Advertisements

Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 44

Posted by

BA LABARI BOOK

 

Advertisements

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 44

Kamar bazai dauka ba har sai da ta kusa katsewa sannan ya zaunar da Unaisa shima ya zauna tare da daga wayan, bayan sun gaisa tace, ” Modibo dan Allah kai hakuri Safna kwata kwata batasan inda ke mata ciwo ba, bata da hankali  sam.

Advertisements

  Jimmm yayi sannan yace bakomai  Mama.

   Dan Allah ka kara hakuri da ita…..

  Adai yi mata fada Mama, dan abun da take yi ya wuce na hankali.

Advertisements

   Na mata Faɗa Modibo, banda rashin hankali ai komai na Allah ne, banga abun tada hankali ba, amma ita tun safe tabi ta tada hankalin ta.

   Shikenan Mama ya wuce bakomai.

  Toh Nagode Modibo Allah yai mako albarka.

   Ameen nagode,ya fada tare da sauke wayar  ya ajiye ta a gefe.

  Juyawa yayi ya kalli Unaisa data kwanta yayi murmushi tare da fadin kin gaji ko?

     Kaita daga alamar eh, tare da fadin bacci nake ji can kasa kasa.

      Bacci ko?, toh ki gyara kwanciyar ki idan baccin yazo sai kiyi abin ki, amman kin ko kira Dada kin mata albishir?

     Name?

    Cikin sauri ya daura hannun sa akan maranta tare rankofowa kanta yana fadin, “na wannan ƙaruwar da muka samu.

       Kawar da kanta tayi tare da fadin, a’a ai bazan iya ba.

    Kallo yabita dashi tare da fadin, ” ya kamata ki iya mana, hannun sa yasa ya juyo da kanta gefen shi tare da fadin, dan Allah ki daina jin kunyata haka mana Unaisss, ya isa haka mana, har sai yaushe zaki daina jin kunya ta.

     Ni ba kunya ka nake ji ba.

  Toh wannan kawar da kan yaya sunan shi, tun a asibiti nake kallon fuskan ki babu wani canji dake nuna kinyi farin ciki da samun cikin ki, nikuma lallai ina son in gani, inason inga farin cikin ki, kinga ni tunda naji wannan labarin bakina yaki rufuwa, har bana sanin me nake yi, sabo da tsabar farin cikin  nayi sadaka dana fita, sannan kuma gobe zan tashi da azumi.

    Cikin sauri ta tura kanta a kirjin sa tare da fadin nayi fa, nima goben zanyi azumin…

    A’a baza kiyi ba, kina son ki ballo mana ciwo ka ne?

    Ni lafiya ta lau, zan iya yi.

   Guda nawa zaki yi?

   Kai guda nawa zaka yi??

    Uku zanyi.

  Nima haka.

Dariya yayi tare da kara rungume kanta akirjin sa yana fadin, ” kina gasa dani ne?, ko kina son ki nuna min ban fiki barin cikin bane ?

    Kanta ta daga alamar eh, har yanzun tana kwance a kirjin shi.

   Dariya yayi har yana bada sauti mai karfi yayin da Unaisa ta lumshe ido batare data shirya ba, sosai sautin ya sata nishaɗi.

  Shima Modibo kara rungume ta yayi sannan ya sumbaceta tare da faɗin, karya ne wannan Unaisss, baki kaini ba,  shekara fin shida da aure ko bari ba’a taba yi ba acikin gidana, kwatsam yau naji wannan dandaɗa labarin, har fa wasu na cewa acikin Ni da Safna daya baya haihuwa, sai gashi Allah ya nuna masu ikon shi, yanzun idan Allah ya tashe mu lafiya zan kira Mama in baki ki gaya mata.

    Ni A’a, kai ka gaya mata mana, baka kwace min ita ba, kullum kuna waya kuma kana zuwa amman ko labari baka bani barema kaje sani.

     Ajiyan zuciya yayi sannan yace, nima ba haka nan nake zuwa ba, akwai abun da yake kaini, In gaya miki wani abu?

     Eh

  Wannan gidan naki dakike kunshe kanki ke kaɗai nasa an gyara shi an bada haya.

Cikin sauri ta d’ago daga jikin shi tana kallon cikin idon shi tace, kayan Innawuro fah?

     Suna gidan Mama, akan su nake son nai miki mgnr yanzun kin amince a badasu sadaka?

   Ni A’a

  Toh me zakiyi dasu Rahma?, kinfa biye rigima ke fa, kaya ne irin na tsofi ko nan zakizo dasu ne?

   A’a ni dai abarmin kayana ina so.

     Shikenan naji, toh kimin kudin su in biya.

     Aini Ina son kayan ne sabo da Innawuro.

    Rahma banson irin haka, bana tunanin akwai wani abu da zai miki amfani agidan nan idan kuma akwai toh ki bari nan gama zan kaiki ki dauka sauran ayi sadaka dasu, da ana aje kayan duk wanni wadda aka rasa da kowanni gidama tsohon kaya zaki gani dan ba kanki farau ba,

      Sunkuyar dakai tayi domin babu yadda zatayi dashi.

   Kanta na kasa taji yace, Mama ta tashi a wannan Unguwar fa.

    Ina ta koma ?

    Sun saya sabon gida harma sun tare.

   Jimmm tayi, zuwa can hawaye suka fara zobo mata.

   Hannun sa yasa ya jawota jikin shi yana fadin menene haka?

    Cikin kukan tace, ” nasan kaine ka saya masu gidan, duk ka canza min rayuwata  har wani lokacin inajin kamar bani bace.

  jiya zuciya ya yi tare da sunbatan ta sannan yace, ” Ina son ki da yawane Unaisss, sosai nake son ki har inaji acikin zuciyata Ina son ki fiye da yadda nake son kaina.

    Tsintan kanta tayi tasa hannu ta rungume shi can kasa kasa take fadin, Ni kaine komai nawa idan baka babu ni, har inajin ma meyasa ni ban fara haduwa dakai ba.

     Murmushi yayi sannan ya ɗan kwallon ta yana shafa kanta yake faɗin, ” Ƙaddara mu ce ahaka.

      Ahankali tace Hamma?

    Shiru yayi tare da lumshe ido.

  Ahankali yaji ta sake cewa Hamma?

   wannan karon ma shiru yayi har saida ta sake cewa Hamma Modibo kayi bacci ne?

   Idona biyu, ina jin ki me kike son kice?

       Kwanciyarta ta gyara ajikin shi sannan tace, nifa bana son kishiya wlh.

    Aina sani Rahma, amman ya zamu yi wannan ƙaddara mu ce.

    Lumshe ido tayi sannan ta sake cewa yawwa Amma In tambaye ka?

    Ina jinki Unaisss.

   Nida Safna wa kafi so  ?

Dif tajisa ko motsi beba zuwa can ta sake cewa, Hamma?

   na’am

Kayi shiru?

Mema kika ce?

Cewa nayi nida Aunty Safna wa kafi so?

Ina son ku gaba daya Unaisss.

   A’a ni ba haka zakace ba.

Toh me kike son ince?

  Wadda kafi so zaka kira sunan ta.

  Gyara kwanciyar shi yayi ya mike sosai a gadon, sannan ya rungumota yana sunsunar jikin ta yake fadin, Unaisss Safna.

    Suna daya zaka kira fa.

    Shiru taji shi dan haka tace, Hamma ?

    Wannan karon ma be amsa ba har saida ta kara cewa, ” Hamma Modibo?”

   Cikin yanayi irin na me bacci yace,’ bacci yake yi fah.

    Dan dariya tayi sannan tace, “Allah kanaji na toh wa kafi so, Ni?

    Ummm

  Aunty Safna ?

Ummm

Hamma ni?, ko Aunty Safna?

  Ummm, ya sake cewa yana kara mannewa ajikin shi.

Hannun ta tasa ta ture shi daga jikin ta tare da juya mishi baya tana fadin, shikenan.

  Kwanciya yayi ta bayan ta ya sunbaceta tare da fadin, banson irin wannan tambayan Rahma, domin amsata babban kuskure ne da namijin kanyi wajen haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin  matasan sa, ku mata da anyi mgn da ku kun iya gori sai kun gorantawa junan ku, shiyasa maza suke gwara kanku, abun da suka fada anan shi suke maimaitawa acan, kowacce tanajin ita sarki ce, sai ranar da gaskiya ta fito fili sai kuma kuce namiji muna fuki ne.

      Ni ka gaya min ba wadda zan gaya mawa.

   Shikenan barin nuna miki irin son da nake miki, hannun shi ya fara turawa jikin ta yana shafa wa tare da sauke numshi.

   Bata hanashi ba dan tasan bazai yi abun da ranta keso ba ɗin, dan zuwa yanxun ta fara hahimtan halin sa.

   A Hankali ya shiga rabata da kayan cikin ta sannan ya shiga sarrafata cikin kwaraiwa da nuna zalamar sa.

      Sai kusan karfe uku sukayi bacci bayan sunyi sallama komawa suka yi bacci wadda har yakai shi ga makara, takwas saura ya tashi dan haka cikin gudu gudu ya tashi ya shirya ganin harya gama bata tashi ba ya nufi part din Safna ko zai samu abun da zaisa a cikin sa, harya shiga falon ya tuna da abun da tai masa jiya, cak ya tsaya sannan ya juya ya koma da baya part din Ammi ya shiga cikin sauri sosai.

Bayan sun gai Ammi tace ca nake ka wuce ai?

A’a Ammi makara mukayi, za samu wani abun da zan dan cin ne anan?

     Amsawa Ammi tayi sannan ta mike ta fita, bata jima ba ta dawo ɗauke da tire.

   Mikewa yayi ya amsa yai godiya sannan ya zauna ya fara sawa acikin sa cikin gudu gudu ya gama ya mike godiya ya sake yiwa Ammi karo na biyu sannan ya juya yana fadin, ” idan Rahma ta tashi zata zo.

    Toh Allah ya kawota lafiya.

   Juyawa yayi ya fita yayin da Ammi ta bishi da kallo tana mejin farin ciki cikin zuciyar ta.

                         *****

Waigawa tayi ta duba bayanta, ganin babu Modibo ta tashi zaune, agogo ta duba tara saura dan haka ta tashi da sauri, wanka ta fara yi bayan tayi wanka ta shirya ta tsintan kanta dason kiran Modibon.

    Kamar jira yake ya daga wayar yana fadin kin tashi?

   Cikin shagwaba tace tafiya kayi?

     Shima cikin wata irin murya yace, ” naga kina bacci ne bason in tada ki.

   Wani irin kuka tasa masa wadda yai matukar canja yanayin jikin sa dan haka ya lumshe ido batare da ya sani ba yana faɗin, ” menene haka?”

    Cikin kukan tace wlh bazan yadda ba, shinr ka wuce abun ka alhalin kasan idan ka dawo banan kake ba, ni kuma ka wuce min da sauran lokaci na.

   Nan danan fuskar Modibo ta faɗaɗa da matsanancin murmushi, ji yake inama tana kusa dashi take mishi wannan kukan shagwaba sam be saba dashi ba amman ya tsinci kansa cikin tsananin farin ciki yanzun da yaji Unaisa na masa.

   Idon shi a lumshe yace yi hakuri, ya isa, kina bacci banson in tashi ke amman gaba zan kiyaye miki lokacin ki?

   Allah bazan yadda ba saika biyani, kuma baci breakfast dina ba.

   Kwata ta farin ciki agurin Modibo be misaltuwa, murya can kasa yace agurin Ammi na karya, sauran awannin naki kuma kimin kudin su in biya.

   Kara shagwar gwabewa tayi, tare da saka masa rigima ita sam bashi da kudin da zai saya .

    Cikin sigar rarrashin yake faɗin, ya isa toh nasan me za’ayi, idan kin gama abun da kike mu haɗo a part din Ammi, kije can ki karya na gaya mata zaki zo.

                       ****

Anya kuwa Modibo zai yadda da wannan tsarin.

  Ai shiyasa nazo ta gurin ki idan ke kika masa mgn nasan zai bari .

Toh nifa gaskiya Hajiya bana daya daga cikin iyayen da suke ma ‘ya’yan su shishigi acikin lamarin su, ni kin ganni nan, idan ba wata matsala nagani bana shiga shirgin su, sannan shi wannan ba biki babu suna bare ace mishi ya cancanta, Ni ina ganin kibar yariyar nan a dakin ta zaifi.

    Hajiya nidai inason lallai inje da ita da zaki saka mana baki.

   Toh shikenan tunda kin matsa waya Ammi ta danna tasa a kunnen zuwa can tace, ” Modibo.

   Na’am Ammi.

   Momy Safna ce, tazo neman alfarmar abata Safna bayan kwana biyu ta dawo da ita.

    Jimmm yayi sannan yace, me hakan ke nufi Ammi?

    Kunyi rigima ne?

Ita kadai take hauka ta Ammi tun jiya da muka dawo asibiti.

     Nagane, idan ka dawo Mayi mgn, yanzun dai ga Momy ta a zaune izinin ka take nema.

       Shiru yayi tsayon lokaci har Ammi ta sake cewa, kai nake saurare.

    Ajiyan zuciya yayi sannan yace, ni Ammi bansan me zance ba, ban taba ganin irin hakan ba, amman shikenan kawai ki yanke hukuncin duk yadda kika gani shikenan.

     Da haka Ammi ta sauke wayar tana me yabawa ɗabi’un Modibo acikin zuciyarta, sannan ta kalli Momyn Safna tace, ya amsa jibi dai kikace ko?

    Eh insha Allahu jibi da kaina zan dawo da ita.

  Fatan sauka lafiya Ammi tai musu, adaidai lokacin da Momy ke kokarin fita Unaisa ta shigo.

  Kallon ta Momy tayi tace, ke sai yanzun kike zuwa, tun safe mijin ki yace zaki so.

  Ammi aiki na tsaya nayi.

Amman kin karya ko?

  A’a

Lallai kina wasa, kika tsaya aiki baki sa komai acikin ki ba, bari Modibo ya dawo inba dauki mataki ba akwai matsala.

     Misalin ƙarfe 04:50pm Modibo ne ke kokarin shiga falon Ammi wayar sa tai kara, yana dubawa yaga Suraj ne dan haka yaji gaban shi ya fadi tare da addu’ar Allah yasa ba jikin Yadikko bane ya tashi.

     Daga wayar yayi, yayin da Ammi ta bishi da kallo.

     Zuwa can taji yace, ” Moh’d?!, yazo?!

    Shiru yayi yana saurare daga cikin wayar yayin da Ammi ta mike da sauri tana fadin Rahma bani gyale na.

   Modibo taji ya cigaba da fadin, ” yazo da yaron?!!

   Saurare yake cikin wayar sannan ya shiga fadin, ” karka sake ka barshi yabar gidan nan, ka rike min shi gani nan zuwa, sakin kofar yayi ya juya…..

3 comments

  1. Pingback: Science
  2. Pingback: Diyalaa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *