Advertisements
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 40
Advertisements
Ganin shigowan shi Ammi tace Yaya dai?
Be iya cewa komaiba ya nemi guri ya zauna
Bin shi da kallo Ammi keyi ganin sa tayi ran sa hade sosai, dan haka tai shiru kawai tana binsa da kallo.
Advertisements
Safna dake gefe ma kallon shi take, domin wannan halin nashi ba bako bane awajen ta.
Shiru dakin yayi tsayon lokaci, zuwa can wayar shi ta shiga Kara saidai be kula wayar ba.
Ammi ce ta kalli shi tace ka dauki wayar Mana.
Ahankali ya dauki wayar ganin Suraj ne yasa wayar a kunnen sa batare da yace komai ba.
Zuwa can, yace a’a, jimmm yayi yana saurare acikin wayar, zuwa can kuma ya kashe wayar.
Agogo ya kallah goma saura dan haka yaji tashin hankalin shi ya karo, tunin mintin talatin din da yabama driver ya cika, dan haka ya dago ya kalli Ammi tare da fadin yau zan kori driver nan.
Wanni driver kuma?
malam Abdullahi ya Bata amsa a fad’ace.
Me yayi kuma?
Ammi shi ya fita da ita, kuma datace mishi zata sauka akan ahanya ya barta ya dawo gida abin shi, sabo da bashi da hankali, kuma tun akan Safna na mishi mgn idan banine nace mishi ya kaita wani guri ba duk yadda zata mishi mgn karya kaita, in ita taga zata fita da kanta taje, toh akan me zai fita da Rahma?
Cikin sanyi Ammi tace Modibo, ka dinga hakuri dan Allah, shekara da shekaru muna tare dashi bashi da matsala, kuma Yaya zai da ita tace mishi zata sauka.
Ammi ai nata taba gaya mishi banson haka Nan.
Akan ta ai baka mishi wannan mgnr ba, kuma shi ka mishi uzuri ya saba da kaisu Unguwa ita da Afnan ya kuma baro su acen, wani lokacin ma saidai su dawo da kan su.
Komawa yayi ya jin Gina da bayan kujera Yana jin yadda wayar sa keta Kara ya gaza dauka.
Zuwa can wayar Ammi ta fara kara cikin sauri ta dauka, Magaji ta gani Dan haka tai saurin dauka tana fadin, Yaya?
Gamu Nan zuwa Ammi mun dauko ta.
Toh Alhamdulillahi sai kunzo.
Sauke wayar tayi tace Gasunnan zuwa Wai sun ganta.
Safna ce tace Alhamdulillah yayin da Modibo ke fadin a Ina?
Ai sai mu Bari su iso tukuna, tunda an ganta dai ai Alhamdulillah.
Daidai wannan lakacin wayar sa tai Kara Yana dagawa yaga Suraj ne dan haka ya daga.
Fito gani awaje, batare da yace komai ba ya juya ya fita.
Cikin Motar Suraj ya shiga ya zauna yana shafa kansa daga gaban goshi zuwa keya tare da fadin, daga Ina haka?
Daga Asbiti Magaji yace min kana gida nace ai be kamata ka zauna a gida ba, inda ya sauketa zaje a dudduba.
Ajiyan zuciya yayi sannan yace sunyi waya yanzun ma ai sun ganta.
Toh Alhamdulillahi, saika mata fada sosai, ta cika yawo duka duka kwanan ta nawa da tarewa dahar zata saka kafa ta fita.
Shigowan motar su Magaji yasa Modibo ya maida hankalin shi a Kan motar Yana ganin sun faka ya bude motar Suraj ya fito, adaidai lokacin dasu Suraj din ke sakkowa, gani yayi ita ma ta sakko dan haka yai saurin karasa wa.
Suraj Magaji Muftahu Modibo duk binsa da kallo suka yi, tare da tausayin Rahma akan hukuncin da suka San Modibo zai iya yankewa cikin fushi.
Cikin sauri Modibon ya karasa gabanta yasa Hannun sa ya ware alamar tazo gareshi, sunkuyar da kanta tayi, tsaron sa fal zuciyar ta, ganin haka ya Mika hannun sa ya jawota jikin shi ya rungume ta tsam kar ma zai sata cikin jikin shi tare da sunbatan ta kota Ina.
Mamaki ne ya cika kowa a gurin yayin da suka bishi da kallon Mamaki har yanzun ya kasa sakin ta sunbatanta kawai yake yi
Tsayon lokaci sannan ya dagota ya rike hannun ta tare da fadin Muje.
Su Magaji ne suka fara yin gaba, dakin Ammi duk suka shiga yayin da Ammi ta mike da sauri ta tare Unaisa tana fadin, Aina kukaganta Magaji?
Gidan Afnan, ai naso in hado har Afnan din in taho da ita abasu Kashi gaba daya, wanni irin rashin hankali ne wannan.
Innalillahi wa Inna laihir raju’un Ammi ta fad’a sannan ta Kara kallon Unaisa daga jikin ta tace, toh yanzun ke da bazaki dawo gida ba kenan toh me yayi zafi ne?, juyawa tayi ta kalli Modibo tace ko kunyi rigima ne?
A’a, Ammi, ba komai, juyawa yayi ya kalli Unaisa tare da fadin, mijin Afnan din ya ganki?
Cikin kawar dakai ta girgiza Kai.
Ajiyan zuciya yayi sannan ya mike ya kalli Safna dake gefe yace Safna muje.
Mikewa Safna tayi tana ma Ammi Sallama har sunkai kofar Ammi tace toh ita Rahma fa?
Ammi ta zauna gurin ki, Saida safe.
Me hakan ke nufi Ammi ta sake tambaya.
Bakomai fa Ammi.
Toh shikenan Ammi ta fad’a sannan ya juya ya fita.
Suna fita Ammi tabi Rahma da kallo sannan ta kawar da kanta can gefe, shiko Magaji cewa yayi naso daya zane tane kila ya huce, ni kaina idan bedan dake taba bazanji na huce ba gara Afnan na rankwashe ta.
Akan me zai dake ta Ammi ta fada cikin hade fuska.
Muftahu ne yace ai ba wani hukuncin da zai mata bakaga yadda yayi ba da ya ganta.
Kofa Magaji ya nufa yana fadin, toh Allah ya kauta.
Muftahu ma mikewa yayi yabi bayan sa yana fadin Ammi saida Safe
Allah ya tashemu lafiya tace, sannan tai shiru tsayon lokaci tana kallon Rahma, zuwa can ta daga wayar ta sa a kunnen ta tana fadin kazo ina son ganin ka,
Unaisa batasan wa takira ba dan haka tai shiru kawai tana jiran taga waye zai shigo.
Bayan kusan minti goma Modibo ya Turo kofar ya shigo, sau daya ya kalli inda Unaisa take ya dauke kansa sannan ya isa gaban Ammi ya zauna yana fadin gani Ammi.
Mgnr da kayi ne ban fahimta ba kace ta zauna anan shine nake son inji badai fushi bane kayi ko?
Dagowa yayi ya kalli Unaisa idon shi akanta yace, A’a Ammi, banyi fushi ba.
Toh meyasa zakace ta zauna anan.
Ammi ba wani abu bane, karki damu naga ne ita kadai ce a part din yau shigasa nace ta zauna anan, zuwa jibi intaso saita koma.
A’a toh meye kuma intaso?, Ammi ta fada sannan ta kalli Modibo hankali kuma ta juya ta kalli Unaisa dake wasa da hannun ta.
Eh mana Ammi, bakiga abun da taga dama take yi ba?, yanxun fa Ammi sabo da ta kirani ban dauki waya bane kawai ranta ya ɓaci ta bar gida fa.
Ita ta gaya maka haka?, ninaso kaje da ita kaji menene matsalar.
Basai ta gaya min ba Ammi nasan halin ta, wlh tari wannan idan yarinyar nan tayi nasan me take nufi, ta zauna anan din Ni barin inje, mikewa yayi yana kokarin fita yake fadin Aunty na Saida safe.
Kawar dakai tayi kawai, shiko Modibo cike da tunani ya koma part din Safna yayin da Safna ta shiga cikin tsananin farin ciki.
Washegari da Safe Afnan ta kira Ammi, rufeta da fada Ammi tayi akan abun da ya faru jiya, cikin son fahimtar da Ammi tace wlh Ammi ba laifina bane, lokacin da tazo idon ta ya rufe in ma nace ta tafi ba gidan zatazo ba.
Taran numfashin ta Ammi tayi, meyasa bazaki kira Modibo ki gaya masa gata tazo gidan ki ba?
Ai nata kiran shi Ammi be dauki wayar ba.
Toh ai shikenan, ta gaya miki me ya bata mata rai??
Ammi Rahma fa kishin tsiya gare ta, kawai ta kira Hamma ne Aunty Safna ta dauka tana tambayan ta wacece, irin dai tana nunar mata be aje number ta cikin wayar ba, da dai ‘yan wasu abubuwa wadda nasan ko Hamma Modibo yayi toh tsokanarta yake yi.
Toh Akan me za’a tsokane ta?, mahaukaciya ce ita?
‘Yar dariya Afnan tayi tare da fadin, ” a’a Ammi
Toh akan me za’a dinga tsokanar ta?, idan fa mutum beson abu beso ne.
Ammi toh mutum bazai dan zolayi matar shi ba.
Ba neman zaman lafiya kuke ba kenan, ai akwai zolayar dazai mata tayi dariya amman ina amfanin zolayan da zaka saka mutum cikin bacin rai.
Ammi ta cika kishi ne fa, kuma wlh Hamma yana sonta sosai, yama fi son ta ko a idon sa ana ganewa.
Itama Rahma son sa take ai, soyayya ai itake kawo kishin, idan baki sani ba ki sani daga yau, kuma Ni dama can nabarwa zuciyata ne kawai, soyayyar da Modibo yakewa Rahma me girma ce na kara tabbatar da haka daren jiya, barin gaya muki wani abu da nasan baki sani ba, Modibo be taba ganin fuskan Rahma ba ya aurenta, kuma yayi alƙawarin zama da ita ko ayaya take tunda har ya kawo ta gabana amatayin matar shi, haka ita ma Rahma ga dukkan alama tana tsananin kaunar Modibo, wadda har tunanin ta ke bata Safna tai mata kutse, ko tantama banayi wannan tunanin tasa a ranta wadda ke hana mata sukuni, dan haka ba dan’uwan ki zaki dinga shigar mawa ba, itama ‘yar uwanki ce, kijawota a jiki, ki dinga bata shawarwari, koda ace ita ta fara auren Modibo duk iya tsananin kaunar da aikewa juna idan Allah ya kadarto zai kara aure zai yi, toh bare kuma wannan data same ta agidan, nima zan mata kema ki danga mata.
Jikin Afnan a sanyaye tace, ” haka ne Ammi insha Allahu zan yi hakan
Katse kiran sukayi yayi da Ammi ta mike ta dauki mayafi tana kokarin haɗawa take fadin, Rahma idan kin gama ki fito na shirya.
Fitowa tayi cikin dogowar riga wadda ta amshi jikin ta tare da mayafi.
Murmushi Ammi ta sakar mata tare da fadin kinyi kyau yariyana.
Sunkuyar dakai tayi sannan tai murmushi.
Fitowa sukayi ita da Ammi yayin da suka Samu Abdullahi yana goge motar Ammi.
Ammi ce ta shiga mazaunin driver ta zauna yayin da Unaisa ta zagaya ta shiga ta zauna, tafe suke Ammi najanta da hira, daman tuni suka saba da Unaisa saidai tun tarewan ta gidan Modibo take kasa sakewa da ita kamar da.
Har suka isa Baban asibitin da Yaddiko take hira Ammi kejenta dashi wani tai dariya wani ta bata amsa cikin yanayin jin kunya.
Ammice ta lura da yadda Rahma kejin kunyan ta dan haka tace, wai kunya ta kike ji ne Rahma? kisa ki jikin ke Ni kece ‘yata ba Modibo ba, duk abun da ya shige miki duhu ko Madibo yai miki bakiji dadi ba kizo ki gaya min nidake zamu warware ba tare da kowa yaji ba, kiyi kokari ki dinga boye dabowar ki kibar barin kowa na fahimta.
Cikin kwalkwal da ido tace nagode Ammi.
Bakomai dukkan ku nawa ne nidai burina ku zauna lafiya Allah yai maku albarka.
Labenta ta motsa tace Amin
Da haka suka isa cikin Babban asibitin da ya dikko ke kwance.
Saidai cike asibitin yake da wasu zafafan motoci Masu daukan hankali.
Daker Ammi ta samu inda ta raba motar ta sannan suka sauko, tafiya me nisa sukayi kafin suka iso, koda suka isa dakin da Yaddiko ke kwance cike yake makil da jama’a, baki kofar suka Samu Safna da Magaji tare da Muftahu.
Tuni Unaisa ta tsaya cak sabo da yadda taga mutane cike, jakarta tare da ta Ammi duk suna hannun ta.
Ammi ce tace lafiya me ake yi?
Safna ce tace wasu baki ne suka zo duba jikin Yaddiko.
Daga ina Ammi ta sake tambaya.
Muftahu ne yace, wata dai tsowar balarabiya ce naji hausan ta baya fita.
Magaji ne yai karaf yace, naji Modibo nacewa Babar Moh’d ce.
Ikon Allah Ammi ta fada tare da cigaba da fadin, Moh’d din fa?
Toh ai mu Ammi ba sanin su mukayi ba, sunan dai ciki suna da yawa.
Ikon Allah barin shiga inga idon tsohuwa Yasmeen Babban burin na ace sun taho da Moh’d domin ya shammace mu ya tafi kusan shekara ashirin ake nema BA LABARI, babu nashi labarin babu kuma na wani daga cikin dangin sa….
3 comments