Advertisements
BA LABARI BOOK 2
BY
Fadila Lamido
Page 38
A’a
Advertisements
Wasan zamu fara duk abun da na miki ken ma ki min.
Jimmm, tayi Zuwa can tace toh.
Hannun sa ya fara kaiwa jikinta Yana taba ta sannan ya dauke hannun nasa Yana fadin kema ki min.
Advertisements
Ni bazan iya ba.
Zaki iya kiyi min kamar yadda nai miki.
Hannun ta ta mika kadan ta dan gogi jikin jikin sa saidai ta gaza yi kamar yadda yace, daga karshema kuka tasa sabo da yadda yake ta nanata mata cewa tayi fa alkawari.
Rarrashinta ya shiga yi bayan da ya tabbatar baxata iya ba, shikuwa ya riga ya daukantu dan haka ya shiga sarrafata, ahankali yake bida ita har ya samu nutsuwa, bayan ya dauki tsayon lokaci Yana Abu daya.
Albarka yaci gaba da sa mata tare da ringuman ta sosai.
Misalin karfe bakwai da rabi da nafe Suraj ne ya Kira Modibo adaidai lokacin da yake kokarin shiryawa domin xuwa aiki.
Daukan wayar yayi yasa a kunnen sa tare da sallama, shiru Unaisa taji yayi tsayon lokaci sannan yace gani nan zuwa zan biyo ta gidan.
Zuwa can ya sauke wayar sannan ya kalli Unaisa tare da fadin, matso ki taimaka min.
Mikewa tayi ta isa gaban shi ta Kama buturin rigarsa wadda ta kula shi yake sakawa a lokacin ta karasa sawa tana sawa ne ya sanar mata Yadikko bata da lafiya.
Nan danan jikin Unaisa yayi sanyi bayan ta gama gefe ta koma ta zauna cikin yanayi na me tunani.
Bayan ya gama yace toh nina fita saina dawo.
Inzo muje gidan Yaddikon
a’a kije kiyi mene, tafiya ya fara yana fadin saina dawo.
Allah ya tsare, ta fada, ta tare suka fita falo yayin da ya nufi part din Safna bayan wani lokaci ya fito cikin yanayin dake nuna sauri yake ya fara kokarin fita, mikewa tayi cikin kokarin yi Masa rakiya kokarin fita take yai saurin fadin Ina zuwa haka?
Cikin kawar dakai tace rakiya nake maka.
A’a, nan ma ya isa Madam koma ciki.
Komawa tayi cikin sanyin jiki badan karta Zama me korafi ba da tace wani abu.
Komawa tayi ta fara gyara part din shi sannnan ta rufe ta koma nata tana me sauke ajiyan zuciya, Allah ya sani Bata son wannan zuwa part din nasa dan dai babu yadda zata yi ne.
Yau Madobo har biyar tayi be dawo ba, dan haka ta fara tunanin ko lafiya, haka taita tunani sai misalin 6 sannan taji alamar shigowan motar sa, cikin sauri ta tashi ta laka ganin shine ta saki ajiyan zuciya, part din Ammi ya nufa da haka ta koma ta zauna.
Tana Zama taji Kiran sa, dauka tayi saidai tunkafin tace komai yace na dawo Ina dakin Ammi.
Inzo?
Me zaki yi?
Zan gaida ita ne sannan kuma nagaji da Zama ni kadai.
Uhum lallai, ke din?
Eh Mana, inzo din?
A’a, kijira ni yanzun zanzo.
Toh kawai tace, sanan ta sauke wayar.
Jiran sa taitayi har akayi isha’i be shigo ba hakan yasata tunanin ko lafiya,
Sai misalin 9 ya shigo, cikin sanyin jiki sosai, Zama yayi tare da sauke ajiyan zuciya tare da fadin, Kimjini shiru ko?, wlh na dauki Ammi ne munje gidan Yaddiko bata da lafiya.
Me ke damun ta?
Jikin ta ne ya tashi sosai.
Subuhanallahi Unaisa ta fad’a tana kallon Modibo.
Nakai Ammi can zata kwana gurin ta.
Jikin sosai ne kenan?
Lumshe Ido yayi ya bude sannan yace, eh toh amman da sauki yanzun.
Shiru ya sake yi alamar nazari zuwa can yace, Suraj ya samu yariyar da zai aura nan da sati biyu za’as yi bikin.
Bazawara ce?
A’a budurwa dai ko.
Yamutsa Baki Unaisa tayi sannan ta kawar dakai tare da tunanin ko auren nasa ne ya tada ciwo Yadikko.
Yau abincin kadan Modibo yaci da alama ma turawa yake yi yayin da tunani ke yawan daukan shi.
Bayan sun kwanta ma jawota yayi kawai ya rungume ajikin shi tare da sauke ajiyan zuciya.
Zuwa can Bacci ya dauke ta gane hakan da Modibo yayi yasa shi tashi zaune tare da rungume hannun sa a kirji cikin yanayin na me tunani
Unaisa kuwa Bacci tayi sosai sai gurin karfe Uku ta farka waigawa tayi ta ganshi zaune dan haka tace, Wai menene?
Muryan ta kawai yaji batare da yasan ta tashi ba, dan haka yai saurin yin Murmushi tare da fadin, “Babu, na tashi inyi Sallah ne, Yana gama fadin haka ya mike ya shiga toilet, alwala ya dauro sannan yazo ya tada sallah.
Da Asuba ma Yana kokarin tafiya masallaci wayar sa tayi Kara, dauka yayin cikin sauri Yana fadin, Yaya ?
Shiru yayi tsayon lokaci sannan yace, ka Kira Magaji da Muftahu zan same ku acan, sauke wayar yayi tare da kallon ta sannan ya juya ya fita, bayan ya dawo ma cikin sauri ya shirya ya fita, Yana fita ta Kira Ammi bayan sun gaisa ta mata yame jiki.
Alhamdulillahi tace, nan take sanar mata gasu ma a hanya zasu je asibiti, addu’a Unaisa tayi sannan ta sauke wayar jikin ta a sanyaye.
Yauma har dare bataji dawowan sa ba duk da cewa dai ba agurinta take ba amman sosai ta kagu ya dawo kodan ta tambayi jikin Yaddiko.
Ganin har anyi managari shiru yasa tai tunanin Kiran shi, daukan wayar tayi sannan Kiran sa, sai dai harta kusa yankewa ba’a dauki wayar ba, lakacin data cire rai da tsammani taji muryan mace cikin kunnen ta tace, ” Wake mgn?
Cikin tsananin mamaki Unaisa ke sauraron muryan Safna cikin wayar Modibo, dama tare suka fita ne koko binsa tayi daga baya, da alama ma ni d’aya ce a gidan, domin Ammi ma bata Nan, Abba ko yana riga kowa fita sannan tasan Magaji ma baya na.
Muryan Safna taji ta sake cewa wa ke mgn?
Acikin ranta take tambayan kanta ita kuma wannan tana son ta nuna min babu no dina ne awayar Modibo, tsintan kanta tayi da fadin, ” ki bawa me waya wayar shi.
Cike da kissa tace, ” Ai shine nake son inji ko wacece dan insanar masa no ce kawai ba suna.
Ai number da ba’a haddace ba ita ake ajiyewa, idan yana kusa ki karanta masa number zai gane.
Cikin Sauri Safna ta kashe wayar domin ta rasa amsan da zata bawa Unaisa.
Itako Unaisa Saida ta sauke wayar sannan taji wani haushi ya kamata wadda takejin inama ta gaggayawa Safna mgn, bacin raine sosai ya sameta wadda har yasata ta rasa inda zata yi, yadda takejin daci azuciyarta yasa ta mikewa gyale ta dauko ta yafa tare da daukan karamar jakarta ta fito ta rufe part d’in ta.
Part din Ammi ta nufa nan ma rufe yadda ta kulla duk cikin gidan babu kowa daga ita sai ma’aikata waigawa tayi ta kalli girman gidan, katon gaske bangare bangare, akwai alamun akwai ma part din da babu kowa aciki, juyawa tayi ta fara takawa tana dosan Babban gate din gidan.
Tundaga nesa taji Muryan driver Yana fadin, ” Hajiya intaso ne?
Batare da ta juyo ba tace a’a ba nisa zanyi ba.
Ficewa take kokarin yi daga gidan yayin da megadin yace, Hajiya ba asibiti Zaki ba?, Ibarahim ya kaiki mana?
Tsayawa tayi yayin da megadin ya Kira driver cikin sauri ya dauko motar, tsayawa yayi daidai kusa da ita tashiga sannan suka fice a gidan.
Saidai kuma ita akasan ranta Bata san Ina zata ba, dan haka bayan sunyi nisa a tafiya taja tsaki tare da tambayan kanta, toh Ina ma zani ne?, gurin wa Zani? hawaye ta share sannan tace bazani ma asibitin ba, tunda Yana tare da matar sa, wata zuciyar ce ta sake ce mata ai besan zakizo ba, bada izinin shi Kika fito ba, ki koma gida kawai, inkoma gida bacin am maidani banza duk wadda suke da mahimcin an tafi dasu, ni ambarni a gida tun sabe ko waya babu, sannan kuma ashema ko number ta be aje ba, sabo tsabar wula kanci.
Hawaye ta sake sharewa sannan tacewa driver sauke ni anan.
Nan kuma, inace Asibiti zamu?
A’a nan ma yayi ta fada adaidai lokacin daya faka motar.
Sauka tayi da sauri sannan ta tare adaidai ta ta shiga.
Binta da kallo driver yayi aransa yake tunanin anya kuwa lafiya.
Bayan ta zauma hawaye taita sharewa, yau daya a rayuwarta ta taba yin bakin cikin rashin dangi da karancin gata da Bata dashi, ganin baccin rai ya dameta ta rasa in da zata saka kanta taji dadi, Innaworo taita tunuwa a kasan ranta dan haka hawayen ta ya kara karuwa kamar an bude famfu.
Ganin sumyi tafiya me yawa yasashi tambayan ta Ina muka nufa ne Hajiya.
Sunan Unguwar Su Afnan ce ta fara fado mata arai dan haka kawai ta fada mishi sunan Unguwar.
Wata zuciyar ce tace mata me kuma zai kaiki gidan su Afnan, yayin da wata zuciyar ke fadin in banje ba Ina zani, kukanta ne ya karo dan haka taita share hawaye.
******
Modibo ne shida Safna akan hanyar su ta komawa gida tace, ” Dazon an kira ka da wata number, barin karonto maka kaji.
A’a karki karanto idan mun isa gida sainabi kiran.
Waida zan Kira ne inga koka rike number.
A’a karki kira, computer ce ni?, ko number Ammi da Abba da suke kaina suna na nan ajiye cikin wayar.
Murmushi tayi tare da kawar da kanta gefe, lallai tana son ta Kira numbar dan haka ta sake fadin kamar nasan Number nan wlh, karantowa ta fara yi tun bakai ga fadan number dake karshen ba yai saurin waigowa yana fadin 8?
Eh, ta bashi amsa tana me Masa kallon kurullah.
Unaisss, ya fada yana kokarin amsan wayar tare da fadin, amman Yaya akai haka.
Mike mishi wayar tayi yayin da ya gangara gefen hanyan.
Kira ya kiga yi har sau 4 ba’a dagaba dan haka ya koma kan titi.
****
Me gadin ne ya bude matar kofar ta shiga, tsayawa tayi ta share hawaye tasss sannan ta doshi kofar da take zaton nanne kofar falon Unaisa.
Bata taba shiga gidan ba Amman tasan gidan ta wajen sa.
Tsayawa tayi ta kwankwasa zuwa can Afnan ta taho ta bude kofar, ganin Unaisa ce tai saurin rungumar ta.
Saidai tun kallo d’aya da tai mata ta gane da damuwa a daddare da ita.
Falon suka shiga suka zauna, yayin da Afnan ta dubeta cike da mamaki tace, Lafiya kuwa?, nayi mamaki da Hamma Modibo ya barki Kikaxo nan, d’azon muje Asibiti lokacin Sai Aunty Safna kadai harna tambaye ki yace kina gida.
Tana kaiwa Aya ta dago ta kallo Unaisa yayin da taga tana share hawaye Dan haka a firgice tace menene?
2 comments