Advertisements

Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 45

Posted by

BA LABARI BOOK

 

Advertisements

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 45

Ganin Haka Ammi ma tai saurin rofa masa baya, ko kafin ta fita Modibo ya fice agidan.

Advertisements

Itama motar ta shiga tare da kwalawa driver kira domin bazata iya tuki ba awannan lokacin.

Modibo ko yana isa ya hangi Falon Daddy su Suraj cike da mutane, dan haka can ya nufa da shigar da ya fara fadin, ina yake?, ya tafi ne??

Daddy su Suraj ne yace, Modibo nemi guri ka zauna yana nan, gashi nan.

Advertisements

Da hannu ya nuna masa farin dattijon dake zaune gefen sa kamar ruwa ya cisa, fari ne dogun Dattijo siriri sosai yana zaune daf da Daddy, cikin sauri Modibo ya nufeshi ya cakume yana fadin, ” ina yaron yake?, ina ka kaishi tsayon wannan lokacin ka raba uwa da ɗa ta?, kasan girman hakkin da ka dauka kuwa?, tsayon wannan lokacin shekara da shekaru kabar wannan baiwar Allah cikin zullumi da tunani, baka da hankali ne? wanni irin zalin ci ne wannan.

Cikin sanyi jiki mutumin ya kama hannun Modibo yana faɗin, dakata yaro sake ni.

Suraj Yana zaune dafda Daddy da hannun su cikin na juna yace, ” anki a sake ka, Modibo kwasa mishi mari.

Ammi dake shigowa yanzun ne ke fadin, ” a’a Modibo karka fara, waige waige take cikin son sanin inda Modibon yanke, hango shi tayi rike da kayan Moh’d din Yana jinjigashi tare da tambayan ina yaron yake.

Cikin Baccin Rai Daddy ya saki Suraj tare da fadin, jeka kayi abun da ranka ke su.

Ammi ma tsawa takewa Modibo akan cewa ya saki Moh’d.

Shiko Daddy cikin fada yake faɗin, Hajiya rabo dasu suyi abun da dukaga dama, tunda duk sun fi karfin mu, na rike Suraj amman sabo da rashin tarbiyya yana hannu na ɗin yake aikawa da magana, to kuyi tunda kun fimu iyawa.

Tarowa sukayi da Ammi sukaita masu fada, dan haka dole Modibo ya saki Moh’d yayin da ya zauna a gefe yana huci tare da Hararan gefen da Moh’d din yake.

Bayan falon yayi shiru tsawon lokaci sannan Ammi ta kalli Moh’d kallon mamaki, wani lokaci ne ya dawo mata kusan shekara ashirin baya da suka wuce.

Walokacin ta dawo daga kasuwa ita da Suraj da Modibo, suna zaune a bayan motar lokacin suna da kimanin shekara 14,

Wata mota tagani me zafi cikin gidan tun kafin su fito ta hangi ƙanwar ta Maryam ta fito daga cikin motar.

Zuwa can aka bude daya gefen wannan Moh’d din ne ya bayya, cikin nutsuwa ya gaida Ammi nan take ta ce wannan kuma fa, annan take sanar mata neman ta yake da aure, babu makusa ajikin sa kuma da alama yana da abun yi dan babu wahala a tattare dashi, dan haka tundaga ranar akasa bincike akan sa kuma aka gane mutumin Sudan ne tare da tabbatar da Asalin sa, nan mgnr aure ta fara kankama.

Tun awannan lokacin Suraj ya tsana Moh’d domin yaso kawai ta koma gidan mahaifin shi wadda ƙaddara ce ta raba auren su kuma baccin sun rabon yata Binta yanason ta koma amman taki amincewa.

Cikin kankanin lokaci aka shirya auren Yadikko da Moh’d, a Yobe suka zauna, bayan wani lokaci ya tafi da ita Sudan, sun dade acan tsayon lokaci suka dauka, sannan suka dawo Yobe, sai dai basufi wata daya da dawo wa ba zaman ya zama sai a hankali, wulakancin yau daban na gobe daban, dan haka Yaddiko ta fara yiwa yayarta korafin zaman da take da mijin ta.

Hakuri taita bata, domin a wannan kalokacin iyayen sun sun rasu dan haka bayan mutuwar auren Yadikko da Baban Suraj gurin Ammi ta zauna, haka kuma surikin ta mahaifin Abba su Modibo shike zane musu Uba tun mahaifin su nadarai shike daura masu aure aminan juna ne da suka taso tun suna yara.

Duk da hakuri da take yi abun yaci tura, domin kullum abun kara gama yake, dan daga baya har dukan ta yake yi, sabo da irin dukan da yake mata har ciki biyu saida ya zube ajikin ta.

Lokacin Da Yaddiko ta gaya ma Ammi ita tagaji da auren Moh’h gashi har ciki biyu ya zobe ajikin ta dalilin dukan da yake mata, hankalin Ammi ya tashi sosai dan haka ta kira Me martaba ta sanar masa.

Sosai ya nuna bacci ransa alokacin har Kano yaje ya bashi hakuri sannan yabawa Ammi, tun daga lokacin Ammi bata sake jin kansu ba, kullum suna waya kuma tana tambayan ta ba matsala tace mata babu.

Wata rana Ammi ta kira Yadikko ganin sun jima sosai basu haɗo ba, bayan sun gaisa Ammi tace, “idan na haihu zaki zo?

Kina da ciki ne?

Eh mana, harna kusa sauka.

Alhamdulillah, Allah ya raba lafiya, ai da naga shirun yayi yawa na dauka Magaji ne auta.

Dariya Ammi tayi tare da fadin ni kaina na cire rai.

Yar dariya Yadikko tayi sannan tace, toh ni dake ko wanne zai riga wani oho.

Masha Allah kice min wannan karon cikin ya tsaya?

Eh ya tsaya, dan yanzun yana cikin wata na biyar kenan.

A toni zan riga ki, danni fa kadan ya rage, addu’a sukama juna saidai koda Ammi ta haifi Afnan bebar ta taso zo Barka ba wannan ya tabbatar ma Ammi da ba wani zaman lafiya da suke.

Bayan wasu watanni ne Yadikko ta kira Ammi tana matsanancin kuka.

Ariki ce Ammi ke fadin me ya faru Maryam?

Cikin kukan take fadin, mun rabo da Moh’d tsayon wata shida da suka wuce.

Ajiyan zuciya Ammi tayi sannan tace Alhamdulillah, toh zaman me kike yi anan din?

Cewa yayi babu inda zani saina gama idda.

Cikin sauri Ammi ta mike tare da fadin, a’a Sam karki zauna, barin kira me martaba in sanar masa idan kika zauna kuma ya kashe ki fa?

Cikin matsanancin kuka tace, ai ya riga ya kashe ni.

Ya kashe ki?, ya zakice min ya kashe ki bayan gaki ina mgn dake?

Aunty na haihu dagani sai Moh’d adakin, nayi nayi yakaini Asibiti amman yaki, na galabaita aunty, banyi tunanin zan rayu ba, naji kukan jariri har ma na tambayi me na haifa, sannan naji Moh’d yace min namiji ne, daga nan ban san In da kaina yake ba, lokacin da na dawo hayyaci na, babu Moh’d kuma babu jaririn da na haifa, cikin matsancin kuka tace akwai zannuwa na guda biyu dana shinfiɗa dana fahimci bazai kaini asibiti ba, aunty duk babu su, babu wani alama dake nuna cewa na haihu sai ɗan alama jini kaɗan dake kasa sai kuma wadda ke jikina.

Innalillahi wa Inna ilaihir raju’un, tashi Ammi tayi ta zauna tana fadin mafarki nake yi ko idona biyu?

Sheshshekar kuka Yadikko keyi dan haka Ammi ta sake cewa, ” me yasa zaki yadda ki zauna, me ya kaiki, idan son ki yake ya mai dake mana.

Anan Yaddiko ke sanar da ita auren ya kare, domin saki har kashi uku yai mata, tun daga wannan lokacin Yadikko take neman zaucewa kuma tundaga ranar suke neman Moh’d ruwa a jallo amman BA LABARI Sai yau Allah ya gwada masu, mutane da yawa suna fadin kila daman amfani zai da jaririn yayin da mafi yawan mutane suke ganin kishi ne yai masa yawa so yake ya hana mata kwanciyar hankali da har zata iya auren wani.

Nisawa Ammi tayi bayan ta dawo daga dogon nazarin da tayi.

Batare da Ammi ta cire idonta ana Moh’d ba tace idon ka kenan Moh’d, idon ka kenan?

Cikin sauri ya kawar da kansa can gefe tare da share zufan dake wanko mishi.

Mahaifiyarsa dake zaune a gefe tace, kai muke saurare baki daya muna son muji in da ka kai yaron?

Cikin Hausar sa da bata fita sosai yace, na aikata kuskure babba arayuwa, lokacin da nafita da abun da Maryam ta haifa, shagon me wanki da kuka na na nufa, nan cikin gari Yobe, domin nafi sabawa dashi kuma na yadda dashi har cikin zuciya na dari bisa dari kuma nasan yana shagon ne sabo da nakai masa gogo da yamma na gaya masa Ina son kayan gobe sai yace yana da aiki amman bakomai ko kwana ne zaiyi domin ya gama min.

ina zuwa kai tsaye na buga kofa, daga cikin ya tambaye ni wanene?

Amsawa nayi, yanajin muryana kuwa ya taho ya bude kofar tare da tambayan lafiya da wannan daren?

Da ya ganni da jariri ya ɗan tsorata tare tambayan na daga ina, nan na sanar dashi matatace ta haihu dagani har ita bamu iya yanke cikin ba. gashi nikuma ba yan kasar nan bane bamu san kowa ba.

Abun da ya bani mamaki yadda mutumin ya rufeni da faɗa tare da tuhuma na inda nasamu jariri, cikin fada tsohon ke daga murya ganin yana neman tara min mutane naita bashi hakuri tare da tabbatar masa nawa ne bana wani ba.

amshe jaririn yayi a hannu na cikin sauri ya fara tafiya kamar zai tashi sama inason na bashi jakar kayan jariri ma amman ya min nisa dan haka na bishi a mota na bashi sannan nace mishi da safe zan dawo na karba jaririn.

Ko kulani beyi ba ya wuce abun shi nasan yana gani rashin hankali na ne na fitowa da jariri a irin wannan yanayin, Ni kuma awannan lokacin burina karna bar Maryan da kwanciyar hankali, domin nasan tana tafiya gidan tsohon mijin ta zata koma.

Da safiyar ranar na wuce Sudan, saida nai sati Uku na dawo bayan na mayar da tsohowar matata, kai tsaye shagon tumin na nufa sai dai shagon rufe yake, dan haka muka isa gida, wadda nake ginin zan Samu maryam acan, amman sai naga babu ita babu wani abu nata , da yamma na sake komawa shagon tsohon nan amma babu shi dan haka iyalina tace mu tambayi gidan sa, saidai abun mamaki duk wadda muka tambaya sai su ce ya daina zuwa kasuwa gidan sa kuma ba’a shiga, ba yadda banyi ba har kudi nake cewa zan bada a nuna min gidan ko daga nesa amman suka ki daga karshe ma wasu sukace wai shida matar sa duk aljanu ne, nashiga tashin hankali haka matata ma ta firgita dan haka muka shiga zullumi, bantaba sanin da irin mgnr nan ba harna dauki ɗana na bashi.

Kowa afalon kuka suke sabo da ganin irin muguntan da mutumin nan yai ma yadikko,

Itako Yadikko zuwa wannan lokacin hannu tasa ta danne kirjin ta, yayin da jama’ar gurin sukayiwa Moh’d ɗin can……

 

 

5 comments

  1. Pingback: dultogel
  2. Pingback: mexican dutch king
  3. Pingback: free chat rooms
  4. Pingback: vakantie

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *