Advertisements
ABU MAI MUHIMMANCI AKAN WAYOYINMU DA MUTUM ZAI CIKE DON TSERATAR DA KANSA IDAN YA YI HATSARI (ACCIDENT):
Yawanci wayoyinmu na android muna saka musu password ta yadda idan mutum ya yi hatsari za’a rasa yadda za’a kira yan’uwansa, ko kuma idan wayar ta fadi ta shiga hannun mutumin kirki dole sai ya jira an kirashi, amma babu halin ya kira na kusada mai wayar don sanar da shi.
Haka mutane ma ya kamata su san wannan saboda idan suka tsinci waya kai tsaye za su iya kiran yan’uwan mai wayar, haka idan sukaga hatsari suna iya daukar wayar mutum su shiga wadannan guraren don taimakonsa.
Advertisements
To ga hanya mai sauki da za ka cike wasu muhimman abubuwa akanka ko da wayarka na cikin password za’a iya shiga wadannan bayanan naka kamar yadda na nuna guraren a hoto;
1. Idan ka shiga gurin da za ka saka password ko pattern na wayarka, a kasa za ka ga inda aka rubuta #Emergency kamar yadda na nuna gurin a arrow a hoto na 1. Sai ka danna kansa.
2. Zai kai ga gurinda aka rubuta #Emergency_information a sama, kamar yadda arrow ya nuna gurin. Sai ka danna kai sau 2.
Advertisements
3. Zai kai ka gurin da har yanzu aka rubuta Emergency information din, amma a gefensa na dama akwai inda aka nuna wani alama (icon) na kamar bairo ✏️ sai ka danna gurin. Kamar yadda na nuna gurin a arrow.
4. Daga nan zai kai ka gurinda aka rubuta #Edit_information da kuma #Add_contact. Wannan gurin sun rabu kashi biyu;
a. Na farko shi Edit information din zai baka damar ka cike bayanai akanta kamar sunanka, inda ka ke zaune, garinka da sauransu. Kamar yadda za mu gani a gaba.
b. Shi kuma add contact din zai baka damar ka saka lambar wayoyin wasu daga cikin yan’uwanka wadanda za’a iya nemansu in case of emergency, kana iya saka sunaye da yawa, kuma ka tabbatar ka rubuta lambar wayoyin wadanda idan aka nemesu za’a samesu.
5. Idan ka shiga Edit information kuma zai baka damar ka rubuta wadannan abubuwan;
a. (Name). Sunanka
b. (Address). Gurinda ka ke zaune, gidanka ko wajen sana’arka da garin da kake.
c. (Blood group). jininka. Domin wani lokaci idan aka yi hatsari zai iya kaiwa ga bukatar jini idan an kai mutum asibiti, kai tsaye za’a san jininka wane iri ne. Za ka gansu a jere, sai ka zabi naka.
d. (Allergies). Shi kuma idan akwai abinda idan ya sameka yana iya jawo maka wata matsala, kana iya rubuta shi a gurin. Kamar misali wani idan ya ga jini hankalinsa na tashi misali. Irin wadannan matsalolin.
e. (Medications). Shi kuma idan akwai wani magani da kake kansa wanda likita ya doraka akai, kana iya rubutawa saboda kar ka yi hatsari a samu matsala domin akwai cutar da wani magani ke iya tayar da ita.
f. (Organ donor). Shi kuwa zai tambayeka ne ko kana iya bayar da kodar ka ko kuwa a’a. Yes or no ne a wajen.
g. (Medical notes). Shi kuwa bayani za ka rubuta akanka gameda lafiyarka ko akasin haka.
Idan mutum ya cike wadannan bayanan akanshi, lokacin da kaddara ta jawo mutum ya fada wani hatsari musamman a garin da ba nasu ba, za’a iya amfani da su idan an kai shi asibiti, sannan jami’an tsaro na iya amfani da shi don neman yan’uwansa kai tsaye ba tareda an bude wayarsa ba ko da tanada password. Haka idan wayar ta fadi kuma ta shiga hannun mutumin kirki, zai iya tuntubar lambobin da ka rubuta ya kirasu.
Allah Ya sa mu dace Ya karemu daga mummunan kaddara.
Daga; Abu Albani Auwal Ahmad
4 comments