi tace jalal kayi kuskure da kasani ka fada da wuri gashi yan zun kama kan ka.
ummi lokaci fa be kure ba sai dai in kun zabi wani akaina, ya miki zai fita alhaji yace kashirya anjima kaje kaga yarinyar, bece komi ba ya fata adakin.

yana fita alhaji yayi dariya yace zaliha kifara tanadi dan baza,a sa da yawa ba, cikin murna zaliha tace ai alhaji shiri zanyi sosai yara biyu fah, jalal yana barin dakin daddyn sa, dakin safna ya shiga ya same ta zaune tayi kuka idonta duk sun kunbura, tana ganin shi ta durkusar dakai, jalal yaje daf da ita ya zauna safna kuka kikayi har idon ki suka kunbura haka , me yake damunki ko kema baki son auren ne?
shiru tayi ta kasa magana bazata iya gayawa jalal cewa shitake soba itama kanta tana ganin lefin zuciyar ta datake son wadda yafi karfinta, jalal ne ya katseta safna nifah bazan bari amin auren dole ba, safana zan tambaye ki amman ina son kimin alkawarin zaki gaya min gaskiya tsakanin ki da Allah .

Advertisements

me zai hana yaya jalal indai na sani zan fadama ka.
safna tsakani da Allah babu wani da kika taba jin kina son ki aura.
hawaye ne suka gangaro mata dan bata zaci wannan tambayar ba ,tace akwai.
jalal yace waye wannan safna?
yaya jalal mubar wannan maganar ai kai ma baka fadamin yarinyar da kake so ba.
Safna ni bani da budurwa saidai ko zakimin hanyar kawar ki sai na aura. tace to aigashin nan daddy yasamar maka.
shi ko jalal so yake yayiwa safna wayau yaji ra,ayinta kuma ya rasa tayaya zai fara kuma yana tsuron karya fada tace bata sonshi, dago kan shi yayi ya kalli safna yace,
ni bana so ta gurin daddy ta gurinki nake so.
wai kai yaya dan Allah da gaske babu wacce kake so?
jalal yace gaskiya akwai safna amman tsoron gayamata nakeji kartace bata sona.
safna mantawa tayi dawa take magana tace , kai👉🏻 yaya jalal wacece zata kalleka tace bata so.
cikin dauki yace da gaske safna,saboda me kikace haka.
yaya wlh babu wacce zata ce bata soka komai kyanta komai kudin gidan su sai dai kawai inbata samu ba, kai baka san ka hadu ba ne, wlh yaya kai kyakyawa ne kana da kyau sosai.
dadi sosai jalal yaji ya kashe murya yace toh safna ko zaki taimaka ne ki aure ni.
Sai alokacin safna tatuna tayi subutar baki ciki tashin hankali ta mike zata fita tana fadin mezaka ci dani?
da sauri jalal yamike ya rike safna yace karki kara cewa haka safna, na dade Ina sonki Ina tunani karkice baki so nane shiyasa ban gaya miki ba,
fashewa tayi da kuka tace me zakayi Dani rorarriya mara dangi bani da kowa fah jalal , kaikuwa dan gata ne ummi da daddy suna matukar sonka.
tausayin safna yakama jalal besan lokacin da yasata akirjishi ba itama lafewa tayi kamar karama yarinya yace safna kema suna sonki, nima kuma Ina matukar sonki dan haka karki kara cewa baki da kowa, mune dangin ki.
a,a yaya ummi bazata bari ka aure ni ba.
a hankali yace safna karki kara kiran sunan ummi akan wannan maganar ba runwan ki ,nidai kawai abinda nake so dake , idan daddy ya tambaye ki kice ni kike so , kinji?

suna cikin haka sukaji anturo kofar miryar ummi sukaji tace jalal.
zabura sukayi da sauri yasake ta.
ummi tace zoka wuce daddyn ka nakira, jalal wucewa yayi yana sosa kai yabar ummi adakin.

***********

safna bakin gadon tabi ta zauna, ummi ta harare ta, tace yar iska kawai zata koyawa yaro iskanci, in Allah ya yarda saikin bar gidan nan, baza kizo ki lalata mana yaro ba.

bayan kwana biyu hakalin jalal ya kara tashi dan yaga sai shirye shirye ake agidan ya sake koma wa wajan alhaji ya kara gayamai shifa babu wacce yake so sai safna
alhaji yace wai dama da gaske kake ne, aina dauka wasa kakeyi, to kabari zanyi shawara.
ran jalal beso haka ba amman yasan abinda zaiyi yace daddy yau gidan hajiya zani.
alhji yace ya kamata jalal inkaje ka gaida ta, yace tare da safna zantafi, kafin alhj yace wani abu ummi ta shigo Ina zaka da safnan kuma?
gidan hajiya zamu.
alhaji karma barshi ya tafi da ita ban yadda da jalal ba ,ya canza hali.
alhj yace wani irin magana ne wan kuma.
wlh alhaji rannan ganin jalal nayi rungume da safna kaga kuma be kamata suna fita waje tare ba.
alhaji ya kalli jalal, yace abduljalal haka ne?
shiro yayi ya dukar da Kai, alhji yace tashi ka bani waje. jalal yaso ya leka gurin su safna amman ya fasa ya wuce gidan hajiya.

hajiya mahaifiyar alhaji ce kakar jalal tana matukar son jalal dan duk cikin jikokinta shi kadai ne namiji sauran duk matane kuma kanana ne yayanta guda uku ne mahaifin abdul jalal shine babba sai kaninsa wadan yanzun ne ya samu haihuwa yarssa mace kusan garman su daya da kairat sai kanwar su mace anty nusaiba bata dade dayin aure ba tun lokacin da alhaji ya kawo zaliha amatsayin wacce zai aura, hajiya ta nuna batayi na am ba, amman daga baya taga ya matsa ta hakura akayi.
bayan ummi ta haifi jalal suka gane bata son mutane duk wanda yaje gidañ saita mai wula kanci, dan haka suka hakura da zuwa gidan.

jalal ya shiga gidan hajiya tun abakin falo yake fadin matassss.
ah,ah dan duniya saiyau ka tuna damu

daidai lokacin jalal ya shiga falo yaje kusa da ita ya zauna, yace wlh hajiya kina raina abubuwa ne suka min yawa, shiyasa baki ganni ba.
kai dai kace mahaifiyar ka ta hanaka zuwa koda yake harda laifin baban ka aishi kullum yana zuwa ai sai ya tasoka gaba, amman ku kuka sani, nidai kujera ce.
jalal yace hajiya kiyi hakuri ni bawan da ya hanani zuwa, ni yanzun ma akwai abinda ya kawoni.
toh ina jinka me ya kawo ka.
ya kwashe duk abinda yake faruwa ya gayawa hajiya.
dariya tayi tace jalal ai ina da lbrn komi baban ka yagaya min komai tsokanan ka yake amman har an tsai da ranar biki sati uku masu zuwa , karka kara tada hankalin ka , me yasa baka taho da safna ba, ko baka son naga kishiya ta.
hajiya wai dan Allah da gaske kike yi?
jalal na taba irin wannan wasan ne dakai?
hajiya bari naje gobe zan dawo
yana shiga gida yasamu alhaji afalo alhji yayi dariya yace jalal kadawo daga kai karar tawa ne?
jalal ya sosa kai yace ba haka bane daddy ni gai sheta naje .
jalal kana nufin ban san halin da kake ciki bane, nagane kana son safna tun ranar da naga kishinta karara a idon ka, amman sai kamin karya kace basan ta kake ba, kuma nama haka ne dan kar ka ga kasa meta asauki nan gaba kace zaka wulanta ta jalal safna itama mutun ce kamar kowa duk son da nake maka inhar ka wulakanta ta , zamu raba hanya dakai

kuma daga yau na haramta ma shiga dakin safna, inzaku yi hira kuyi afalo , suna cikin haka ummi ta fito , alhaji yace kafin kizauna kiramin safna.
ummi ta shiga ta kama kunnen safna ta rike sannan tace idan alhj ya tambaye ki kina son jalal kice a,a, idon safna cike da kwalla tace toh ummi.
suna zuwa safna ta zauna akasa, ummi ko tunkan ta fito tawashe fuska,
alhj ya kalli safna yayi murmushi yace yace safna ki fara shiri bikin ku nan da sati uku masu zuwa na zaba miki yayan ki jalal.
zufane ya fara karyo ma ummi tace alhj ita baka tambaye ta ko tana sonshi ba.
a,a basai na tambaye taba nasan ma tana sonshi ai dama tare muka gansu.
Jalal ya kalli safna yayi murmushi, itako safna kanta na kasa banda far gaba ba abin da yake damun ta.
alhj yace jalal naga kamar bakinka akwai magana?
daddy ranar ne naga kamar yayi yawa ko za ,a dan rage ne
ummi mikewa tayi ta buga tsaki tashige daki, tashiga tunani gakiya nayi kuskure dahar na bari wata alaka tashiga tsakin sultan da safna gashi aure yana neman shiga tsakanin ta da dana kuma zaiyi wuya ace sultan bashi da H.I .V

6 comments

  1. Pingback: fuck girldice
  2. Pingback: special offers
  3. Pingback: Blub

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *