Advertisements

Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 48

Posted by

BA LABARI BOOK

 

Advertisements

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 48

Ji tayi gaba daya ta kosa gari ya waye ya fita domin ta labartawa Momy.

Advertisements

Ko kusa bata tambayi Modibo yadda akayi ya kwana ɗaya dakin ya dawo gurin ta ba, haka kuma ko da ya nemi ta bata mishi musu ba, sosai taga yana zumudi wannan yai matukar faranta ranta.

Saidai yana dawowa masallaci taga ya hau shiri, akwai alamun akwai inda zashashi, sai dai Momy ta gargadeta ban da tambaye tambaye, dan haka ko bayan ya gama shirya da ya sanar da ita zaiyi tafiya bata iya cewa ina zashi ba, fatan sauka lafiya kawai tai masa.

Yanajin shigowan mota gidan ya fito domin yasan Suraj ne ya kawo Yadikko, yana fitowa Yadikko na sakkowa daga motar, gaidata yayi sannan ya isa gurin Suraj yayin da Suraj din ke fadin, ” dalla gafara can, dubi yadda ka hana mutane bacci safiya, kuma wai Mama cewa tayi ni zanja motar.

Advertisements

Dariya Modibo yayi sannan yace, da kyau, Yadikko ta kyau ta, nasan da ace ba Yadikko ni kadai zani bikon nan, dan Ammi tayi fushi, kai kuma baka da mutunci.

Eh wlh banni dashi, yanzun ma matsamin aka yi, wai baka da nutsuwar tuki, idan baka da nutsuwa driver ya kaiku mana, nifa duk kun kashe min abubuwan yi na.

Dariya Modibo ya sakeyi sannan yace, daidai kenan.

Sokkowa Suraj yayi suka nufi gaida Ammi inda suka samu Ammi nawa Yadikko fada akan dan me zata raka Modibon.

Cikin sauri Suraj yace, Ammi nima abun da nagani kenan.

Wallahi kuwa Suraj, shifa yace ta bar mishi gida, tunda ta fita ba shikenan ba.

Suraj ne ya sake fadin, shi dai nagani Ammi.

Hararan shi Yadikko tayi sannan tace, mudai kice Allah ya tsare kawai, zan raka shi ya dauko matar shi, kuma saina mata fada, mu bamu da mutunci a idonta kenan da yace ta fita saita tsallake mu ta wuce abun ta.

A’a karki mata fada, ai maganin shi tayi, gobe ma ya kara ce mata ta fita, tun shi saran shi kenan.

Aiko saina mata, shima fushi ne yasa shi ya faɗa, kawai sai ta dauki kafa tabar gari, tana dauke da karamin ciki?

Suraj ne yace shi besan halin da take ciki bane ya kore ta?

Hararan Suraj Yadikko tayi tare da fadin, tashi ka fita.

Yana dariya ya Amike ya fita yayin da Modibo ya bi bayan shi.

Yadikko ma mikewa tayi ta fito inda Ammi ta biyo bayan ta tana masu fatan sauka lafiya, bayan motar ta shiga yayin da Modibo ma ya shige kusa da ita ya zauna.

Suraj ne ya juyo Yana kallon Modibo tare da yamutsa fuska yace ka dawo nan mana.

Batare da Magaji ya dube shi ba yace, ni kusa da mamana zan zauna.

Mama kimai mgn ya dawo nan?

Dan Allah muje Suraj, Yadikko ta fada dan haka Suraj yaja motar yana fadin, wlh Mama abun da kike min banjin dadin shi.

Bata tanka masa ba dan haka suka sharari hanya kawai.

*****

Misalin biyu da rabi suka isa, gidan su da suka zauna sadda sukazo amsan magani Modibo yace su nufa, Suraj ne yace, me zaisa mu sauka anan muda zamu koma yau?

Ai Dada ta dawo nan da zama Modibo ya bashi Amsa.

Masha Allah Suraj ya fada sannan ya kara da cewa ka kauta kuwa.

Suna isa bakin gate din aka bude musu suka shi cikin gidan.

Motar su na tsayawa Dada ta fito taryan su, cikin fara take fadin, Sannu ko da zuwa, Unaisa ta taso ko.

Cikin sake fuska suke sauka acikin motar inda suka bi bayan Dada zuwa cikin gidan.

Falon gidan duk suka Zazzauna, a inda Dada ta kawo musu ruwa da abincin dan daman tasan da zuwan su.

Modibo ko banda raba ido babu abun da yake yi, kula Yadikko tayi da hakan dan haka tace, Dada ina Rahma?, mijin ta nata raba ido.

Cikin sauri Modibo ya sunkuyar dakai yayin da Suraj ya gallawa Modibon harara, sanan ya dauki kansa.

Dada ce tace, gatanan zuwa tana sallah ne bacci taitayi sai yanzun na tada ta tai sallah.

Mikewa Dada tayi ta basu guri wai dan suci abincin saidai Yadikko da Suraj ne kaɗai sukaci Modibo ruwa kawai ya kurba.

Zuwa can Dada ta dawo Unaisa nabin bayan ta, ganin su zaune afalon jikin Unaisa yai sanyi kaɗa.

cikin sauri ta nufi Yadikko, gefen yadikko ta zauna tare da kama hannun ta cikin nuna farin ciki.

Zame hannu Yadikko tayi tare da fadin, ba wani nan, sakar min hannu ni, ai baki sanni ba tunda kika iya tsallake ni kika bar garin.

Cikin kwalkwal da ido tace, Yadikko shi fa yace na tafi.

Da yace ki tafi mu baki dauke mu iyayen ki bane?

Kwalkwal ta sake yi da ido yayin da hawaye suka cika idon ta.

Ganin haka Yadikko tace karki sake yin irin wannan abun, Ammin ku na cikin gidan kika iya tsallake ta kikayo nan, ko tana nuna miki banbanci ne?

Tun kafin Yaddiko ta rufe baki ta girgiza kai sannan ta bude baki tace shine yace in fita agidan.

Kibar fadin wannan mgnr, bacin rai ne yasashi ya faɗa, ki kuma bawa mijin ki hakuri.

Da sauri ta kalli Yadikko sannan tace, bam mishi komai ba fa Yadikko, kuma biyan ma ai ba fita nayi haka kawai ba dan yace In fita ne.

Cikin faɗa Dada tace amman koma dai menene tun da akace ki bashi hakuri ai saiki bayar ko?

Da saurin ta ta kalli Dafa sannan ta kalli Yadikko, hawayen dake makale a idon tane ya zobo, cikin sauri ta juya musu baya gaba dayan su sannan ta bude baki ta muryan ta me cike da rawa tace, ” kayi hakuri Hamma Modibo.

Gyaran murya yayi cikin sassanyar murya yace, ba laifin ki bane, ni ya kamata in baki hakuri, Allah ya huci zuciyar ki.

Wani sanyi taji cikin ranta jin furucin Modibo, sosai halin ko in kulan da ya nuna mata ya dame ta.

Itama Dada sosai farin ciki ya kamata acikin ranta take fadin, lallai Allah ya daga darajar Unaisa, mutum mai cikar kamala kamar Modibo har ya bude bakin sa ya bata hakuri cikin bainar jama’a, lallai Modibo ba karamin so yakewa Unaisa ba.

Yadikko ce tace, ko kufa.

Mikewa Unaisa tayi tana kokarin komawa ciki, Dada tace, zoki dauki abin cin nan ki kai mishi wacce falon, kallon Modibon tayi tace, Modibo kuje kaci abincin.

Ba musu ya mike yabi bayan ta, yayin da gaba dayan su suka bisu da kallo.

Suraj ko acikin ransa yake mamakin yadda a kayi kiri kiri yanzun Unaisa tabar gaida shi, yayin da abun ke masa ciwo sosai, yau ko kallon inda yake ma batayi ba bare yasa ran zata gaida shi.

****

Ajiye abincin tayi tana kokarin juyawa, Modibo ya shigo, cikin sauri ya riko hannun ta tana kokarin kwacewa yana sake saka karfin sa harya hadata da jikin sa ya rungume, kanshi sa da nata ne suka cakude waje guda.

Ajiyan zuciya Modibo ya sauke haka ma Unaisa, kansa ya kama ya kura mata ido yana mejin wani farinciki na ziyartan sa, dan matashin cikin dake jikinta yaji Yana tokaran sa dan haka ya sausauta mata rokon da yai mata tare da fadin, ” Allah ya huci zuciyar ki, ki yafe min kinji?

Kawar dakai tayi dan haka ya kama kan nata, juyo da ita yayi tare da fadin, bude idon ki ki kalleni mana, nine fa, Modibon ki, haba Rahma rikeni zakiyi azuciya?

Cikin sauri ta kawar dakai.

Karki rikeni kinji auty na, jiya kawai da baki sainaji kamar ba, a duniya nake ba, kece mahadin jikina, gaba daya ji nayi komai ya tsaya cak, karewama kinsan me naji?

Ganin ta sunkuyar da kanta yaciga ba da cewa, Allah ne kaɗai yasan irin tashin hankalin da na shiga, cikin ta ya shafa sannan yace, ki yafe min kinji?

Ahankali ta zame ta zauna akujera Binta yayi ya zauna hannun kujerar da take kai cikin rasa hanyar da zai ɓullo mata zuwa can wani tunani yazo masa dan haka yayi murmushi sannan ya juyo ya kalleta tare da fadin, ” tunda na fahimci baki gurin Ammi zuciya ta tai wani irin bugawa, duk ilahirin jikina ya amsa, nasan lallai ina kewan masoyiya ta, mafi soyuwa agare ni, zuciyata da gangar jikina basu dawa cikin hali ba saidai na tabbatar da inda kike, dan Allah karki sake min irin haka.

Tunda taji ya ambaci mafi soyuwa ta lumshe idonta tare dajin wani irin farin ciki dan haka yanzun ma da ya kare mgnr tace.

Bakai bane duk ka canza min?

Na bari bazan kara ba.

Idan ka kara fah?

Kimin bulala amman acikin ɗaki.

Juyawa tayi ta mai wani irin kallo daya sashi murmushi tare da jawota jikin shi ya rungume tare da sunbatan ta, ajiyan zuciya yake saukewa yanajin yada itama take saukewa tare da kara yin lamo ajikin shi, cikin ta yakejin Yana tokare su dan haka ya ɗan rabo jiki shi da nata yana me addu’ar Allah yasa zaton da yake akan Rahma da yadikko yama gaskiya.

Kiran Yadikko ne ya shigo wayar sa dan haka yaja hannun Rahma suka fito falon.

Yadikko ce tace Modibo ka barta dazo mu kama hanya mana.

Zama yayi nesa da Yadikko yana fadin, toh, amman naso kafin mu tafi kisata ta fito da kayan mahaifiyarta ta bada sadaka, wai ita baza bada ba take cewa.

Suraj ne yace toh ka barta mana, kasani ko tana da burin nan gaba ta bude gidan tarihi…..

5 comments

  1. Pingback: article
  2. Pingback: free chat
  3. Pingback: bdsm chat rooms
  4. Pingback: mostbet

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *