Advertisements
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 42
Daker ta iya karasawa gaban motar wadda ita kadai ake jira, ahankali ta bude bayan motar ta shiga ta zauna, d’an waigawa tayi ta kalli gefen da Safna take tace ina kwana?
Advertisements
Cikin sakin fuska sosai Safna tace lafiya lau tun daga lokacin ta dauke kanta can gefe.
Suraj ko gyaran murya yayi domin shirin amsa gaisuwar Unaisa, sai dai har aka dauki dogon lokaci beji ta gaidashi ba ko inda yake ma bata kalla ba.
Gajiya yayi da jiran tsammani dan haka ya ɗan waiwayo ya kalleta tare da faɗin, ” Madam ba gaisuwa?, ko baki lura dani bane ?
Advertisements
Batare da ta juyo ba tace eh.
Tasanin mamaki yaji dan haka yayi shiru tsayon lokaci zuwa can ya sake cewa, ” toh Madam ina kwana?
Yi tayi kamar bataji ba sabo da tsabar haushin sa da take ji, Muryan Modibo taji yana fadin ka rabu da ita yau kurmaye ne akan ta.
Dariya sukayi gaba daya, sannan Suraj yace ai saita amsa, waigowa yayi yace, ” ina kwana Rahma?”
lafiya lau, ta fada batare da ta waiwayo ba, dan haka ya kalli Safna yace Safna me kuma mata ne?, da alama akwai abun da kuka mata.
Murmushi tayi sannan ta kalli Modibo tare da fadin, ” saidai ko shi, duk yadda akayi shine ya bata mata rai, dan ni mun dad’e ma bamu hado ba.
Au Modibo baya had’e kanku kenan, ai ya kamata ka dinga hade kansu ko abinci su cishi kwano daya, kuma duk inda zasu su tafe tare, amman ace an dad’e ba a hado ba, ba kanta kenan.
Wani irin kallo Modibo yaiwa Suraj sannan yace, kayi a gidan ka ni banda ra’ayi.
Ai kuma wannan shine adalci Suraj ya fad’a yayin da Modibo yace kai karka dame ni.
Nisa sukayi a tafiya, Magaji da Modibo keta hira, yayin da yawancin hirsa ta kanka su ce, inda Suraj ke fadin,” yanzun in kaje me zakacewa likitan?
Me ko zance, kawai ce masa zanyi Baba ya turo mu shi ya fada masa da bakin sa.
Dariya Suraj yayi yana fadin, gaskiya ya cika rigima, Ni kuma ina ganin na Magaji ya kamata yasawa ido a kuma matsa masa yayi aure, sabo da Magaji ba guri daya yake zaune ba, ina gudun karya kwaso tsaraba.
Allah ya kyauta, Modibo ya fad’a yayin da suka shiga cikin asibitin.
Bayan ya faka mitar, babu wadda ya motsa har saida Modibo yace ku shiga ku samu guri ku zauna zan kira shi.
Amsawa sukayi, sannan suka bude motar suka fita yayin da hankalin Modibo yake kan Unaisa har suka shiga.
Batare da ya kalli Suraj ba yace masa, jiya Sumayya tayi bacci kuwa?
Wanni irin bacci?
Bacci dare mana.
Tayi bacci mana, me zai hanata bacci?
Mgnr auren ka mana.
Eh tana ta kunbure kunbure da korafin ko shekara batayi ba za’a mata kishiya, wai har na gama yayin ta, da sauran maganganu makamantan hakan, amman tayi baccin ta.
Juyowa Modibo yayi ya kalle sa, sannan yace, ” In baka shawara?
Eh inajin ka?
Ka lalla’bi matar ka ka kwantar mata da hankali, ka kuma dinga nuna mata auren nufin Allah ne, bakwai rashin so bane ko wani abu, ka jawota ajiki ka zama kaine abokin shawara ta, idan ba haka ba kuwa akwai matsala, indai baka fahimtar da ita ba hartaji ta gamsu toh zata fita waje tayi hira da wasu za kuma su bata shawara, wani ya bata mekyau, wani ya bata mara kyau, abun da nake son ka gane, kaga dai Sumayya da Rahma kansu ya had’o akwai alamun suna tattauna matala ne tare, ita kuma Rahma bata da sau’ki gurin kishi, bazata bata hakuri ba saidai ta zuga ta.
Dariya Suraj yayi har hawaye ya cika idon sa, sannan yace toh ko shiya yau taki gaidashi?
Haushi ka take ji ma gaba daya, daren jiya batayi bacci ba, inda kasan ita za’awa kishiya, saida na zare mata ido ta bani abinci, sannan akaje aka kwanta a gado aka juyo min baya, dan haka kaje ka lallami matar ka ka rike ta agida kartazo ta kunna min wuta acikin gida.
Akunna maka wuta ko a kunna min?
Ai kaika ballo rigimar kaje kaji da ita nina riga da na rufe kofa, daga waya Modibo yayi ya kira likitan yake sanar dashi isowar su, zuwa can ya sauke wayar sannan yace muje.
*****
Gaba dayan su zaune suke agaban likitan, rubutu yayi cikin wata takarda sannan ya kira wata ma aikaji ya bata tare da fadin ku bita.
Modibo ne yacewa Safna da Unaisa ku je yayin da likitan yace ai har da kai.
Karamin tsaki yaja, sannan ya bi bayan su, yayin da Suraj ya zauna agurin yanawa Modibo dariya.
Tsayon lokacin suka dauka kafin suka dawo, gurin likitan suka zauna, Modibo yaso su wuce amman likitan yace su d’anyi hakuri kadan.
Bayan kusan minti arba’in matar dazon ta dawo, hannun ta rike da takardu ta mikawa Likitan, yayin daya daura gilashi a idon sa sannan ya shiga dubawa.
Dagowa yayi ya kalli Modibo sannan yace Oga naka komai lafiya babu wata matsala.
Murmushi Modibo yayi sannan yace toh ka gaya mishi, lafiya lau nake, duk yabi yasa min ido.
Shima dariya yayi sannan yace ai yana da gaskiya, ajiye dakardan Modibo yayi a gefe sannan ya dauki wata yana dubawa, tsayon lokaci zuwa can ya d’ago yace, ” waccece Rahma?
Modibo ne ya nuna Unaisa yace gata nan.
Ajiye takardan likita yayi akan na Modibo, tare da fadin, ” me ni’kabi kenan?
Takarda ta karshe ya dauka sannan yace, Safna komai lafiya babu wata matsala.
Suraj ne yace ita wacce meyasa ka ajiye ta a gefe?
Likitan ne yace Na Rahma ba, ita Rahma tambaya zan mata, juyawa yayi ya kalli Rahma yace, ” yaushe rabon ki da al’ada?
Modibo ne ya kalleta yana jiran jin amsan da zata bada tare da yin nisa da tunanin sa shima.
Ahankali tace na dad’e
Zaikai wata nawa?
Shiru tayi tsayon lokaci dan haka Modibo yace, barin amsa maka,
Tayi sau daya ne tun bayan data tare.
Kabar yariya tai mgn da bakin ta, Suraj ya fada yana kallon Unaisai.
Toh idan ba haka bane ai saita fada, n Modibo yabawa Suraj amsa.
Murmushi likitan yayi, sannan yace, amman shine daga kai har ita baku yi tunanin kila an samu karuwa ba har wannan lokacin?
Wani irin Mummunan tashin hankali ne ya samu Safna jin wannan kalamin na likita.
Shiko Modibo cikin yanayin mamaki da rudewa yace, toh ai ni bansan yadda abun yake ba, takaici ma tunanin hakan bezo min ba kwata kwata me kake so kace?
Hannun sa ya mikawa Mudibo suka kama sannan ya shiga fadin ina taya ka murna, matarka nada ciki na tsayon wata Uku da sati biyu.
Runtse ido Modibo yayi tare da fadin, Masha Allah Alhamdulillah, ya juma be bud’e ido ba, hannun sa yasa cikin aljihu, idon sa arufe, duk abun dake cikin aljihun ya ciro yana mikawa likitan tare da bude idon sa yana fadin, ga tukuici.
Suraj ko hannu ya mikawa Modibo tare da fadin, wannan murna namu ne gaba daya, ko banza mu huta da rashin hakuri Baba.
Safna ko ban da yake babu abun da take, ganin haka Modibo yai saurin lalubo hannun ta ta cikin mayafin ta yake matsa hannun nata ahankali, itako Unaisa sunkuyar dakai kawai tayi, daman cikin bacin rai take, idon ta jawur, dan haka yanzun ma kwalla ya sake taruwa a idonta, wadda ta rasa ko na menene.
Muryan likitan taji yana fadin, babu wani abu ne dake damun ki, ina nufin bakya jin wasu ciwo ka haka ajikin ki?
A’a babu inda kemin ciwo.
Masha Allah, Juyawa yayi ya kalli Modibo tare da fadin, dan Allah akula da ita sosai zan baku wasu magunguna wadda wadda zata dinga sha.
Amsawa Modibo yayi cike da fara’a
Har suka mike Safna bata iya cewa komai ba banda fara’ar da take zubawa.
Cikin motar suka koma suka zauna Kamar yadda suka zo, Modibo ko har yanzun bakin shi yaki rufuwa yayin da yake wayan waigawa yana kallon Rahma data kawar ga kanta hankalin ta yana kan titi.
Shi kanshi Suraj cikin tsananin farin ciki yake, yayin da bakin shi ke cike da tarin maganganu, saidai ganin Safna agurin ya kasa furtawa, ya kula Modibo ma kokarin boye farin cikin sa yake saidai hakan yaki boyuwa.
Har suka iso gida Safna bata iya cewa kala ba, kusan atare suka sauka Motar Safna da Unaisa, kowacce part dinta ta nufa yayin da Modibo ya kira Rahma, bayan ta ta dawo yace ki wuce gurin Ammi gani nan zuwa.
Cikin sauri ta kama hanya tare dajin sanyi cikin ranta.
Bayanta Modibo yabi da kallo yana sauke wani irin Hajiya zuciya tare da fadin, Allah kaine abun godiya.
Gaskiya ne abokina dole ka godewa Allah, munta rawar kafa Ashe Wala Habaru matar Modibo ce.
Kashhh kabari, idan akwai abun da nafi tsana a duniya, toh wannan sunan ne, sam bana kaunar sunan, akwai wani shiri ma da nake da nufin yi na dakarta dashi ne kawai sabo da matsalar Yadikko, amman da mun gama naga Yadikko ta samu nutsuwa zan bijiro da zancen.
Wanne zance kenan?
Akan mgnr iyayen Rahma ne”
Ba Ace sun rasu bane?
Eh haka labarin yazo, amman ni ina ganin akwai lauje cikin nad’i, sai jikina yana bani wannan Innawuron ba ita bace ta haifeta, na taba ganin hoton ta adakin su, matar bakace sosai babu wani alama ko kusa da zakace itace ta haifeta.
Ai Modibo ba lallai bane sai sunyi kama, ana samun haka, kama be isa shaida ba.
Nasani, amman ni gaskiya ina ganin akwai Magana arufe.
Ita Rahma ta nuna maka haka ne?
A’a ita kullum tana ma iyayenta addu’a ga duk alama bata da shakku akan cewa su suka haifeta, amman ni ina dashi, kuma dalili ne me karbi da kowanni me hankali ya kamata ya duba.
Hmmm Modibo kenan, kaima dai kusan irin halin Mama gare ka, kun cika neman jaraba, bakwa hakuri da ƙaddara, ita yariya ta Amin ce kai kana nema abun mgn, haka ma Mama tabi ta kala rai ta kasa hauri da ƙaddara, wlh duk ranar da naga yaron nan ido da ido saina nannaushe shi sabo da irin bakar wahalar da ya bani, shi kilama yana can yana rayuwar shi be damu da ita ba amman ita tana neman kashe kanta.
Dariya Modibo yayi sannan yace, kajika wai wahalar da ya baka, sai kace kataba zuwa kai kadai.
Toh ai naga kai baka damu bane baka korafi.
Kurafin me zanyi tunda farin cikin ta nake nima
Irin mgnr da sukaita tattaunawa kenan har suka dauki tsayon lokaci sannan Suraj ya wuce, Modibo ko part din Ammi ya wuce cikin zallar farin ciki.
Sallama yayi yana dauke ta farin ciki, itama Ammi ta farin ciki ta amsa tana kallon kwayar idon Modibo take fadin, tunda naga kana murmushi komai lafiya kenan?
Ammi Alhamdulillah ya fad’a sannan ya nemi guri ya zauna
Itama zama tayi tana kara kallon fuskan Modibon tana murmushi.
Shima murmushi yake tare da cire hularsa ya aje agefe.
Modibo ya naga bakin naka yaki rufuwa?
Kansa yai saurin sha’awa tare da mikewa yana fadin inazuwa Ammi.
Bayan sa tabi da kallo sannan ta juya ta kalli Unaisa.
Da sauri Unaisa ta kawar da kanta dan haka Ammi tace, “a’a ikon Allah, kallonta ta maida gurin Modibo dake shirin fita tace zonan Modibo.
Cikin sauri ya dawo.
Menene yake faru?
Zama yayi yayin yana tunanin ta ina zai fara karo na biyu kenan rayuwar shi da irin haka ya faruwa dashi, can kasa, yace” Ammi ashe mun samu karuwa ne mu bamu sani ba.
Juyawa tayi ta kalli Unaisa tare da fadin, Alhamdulillahi, amman wannan shiriritar tnasan sai Rahma ko?
Itace Ammi.
Masha Allah, toh shine har kake kasa fad’i, kai Alhamdulillahi tun yaushe?
Kallon Unaisa Modibo yayi yace ke ana mgn.
Cikin sauri ta kara kawar da kanta adai dai lokaci Ammi tace Ni kai na tambaya ba ita ba.
Wata Uku da sati biyu, Modibo ya fada yana sosa kansa.
Baki Ammi ta rike tare da fadin, yau ga mashiririta, niko fa naka yi tunanin hakan amman saunai shiru sabo da Safna ma abaya nata mata irin wannan kallo, Wannan ai abun farin ciki ne, toh Safna fa badaita da wata matsala ko?
Ance komai lafiya Ammi bata da wata matsala.
Alhamdulillah, itama Allah ya bata, yau mai martaba hankalin sa zai kwanta.
Modibo ne ya mike tare da fadin, Ammi zan dan leka gurin aiki, gata nan jiya batai bacci ba, idan kin kalli idonta zakiga a kunbure suke wai tana taya Sumayya kishi.
Kaji kuma wata shiriritar ba, juyawa yayi ta kalli Unaisa tare da jawota jikin ta ta rungume.
Shikuwa Modibo harya zauna amita wani tunani ya fado masa tare da tausayin Safna tabass yasan zataji wani iri dan haka ya sauka amotar domin yasan halin da take ciki kuma ya nuna mata komai na Allah ne.
****
Cikin matsanancin kuka take fadin, Momy kizo zan mutu, bakin ciki zai kasheni bazan iya zama ba, kawai kizo Momy idan kika wuce gobe sai dai kizo ki tarar da gawa ta, kullum kice indaure kullum kice indaure gashinan abu sai dad’a lalacewa yake yi…..
4 comments