Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 11

MIJIN MARAINIYA PAGE 11

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 11

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

 

Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed

Advertisements

41-45

Anty nusaiba na tsefe wa safna kai tana tunanin ga yarinya me kyau amma gwanin ban tau sayi, bayan ta gama tsefe mata kai taji muryar jalal suna gaisawa da mutane afalo dan haka ta kwala mai kira, ya amsa ya mike ya nufi dakin safna ummi ce ta dakatar dashi yadawo tace ba alhaji ya hanaka shiga dakin safna ba?
eh amman yanzun bakiji anty na kira na bane.
rasa abin cewa tayi dan haka jalal ya juya ya shiga dakin lokacin da jalal ya shigo dakin safna tana bayi tana wanka.
Jalal yace dama ke kadai ce adakin?
anty tace nida safna ne yanzun ta shiga wanka, kai kuma haka ake yi baza ka ba amarya kudin lalleba ko haka kake son akai maka ita.
toh ni anty babu wadda yace na bada kudin lalle agidan nan nifah da daddy kawai muke shirye shiyen mu agidan nan kinga mu bamu san yadda akeyi ba, anty kinsa ma wani abu kuwa rabon da naga safna na man ta in na,aika kairat ta kirata sai tace ta cemin tayi bacci, ko kiranta nayi awaya bata dauka, ni ina tunanin ma babu wanda ta gaiyata katin ma dana aiki kairat takai mata dawo min dashi tayi wai bata da wanda zata bawa, dan haka na barta .

MIJIN MARAINIYA PAGE 11

Advertisements

anty nusaiba ta nisa tace ai irin wannan da sai ka gayawa ummin ka ta mata fada.
wace ummi, ai ummi bason auren nan take ba, ni ina tunanin kamar ma itace take firgita, ta haka sukai ta tattanawa tsakani su, anty nusaiba tace wai safna har yanzun baki gama wanka bane?
safna dake tsaye abayi duk firan da suke tana jinsu tace nagama anty, namanta ne ban shigo da hajjab ba. anty tace au haka ne cikin dariya tace jalal tashi ka fita inta gama shirya wa sai kadawo.

jalal yace a,a anty ta fito kawai ni babu ruwana da ita ba kallonta zanyi ba.
anty tayi tayi jalal ya fita yaki fita, tashi da kanta ta dauko hijjab kato ta mikawa safna, tasa sannan ta fito kanta akasa dan yanzun wani irin kunyar jalal takeji, tashige cen longu ta zauna ta fara shafa mai, acikin hijjab take shafawa jalal Nata kallon ta, cen yace bazaki gaishe ni bane, kafin ya rufe baki tace ina wuni, shiru yayi sai cen yace bazan amsa ba, saida naroka, safna tace ina fa shirin gaisheka kayi magana.

toh nidai bazan amsa gaisuwa daga nesa ba, saikin matso kusa dani.
safna tana kokarin ajiye man shafawa tace inazuwa bari nasa kaya.
a,a kizo ahaka.

anty tana gefe ta jin su tace ke dauki kayanki kishiga bayi ki saka, wai dama jalal ashe baka da kunya haka, agaba na .
jalal yace to menayi kuma daga nace ta matso kusa dani.
safna bata saurari me suke cewaba tashiga bayi tasaka kaya dogowar riga tasaka na atamfa tayi kyau duk da bawani kwalliya tayi sosai ba, ta dora karami hijjab akai sannan ta fito, gurin jalal ta nufa tace ina wuni, mamayan ta yayi ya rike hunnuwan ta, yace tsorona kikeji kuma.
tsugunawa tayi tana boye fuskar ta cikin cinyoyinta shiko jalal yana rike da hannuwan ta yana kokarin daka kanta, ciki ciki suke sosai safna da jalal waishi dole sai yaga fuskarta itakuma taki bari ,
safna taga jalal yafi karfinta dan haka ta fara kiran anty kin ganshi ko?

anty dake gefe tana kallon ikon Allah tace wlh jalal zan bata maka rai, ko kunyata bakaji nazama babba banza kenan .

dasauri ya sake ta yana fadin na bari Anty na mance ne, ya mike yace bari naje anty , yaza ayi maganar kunshin ?

karka damu yanzun zankai ta amman inaga acen zan barta ta kwana dan naga bawani gyara da aka mata.

jalal yaja ya tsaya anty kuma harda kwana toh abar kunshin mana ai badole bane

MIJIN MARAINIYA PAGE 11

 

kallon jalal tayi tace ai yan zon baka da ikon hanata fita saika bari sai an daura auran.

**********

haka anty nusaiba tadauki safna ta kaita gidan kawar ta hajiya asata me ygara amare, hajiya asata tana ta yiwa anty ko rafin me yasa ba,akawo ta da wuriba sai ana jibi biki.

bayan anty ta dawo gida tasamu alhaji awaje ranshi abace saboda ummi ta kitsa mashi magan ganu iri iri.
tun daga nesa alhaji ya farawa anty nusaiba fada, nusaiba ina kukaje har dare yayi haka?
wlh yaya nakai safna kunshi ne.
shine kuka kai dare haka, to yanzun ina safna.

yaya tana cen sai gobe zan koma nadauko ta.
alhaji ya fara fada ta inda yake shiga battanan yake fita ba.
lokacin da nusaiba ta shiga ciki ta samo ummi da kawayen ta sai shewa suke suna ganin nusaiba suka fara yadda habaici.
Madina ta kalli dayar dake kusa da ita to amara kirjin biki komai shishige wanki dai, dan nan namu ne, kuma duk inda akaje dole adawo

5 comments

  1. Pingback: cinema rule
  2. Pingback: Infographics

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *