Advertisements
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 47
Ahankali ya tura kofar ya shiga ya zauna,
Advertisements
Kallo Yadikko tabi Modibo dashi tana sanye da hijjabi hannun ta rike da carbi, zama tayi bakin gado tace, ” Modibo yaya aka yi ne?
Gyaran murya yayi sannan yace, nazo ne muyi wata mgn yadikko.
Toh inajin ka?
Advertisements
Yadikko wai wannan haihuwar da kika yi, kina da tabbaci akan abun da kika haifa?
Eh, Na miji ne Modibo”
Toh amman Yadikko, naji kince ke bakiga abun da kika haifa ba da idon ki?
Bangani ba, amman naji kukan sa.
Wannan ba hujja bace yadikko, kuka ai baya banbance mace ko na miji.
Jimmm, Yadikko tayi zuwa can tace kaga Modibo ka kwantar da hankalin ka, wato daren yau bakai bacci ba, kana ta sake sake, haka Suraj tsakiyar dare saigashi, duk masifar sa wai yazo kara bani hakuri, nace hakuri yazama dole, toh kaima gaka da duku duku, kuyi hakuri ku daina wahalar da kanku, ku fuskanci abun dake gaban ku.
Cikin tsananin tunani Modibo ya sake cewa, amman Yadikko Ni ina ganin mace kika haifa fa?
Modibo, Na miji ne, yana faɗowa duniya nace masa me na haifa yace min Namiji ne, yanzun Modibo koma dai menene ai babu shi dai ko?, dan haka nake ganin wannan mgnr batama taso ba, tashi kaje gida dan Allah ku kwantar da hankalin ku, badai ni bace?, nahakura
Wanni irin kallo Modibo yaiwa Yadikko me cike da tsananin tausayi, sannan yai mata sallama ya taso cikin zullumi da matsanancin tunani ya baro gidan, dakin Ammi ya yada zango inda ya shiga sanar da ita zargin shi, bayan ta gama sauraron sa tace, ” Kaga Modibo banson neman jaraba, karka daga ma yariyar mutane hankali, banda abun ka ta yaya hakan zai faru?, koko kafara zaucewa ne?
Ummi labarin ne yazo iri daya.
Yazo iri daya a ina?, ita yariyar ka tabajin ta ne tace basu ne suka haife taba?
A’a.
Toh meye naka na wannan tunanin?, toh wlh ka kiyaye kanka, karka ballo mana wata fitina, domin tanajin kayi irin wannan mgnr cewa zata yi kaima baka yadda da ita ba, ina sam wannan ma ai ba abun da zai yiyu bane kake faɗa, ku kusa ma karka kara irin wannan tunanin bashi da tushe balle makama, inace a hannun dangin mahaifiyar ta ka amsa auren ta?, toh meye naka na wanni tunanin banza da wofi, banaso.
Cikin rashin kwarin jiki Modibo yace shike nan, Ammi
****
Tun daga wannan rana Modibo ya fara kokarin sakin jikin shi, sai dai shi anashi bangaren ya karfafa tunani sa akan zai yi wuya ace Rahma ba yar Yaddiko bace duk da cewa babu kammani.
Kwanan Safna biyu Momy ta dawo da ita kamar yadda ta faɗa.
Anar Modibo ya koma dakin ta, inda ta tarbeshi da fara’a kamar ba ita ce ke cewa sai an sake ta ba, hakuri ta bashi akan abun da ya faru.
Ranar da ya gama kwana biyun da adakin Safna, tsintan kansa yayi da rashin walwala, be gama gane meke samun sa ba Saida yaji beson komawa gurin Rahma , tambayan kansa ya shiga yi meke damuna ne?
Wurin aiki ya wuce batare da yaje gurin Unaisa ba, bayan ya dawo ma dakin Ammi ya sauka can yaci abin ci har ya raba dare sannan ya taso, koda ya shigo Part ɗin sa, kwanciya yayi afalon sa batare da ya shiga cikin ba.
Saida Asuba sannan Unaisa ta lura afalon ya kwana, domin jiya gajiya tayi da jiran shi har bacci ya dauke ta, dan haka ko yanzun da tagane afalon ya kwana bata ce mishi komai ba, wucewa tayi abun ta zuwa Part dinta cikin tunani sosai.
Kwata kwata be nemeta ba ranar ma saidai sosai hakan ke takura mishi tare da yawan tambayan kansa menene ke faruwa.
Yauma da ya dawo dakin Ammi ya nufa, yaci abincin ya kwanta koda yaje sallah dakin ya kuma sauka sannan suka zauna shida Magaji har bacci ya fara daukan sa sannan ya dawo Part dinsa, yauma afalo ya kwanta, saidai abun da be sani ba Unaisa sam yau bata tako dakin sa ba.
Washegari ko yana dawowa ya wuce dakin Safna cike da zumudin, wannan abun yai matukar daga hankalin Unaisa domin duk shigowa da fitan sa tana gani ta window. Kuka taci sosai harta gode ma Allah.
Tunda ya koma dakin Ammi da safe kawai yake zuwa gaida Ammi.
Abun da yai matukar bawa Ammi
Mamaki yana gama kwana biyun sa, saiga shi dakin ta tare da rokon abinci dan haka Ammi ta kalle shi sosai tace, ” wai meke samun ka ne Modibo?
Jimmm yayi sannan yace ba komai Ammi.
A’a Modibo, ko kunyi fada da Rahma ne naga kwana biyu bakacin abincin ta kuma nan kake raba dare?
Nan danan ya shiga cikin tunani sannan yace, nifa Ammi haka kawai nake jin banson zuwa inda take.
Subuhanallahi, ta maka wani abu ne, ko kunyi faɗa ne?
A’a bata min komai ba Ammi.
Jimmm Ammi tayi sannan tace, Amman shine baka faɗa ba kai shiru, kana addu’a kuwa.
Inayi Ammi.
Toh ka dinga kokari kana fin karfin zuciyarka, mikewa Ammi tayi ta ta kawo mishi abincin kadan sannan ta isa gaban madubin ta ta dauko wata leda, kwanceta tayi sannan ta isa gaban abincin ta barbade shi sannan tace ta koma ta zauna.
Kallon abincin yayi sannan ya kalli Ammi tare da kawar dakai zuwa can ya juyo ya kalli Ammi yace, “Ammi ai kin lalata min abincin.
A’a maza ka cinye shi tass ka tashi ka tafi magani ne ba wani abu ba, kuma daga yau nan zakaci abinci ka karka sake ci ko ina, Umarni ne na bayar.
Kallonta yayi sannan ya sake daura idon sa a abincin tare da fadin, yanzun ci zanyi kenan?
Ci zaka yi Modibo, kasan dai bazan cutar dakai ba ko?
Nasani Ammi, Ni ba nufina kenan ba, ɗeban abincin ya fara yi yana kaiwa bakin shi har ya cinye tass sannan Ammi tace, toh tashi ka wuce, ka danne zuciyar ka, akwai hakkin ta akan ka kuma idan ka zalinceta Allah zai tambaye ka.
Jimmm yayi sannan ya d’ago ya kalli Ammi ahankali yace, Nagode, Mikewa yayi kawai ya fito zama yayi afalon tsayon lokaci, beji motsi ta ba kuma bega ta aje abinci ba dan haka ya nufi ɗakin, ganin bata ciki ya nufi kofar ta.
Kwance ya sameta tsakiyar gado, kayan jikin sa ya cire ya shiga toilet dinta, wanka yayi ya fito, bayan ya gama shiryawa ya hau gadon ya kwanta, ɗago ta yayi ya daura kirjin shi tare da zame hular dake kanta yana kokarin shafa gashin kanta ta zame ta sauka daga jikin sa tana ture shi.
Tsaya mana ina zaki?
Karka sake min mgn ka kuma tashi ka fita.
Ɗanki ne ni? bangane karna sake miki mgn ba, kizo ki kwanta.
Bazan kwanta ba.
Nine kike cema bazaki kwanta ba.
Eh, bazan kwanta ba, ka tashi ka fita.
Bazan fita ba, gidan ki ko nawa, wlh idan bakizo kin kwanta ba saina bata miki rai.
Wani irin kallo ta mishi sannan ta fice a dakin.
Afalon ta ta zauna, Bayan kusan minti goma da fitan ta ta ganshi a gaban ta yana fadin, tashi Muje Rahma ina bukatar ki akusa dani sosai.
Ƙin kulashi tayi, duk da cewa ya daɗe yanai mata nacin harya gaji ya fito yace yana son hakkin shi, amman ta ki, dan haka ya ya rabu da ita sai dai ya kule sosai, domin shi ya tsana irin wannan horon.
Gadonta ya koma ya kwanta yana jero addu’a abakin sa, daker bacci ya dauke shi, washegari da safe ya gama shiryawa tsaf ransa ne ya cigaba musamman idan ya tuna yadda Unaisa ta gwammace kwana a falo.
Bayan ya gama shiryawa fitowa yayi cikin shirin zuwa aiki afalon ya sameta kwance har ya wuce ya dawo da baya tare da fadin, ” tunda ban isa dake ba ki tashi kibar min gida”
Da sauri Unaisa ta kalle shi sannan tace, “toh ”
Juyawa yayi ya fita batare da ya waiwayi bayan shi ba, itama Unaisa yana fita ta mike.
****
Modibo Part ɗin Ammi ya isa ya karya sannan ya wuce aiki, koda Ammi ta ganshi wani iri batai mamaki ba domin halin da ya gaya mata yana cikin jiya dan haka yau tun ana fitowa masallaci ta tura Magaji gurin Mai martaba domin ya sanar masa da sabon yanayin da Modibo yake ciki.
Misalin 4 na yamma Magaji ya dawo da sakon kakansu kamar yadda Ammi ta bukata, sannan da kunshi dabino da yace akawo ma Rahma.
Murmushi Ammi tayi tana rike da kunshi dabino take fadin, Allah sarki Baba, ya dai kwallafa rai yana son yaga kwan Modibo aduniya, Allah uban giji yasa muna da rabon gani gaba daya, yadda mai martaba ya kagu Modibo ya haihu ko mu albarka.
Magaji ne yai dariya sannan yace, ” ai Modibo mutumin sa ne, idan ya faɗa maga kamar fadan Allah Modibo keji, yadda yake musu biyayya ko yaran sa basa mishi hakan.
Murmushi Ammi tayi sannan ta fara kiran layin Unaisa, zuwa can ta sauke wayar cikin mamaki tace, ” wai ina Rahma ta shiga ne tun safe nake kira bata daga ba.
Kallo Ammi kawai Magaji yayi sannan ya dauke kansa batare da yace komai ba.
Masalin karfe biyar na yamma Modibo yayi sallama dakin Ammi har wannan lokacin ita da Magaji ne zaune.
Bayan sun gaisa ne ta cika mishi kofi da sakon da Magaji ya karbi bayan ya shanye ne Ammi ta dube sa tace, ” Rahma ko me ya samu wayar ta tun bayan fitan ka da safe nake kiranta amman bata daga ba.
Kallon Ammi yayi tare da jin faduwan gaba yace, ” Ammi batazo nan ba?”
kunyi zata zo nan ne?
Mikewa yayi da sauri batare da ya bawa Ammi amsa ba, dan haka suka bishi da kallo, ganin ya jima da fita be dawo ba Ammi tace ma Magaji yaje Part din nasu ya gani.
Afalon ta ya samu Modibo zaune, waya manne akunnen sa, zama Magaji yayi gefen sa yana fadin Ammi tace lafiya dai ko?
Wayar na manne akunnen sa yake faɗin, ” bata nan fa Magaji”
Sauke wayar yayi, tare da sake fadin, bata nan, nakirata kuma bata daga ba.
Cikin sauri Magaji yace, toh nasan tana gidan Afnan.
Bata can, nakira ta tace batazo ba, kuma Baba yace min ina fita ta fita.
Cikin rashin Fahimta Mmn Magaji yace toh ina taje?
Shine nima nake tunani, Yadikko ma tace batazo ba, har Muftahu nakira duk bataje ba…
Wayar Ammi ce ta katse su bayan Magaji ya daga yace, Ammi bata nan fa.
Bata nan?, ina taje?
Shine muke tunani Ammi?
Ina Modibo kira min shi yazo yanzun nan.
Sauke wayar yayi tare da fadin, Ammi na kira, atare suka mike yayin da Modibo ya shiga tunanin yadda zai amsa tambayar Ammi.
****
Kallo ta bishi dashi tsayon lokaci sannan tace, ka kira Afnan?
Ammi ba inda ban kira ba.
Daure fuska sosai Ammi tayi sannan tace, ” me ka mata ne Modibo?”
Kawar da kansa yayi tare da jan tsaki sannan yace, ” Ammi taurin kai tamin”
taurin kai?, kai baka duba abun da ka mata ba?, yaushe ka zama haka?
Kawar da kansa ya sake yi cike da sanyin jiki.
Kare masa kallo Ammi tayi sannan tace, “ai shikenan, saika neme ta a Yobe, tunda ance tun safe ta fita, kuma nasan be wuce kai kace mata tabar maka gida wannan halin ka ne.
Kawar dakai yayi batare da yace komai ba, zuwa can yaja tsaki tare da fadin, Ammi ko zaki tambayi Dada miji.
Cike da faɗa tace bazan tambaye ta ba, kai kace ta fita kuma ta fita, wannan ya nuna baka damu da inda zata ba koma ina zata ta je.
Ba haka bane Ammi.
Karka gayamin mgnr banza Modibo, me na gaya maka jiya?
Kawar da kansa yayi tare da fadin, ” kiyi hakuri Ammi ni bansan ma yadda akayi ba.
Magaji binsu yayi da kallo domin be gane kan mgnr tasu.
Tsaki Modibo yai ta ja tsayon lokaci zuwa can Ammi tace kai karka dame ni da tsaki tashi ka fita ka bani guri.
Yadda tai mgnr Afusace ya san lallai ranta ya ɓaci, mikewa yayi ya fita yana waiwayen ta.
Magaji ma kallon tausayi yabi Modibon dashi, dan be taba ganin shi da Ammi sun bata har Ammi tamai faɗa haka ba, kullum yabon shi take.
Ammi na ganin fitan Modibo ta daga waya ta kira Dada bayan sun gaisa Magaji yaji Ammi fadin, Rahma ta iso ko?
Beji amsan da aka bata ba saidai yaji ta kuma cewa toh ina ga tana hanya dan Allah data karaso ki sanar min.
Sauke wayar tayi tare da mikewa cikin tsananin tashin hankali, har misalin goma na dare babu wani labari dan haka Ammi ta sanarwa Abba, sosai ransa ya bacci har yaso yafi Ammi daukan zafi, zaune duk a babban falon Abba, Ammi da Magaji sai Abban dai yai shiru yana tunanin ta ina za’a fara, daidai wannan lokacin wayar Ammi tai kara ganin Dada ce tai saurin dagawa daga can cikin wayar Dada tace, Toh Hajiya ga Rahma ta shigo iso yanzun nan, amman ba lafiya, sai koke koke kawai take.
Alhamdulillah Ammi ta faɗa tare da sauke ajiyan zuciya, sannan tace, dan Allah ki rarrashe ta, ita da Modibo ne, muna nan duk hakali ya tashi nace duk yadda akayi nan ta nufo.
Ashema baku san ta taho ba?, sabo da rashin hankali kina ciki gidan ta tsalle ki tayo nan?
A’a ai ba laifin ta bane,laifin Modibo ne.
Da haka suka sauke wayar yayin da Ammi take sanar dasu Abba
Godiya Abba yaiwa Allah shiko Magaji bayan yayi Barka mikewa yayi yai masu sallama bayan ya fito ya nufi part din Modibo domin ya tsegunta mishi Rahma ta isa Yobe.
Yana kokarin shiga part ɗin yaji Modibo na kiran sa daga bayan sa dan haka ya waiwaya zaune yake cikin mota dan haka yai saurin karasawa gurin.
Idon Modibo yaga yai jawur dan murmushi yayi sannan yace, an ganta fa?
Cikin sauri ya kalli Magaji tare da fadin, da gaske ko wasa?
Wlh, duk yadda akayi ya gaya masa dan haka ya saki ajiyan zuciya, yana don ya kira Dada dan yaji ma kansa amman kuma kunya abun ke bashi da haka ya kira Yadikko ya sanar ma, Number Yadikko tace ya tura mata, zuwa can ta sake kiran Modibo ta sanar masa sunyi waya tana can, nan tace masa ya shirya da an fito masallaci zasu suje su dawo da ita, cike da farin cike ya amsa shiyasa yake tsananin son Yadikkon sa domin sosai take damuwa da damuwar shi.
Sallama sukayi da Magaji ya nufi cikin gida, Part ɗin Safna ya nufa yayin da ganin sa ya cika ta da farin ciki, yau ji take tamkar tafi ko wacce mace daukaka a duniya tare da zama har gaban goshin Modibo……
5 comments