GASAR ƊANGIWA
Advertisements
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Muna amfani da wannan dama, mu sanar da Matasan Marubuta, da ma wadanada ba su fara rubutu ba, amma suna sha’awar farawa. Ga dama ta sake samuwa gare su.
A wannan karon gasar Dangiwa ta mayar da hankalinta ne a kan matsalar “Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi”, da “Zaman Kashe Wando a Tsakanin Matasanmu”.
Advertisements
Kaso 70 zuwa 80 na dukkan mutanen Nijeriya matasa ne, bincike ya nuna cewa mafi gurman kalubalen da Nijeriya ke fuskanta shi ne yadda za ta sarrafa wannan baiwar da Allah ya ba ta ta yawan matasa masu jini a jika, domin su zama masu amfanar kawunansu, kuma masu amfanar ƙasa bakiɗaya.
Babu yanda za a yi matashi ya kasance mai amfanar kansa, bare ya amfani ƙasa a yayin da ya faɗa tu’ammali da kayan maye, ko ya kasance zauna gari banza.
Kasancewar Arc. Ahamed Musa Dangiwa mai kishin cigaban matasa da nema masu mafita, ya sa ya ce gasar mu ta bana ta bada ga matasa su fada wa duniya halin da suke ciki da kansu, ta hanyar baiwar rubutun zube.
Advertisements
Su faɗa mana matsalolinsu da hanyoyin da suke ganin idan an bi za a iya samun mafita, a cikin ƙirƙira da gwanancewar sarrafa harshe da alƙalami.
Matasa ‘yan shekara 18 zuwa 30 ne kawai aka ba wannan dama.
5 comments