Advertisements

BA KOWANNE NAMIJI BANE KE SON FARAR MACE.

BA KOWANNE NAMIJI BANE KE SON FARAR MACE.

Advertisements

 

 

Shafe-Shafen da mata suke yi yana daya daga cikin musabbabin mutuwar aure a arewacin Nigeria, amma fahimta nane wannan!

Advertisements

Mata da yawa bance duka ba sun dauka cewa duk wani na miji farar mace yake yake so, to sam ba haka bane! Wani tunda Allah ya halicce shi be taba jin son farar mace a zuciyar sa ba.

Maza sun kasu kashi-kashi ne ni a fahimta na.

Tabbas haqiqa akwai mazan da suke son farar mace, sannan akwai mazan da suke son bakar mace.

Advertisements

Ashe kenan don Allah ya yi ki baka ba shine yake nuna cewa ko wanne namiji fara yakeso ba.

Sannan don Allah ya yiki baqa baya nuna cewa duk Maza basa son baqar mace har ta kaiga ki sauya halittar da Allah ya miki sabo da gajeren tunanin ki na cewa maza sunfi son farare sam ba haka bane, wasu ne daga cikin mazan suke son fararen Mata, wasu Mazan Baqaqen mata suke so.

Misali Idan Mata sun dauka cewa duk wani na miji Farar mace yake so shine dalilin su na yin Bleach, to mu qaddara haka ne cewa Maza farar Mace suke so.

A lokacinda mai son farar mace ya hadu da wacce asalinta Baqa ce amma yanzu tayi Bleaching ta zama fara sai suka fara soyayya har takai ga sunyi aure, da yake yau da gobe be bar komai ba, sai fuskarta da jikin ta ya fara kodewa tunda farin nata ba natural bane, dama saye take yi da kudin ta, daga nan mijin zai fara jin ta fara fita masa daga ranshi sai kaga daga dan abu qarami sai ya kaiga saki, ko kuma ya nemo wacce dama ita fara ce a halittar ta ba Bleaching take yi ba ya aura daga nan wani na mijin ya fara yi mata wulaqancin da sai ta gwammaci bata taba yin aure ba.

Kuma ba zata taba gane dalilin da yake jawo mata wulaqancin ba har abada duk wata kyautatawar da zata masa ba zata taba burge shi ba, to ina amfanin Shafe-Shafen kenan?

Baqaqen Mata su tsaya a matsayin da Allah ya ajiye su, Akwai mazan da baqaqen mata suke so ba farare ba, idan kika canja Halittar da Allah ya miki don ki auri na mijin da yake son farar mace da tunanin kema yanzu fara ce, to yau da gobe asirinki zai tonu, zaki fara kodewa tunda dama ya aureki ne don ke fara ce, to farin ya fara qarewa kin fara kodewa, soyayya itama sai ta fara qarewa kenan.

Idan maza sun kai goma ka tambaye su zaka sha mamaki kowa da ra’ayinsa dangane da matar da yake fatan samu ya aura.

Kuma abinda yake bani mamaki da wasu mazan da suke son farar mace da yawa yawan su suna ganewa tun kafin ayi aure cewa wacce suke shirin aura asalinta ba fara bace ba baqa bace, tunda akwai alamun da ake ganewa masu yawa.

Warin jin kanshi man da suke shafawa.

Bambancin da yake tsakanin hannuwansu da fuskokin su.

Quraje na musamman dalilin shafa man.

Duk wata gaɓa misali ‘yan yatsu na hannu da qafa ko wacce gaɓa yana nan a matsayinsa yadda Allah ya halicceta baya canzawa. .

Shawara ga maza duk wanda yasan cewa ra’ayinsa shine auren farar mace to ya duba waicece ainihin ta farace ba shafe-shafe tayi ba ya aura, gudun kar sai daga baya anyi aure kaji ta fita maka a zuciyar ka, saboda ta fara kodewa sakamakon shafe-shafe har ta kaiga an sami rabuwa, Allah ya kiyayee Ameen.

Shawarana zuwa ga ‘yanmata baqaqe ku tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ku kuma inayi muku Al-bishir da cewa akwai maza masu tarin yawan daku suke so, ku suke buqatan aura ba farare ba!

Don haka yadda fararen mata suke da maza masu sonsu kuma kuna da maza masu son ku zama uwayen ‘ya’yan su idan Allah ya yarda kuma soyayya ta tsakani da mahaliccin ku.

@Fadila Lamido

 

Leave a Comment