Advertisements
BA LABARI BOOK 2
BY
FADEELA LAMIDO
PAGE 39
Cikin sauri Unaisa tasa hannun ta ta share hawaye sannan tace, ” babu komai”
Advertisements
Kallo Afnan ta bita dashi sannan tace, waye ya kawo ki Hamma Modibo ne?
Bashi bane.
Ke dawa to?
Advertisements
Cikin kawar dakai tace ni ‘yarki ce da zaki tsareni da tambaya ni kadai nazo.
Kallonta Afnan tayi sosai sannan tace, ” Amman yanayin ki ya nuna kina cikin damuwa?
A’a ba haka bane kawai nazo ne idan kuma baki so in tashi in tafi.
Allah ya baki hakuri, mikewa Afnan tayi tana kokarin shiga kitchen Unaisa tace, ” ni karki kawo min komai bazan ci ba.
Ai kodai ruwa kyasha ko?
Bazasha ba.
Dawowa Afnan tayi ta zauna cikin ranta tashiga sake sake.
Zuwa can Unaisa ta Kara share fuska sannan tace, ” Ina Kabir?
Be dad’e da fita ba Abban su ya Kira shi.
Waigawa Unaisa tayi ta kalli gidan sannan ta kalli Afnan da tai kyau tai kiba da haske tace, ” Dan Allah dubi yadda kikai kyau kikai haske, kina cikin gidan ki cikin kwanciyar hankali keda dan mijin ki, kai wlh gara mutum ya samu dan yaro ya aura ba mijin wata ba.
Ni gaskiya Aunty Rahma ki daina irin wannan abun, bana jin dadin sa, Hamma Modibo ma yaro ne ba tsaho bane, kuma idan hakane ai gara ma mutun ya auri wadda yake da cikakken hankali, yaran nan tana iya yiyuwa auren marmari ne da an kwana biyu a gundura da juna, amman wlh Hamma Modibo yasan abun da yake yi.
Afnan baza ki gane ba, sabo da bake bace aciki halin da nake Ciki bakisan me nakeji ba, kedai kawai ki gode ma Allah.
Nidai Aunty Rahma gaskiya bana son kina irin wannan mgnr, idan kina haka sai indinga ganin kamar baki son Hamma Modibo ne….
Ni bance miki ban son shi ba Afnan, kuma shima nasan yana sona.
Toh me zai dame ki?
Matar shi, ni da gaskiya vanson kishiya bazan boye miki ba Afnan, tunda na tare Nakejin tsanar ta.
Ai daman can haka kike, har Ammi ma ta taba fada tace kinfi Aunty Safna kishi kuma shima Hamma Modibo ya sani.
Ni da can ba kishi bane yanzun dai nasan inajin haushin ta wlh banson kishiya ko kadan.
himm’um lallai, kina da aiki kuwa Wlh, garama ki rage shi Ina wad’an da suke auren me mata Uku zasuje ata hudu, sai wannan Safna ita daya tal zata daga miki hankali?
Nima zan iya Zama dame mata hudun ai amman wani mijin ba wannan ba.
Ware Ido Afnan tayi a kanta sannan tace, toh indai haka ne bakaramin son Hamma Modibo kike yi ba, shiyasa kishin ki akan shi yake da girma, kuma wlh shima Hamma Modibo yafi son ki akan Aunty Safna, tuni nagane haka, Yana sonki sosai Allah.
Bawani nan, cewa yayi Wai kowa da gefen da yake azuciyar shi, sannan shidai gashi nan ne dai baka gane inda yasa gaba, sai kiga yaita jia ita, yana yaba abincin ta alhalin babu wani dadi sai magin da take dankarawa, indai wanan abincin ne dadi to wlh besan ma me ake Kira dadi ba, sannan kuma ranar da nayi nawa nakai mishi sai yace, wai yau zaici jagwalgwalon na, wlh abun nan bakaramin Kona min rai yayi ba.
Dariya Afnan tayi sosai harda hawaye sannan tace banda Abun Hamma na kaida ka kwashi dad’i har ka bada kyautar mota jiki na rawa ai abin cin ma ko jagwalgwalon ne haka zai tsuke bakin shi ya lamushe kodan kar a hana Masa da dare.
Yadda Afnan ke dariya har yasa Unaisa murmusawa tare da fadin, kefa Yar isa ce Hamman naki kike ma shakiyanci.
Dariya Afnan ta sake yi tana fadin wlh abunan Mamaki yake bani yanzun shi Hamma Modibo kawai sai ya biyoki Yana ‘yar murya?
A’a ni bemin ‘yar murya ba, Unaisa ta fad’a tare da kara kawar da kanta can gefe.
Toh Wai yanzun Ina Kika baro Hamma ?
Nima bansan inda yake ba, tun safe ya dauki matar shi ya fita, amman ni rakiya ma yace a’a, sannan kuma kinsan ma wani Abu daya Kona min rai?
Saikin fad’a.
Nan ta gaya mata yadda sukayi da Safna bayan tayi shiru Afnan tace karkiga laifin shi, wata kilama besan ta dauki wayar ba, kuma ni ban yadda ace Wai be aje number ki ba, wannan ma ai karya ne, dama tayi ne dan baki haushin, toh yanzun me yasa zaki fita bada izinin mijin ki ba, Hamma fa Yana da fushi sosai wlh ki tashi ki koma tunkan ya dawo ranshi ya baci.
Ni kadai fa aka Bari acikin gidan nasan ko karfe nawa zasu dawo?, tunda yasan ya fita da matar shi kuma gurin ta yake ba lallai ma ya dawo dakina ba, nigaba daya ma nagaji da wannan rayuwar nifa dandai shine kawai amman da bazan auri me mata ba.
Tsananin Tausayi Rahma ta fara bawa Afnan, dumin ta fahimci kishi ne kawai yake dawai niya da Rahma dan haka tace, ” yanzun dai ki tashi ki koma gida, dare yayi gaskiya, ki dinga bawa zuciyar ki hakuri kofa sati biyu baki yi ba agidan haba mana Aunty mu, yanzun in yaje gida be ganki ba hankalin shi zai tashi, kafin yaji dadililin fitowar taki kuma ransa zai baci, Kona kirashi na gaya mishi kina nan?
A’a kibarshi, kidai ce kawai na fitan miki agida, Daman nasan banda wani gata shima shiyasa yake min haka, ganin tana kokarin mikewa Afnan tace a’a zauna nifa shawara nake baki, kiyi zaman ki anan din kawai.
*****
Ammi Rahma ta shigo Nan ne?
A’a muda muka shigo tare kun ma rigamu shigowa gidan ai.
Toh dawo na duba ne Bata nan, kuma nata kiran wayarta bata dagawa.
Kunyi da ita zata wani wajen ne??
a’a
Toh ko Asibintin taje?
Nakira Suraj yace bata je ba.
Ikon Allah toh ko can gidan su Suraj din taje ne Nan ne dai wajen zuwan ta, Ina zuwa barin Kira can gidan inji.
Bayan ya sauke wayar mikewa yayi ya
nufi dakin shi, rigar sanyi ya dauka ya sanya tare da daura hularta akansa sannan ya dauko bakin gilashi ya sanya.
Falon sa ya fito inda ya samu, Safna zaune ganin sa haka yasa ta fadin, ” lafiya? naganka cikin Shirin fita.
Eh wlh, sanyi nakeji, kuma na duba Rahma Bata cikin gidan nan barin je gurin Ammi kocan tayi.
Toh, ai Ammi mun rigasu shigowa saidai ko taje asibitin mukuma mun taho.
Duk tana iya yiyuwa, amman dai barin inje ingani.
Ficewa yayi yayin da zuciyar Safna tai fari kall, afili tace zakici ubanki yau agun sa, Baki San mutumin nan bane shiyasa Zaki fita da auren sa akanki batare da izinin shi ba, dariya tayi sosai sannan ta dauki waya ta kira Momy.
Abun da yake faruwa ta gaya mata yayin da sukayi dariya gaba dayan.
Momy ce tace, ai na gaya miki kisa ranki a inuwa da sannu zamu gasata, idan dama taki ai sai a koma hagu, bari ki ganni indai Modibo ne yau saidai ta kwana a hanyar garin su.
Dariya suka saka gaba daya bayan sun sarara Momy tace, toh ke barin sa kikayi y ya tafi neman matar tasa shi kad’ai.
Toh ni Momy ai haushi ya bani, naso yai zaman shi harta dawo ne ayi komai gabana.
Banda abun ki Safna ai dole ya neme ta, tunda besan wani dalilin ya fitar da ita ba, amman Bari ya dawo ki gani. ko kuma kitashi kibishi can ki numa kema hankalin ki be kwanta ba.
amsawa tayi zuciyarta fal farin ciki.
***
Modibo ne da zaune cikin motar, yayin da Magaji da Muftahu suke cikin wata motar suna kokarin fita gidan Magaji ne ya taho da motar sa suna jerawa data Modibo yake fadin, Modibon tunda bakajin dadi daka zauna a gida.
Fuskarn shi babu walwala yace, ” bazan iya zama ba Magaji, me gadin ne ya taho yana gaida su, bayan Modibo ya amsa yace masa ko kaga fitan Rahma?
Eh ai da mangariba ta fita, zata asibiti, dan da ita kadai taso fita nina Kira mata Abdullahi.
Magaji ne ya kwalawa Abdullahin Kira bayan ya amsa ya taho.
Magaji ne yace Ina kakai Rahma dazon?
Eh asibiti zata toh bamu karasa asibitin ba tace na sauke ta.
Muftahu me yace a hanyan??
Eh bamu karasa ba tace ya isa.
Magajine yace, ” Haba Abdullahi meyasa zaka sauke ta a hanya?
Cikin tsayawa Modibo yace, “wayace mishi dai ya fita da ita?
Duk tsif sukayi suna kallon Modibo idon shi cikin bakin gilashi ya sake fadin, wanene ya baka izinin fita da ita?
Naga dai zata fita ne ranka ya dad’e….
Tasawa ya sake buga mishi tare da fadin, Mena gaya maka tun akan Safna?, laifin ka ne akan me zaka fitar min da mata.
Ahankali Magaji yace, toh ai Modibo shi bashi da laifi laifin ta…..
Kai! dallah rufamin Baki, Modibo ya bugawa Magaji tsawa bude motar yayi ya sauka tare da fadin, bazani nemanta ba Kaine zaka nemo ta, na baka minti dalatin ka dawo min da matata, juyawa yayi afusace ya nufi part din Ammi.
Magaji da Muftahu binsa da kallo sukayi bayan ya kule suka mayar da kallon su Kan Abdullah dake kuka sosai domin tunda yake a gidan Basu taba samun matsala da Modibo ba.
Magaji ne ya figi motar suka fice a gidan yayin da Abdullahi ma ya dauki mota ya biyo hanya.
5 comments