Advertisements

Screenshot 20220208 122220 1

HATTARA MAZA, KADAN DAGA CIKIN TAUSAYIN ‘YA MACE GA IYAYEN TA

Posted by

HATTARA MAZA, KADAN DAGA CIKIN TAUSAYIN 'YA MACE GA IYAYEN TA

HATTARA MAZA, KADAN DAGA CIKIN TAUSAYIN ‘YA MACE GA IYAYEN TA.

Advertisements

Amarya da ango washegarin auren su ga yadda suka kullu alkawari a tsakaninsu cewa.

Munyi alkawari yau bazamu budewa kowa kofa ba, duk Wanda yazo kada mu bude har su gaji su koma, ciki kuwa harda iyayen mu.

Amarya ya alkawarin mu na cewa yau bazamu budewa kowa kofa ba?

Advertisements

Ango yananan daram, domin wannan rana zata kasance tarihi cikin ranakun auren mu.

Sai da suka hada hannayen su suka dauki alkawarin koda ya kasance iyayensu baza bude musu ba.

Tare suka shiga kitchen cikin kulawa da soyayya suke gudanar da ayyukansu sai su ka ji door ring.

Advertisements

Ango ya wuce gaba amarya na bin bayanshi su ka je wurin don ganin waye ke buga musu kofa?

Yana sanya idanunshi daidai wajen sai ya juyo ya ce da amarya mahaifana ne bari na bude musu.

Bude bakin Amarya keda wuya ta ce, ” ka manta alkawarinmu ne?”

Yadan sosu keya ya ce, ” ban manta ba, ya kenan, zamu barsu ne har su gaji da bugu su koma?”

Amarya ta ce abinda zamuyi kenan.

Sannan suka komo parlor ba tareda sun bude musu kofar ba.

Abinka da Iyaye, da sukaga basu bude ba sai suka juya gida a zatonsu Kodai basu tashi a bacci ba.

Can bayan sun gama komai suka baje a parlor suna jista juna cikin raha da annasuwa,sai su ka ji door ring.

Wannan karon ma ango a gaba amarya na biye dashi suka nufi wurin kofa.
Ya na dubawa kuwa ya juyo ya ce mahaifanki ne.

Cikin Sauri amarya ta karaso wajen kofar za ta bude, ango ya yi saurin rike mata hannu cikin rad’a ya ce kin manta alkawarinmu ne?

Amarya ta ce, ” ban manta ba,amma kuma gaskiya bazan iya barin iyayena su koma ba tareda na bude musu kofa ba.

Kafin ma ya ce wuni abu tuni ta bude kofa, cikin Fara’a ta tarbesu suka shigo ciki.

Haka yabi bayan su cikin sanyin jiki tareda amarya suka gama yi musu hidimar komai.

Bayan sun sanya musu Albarka suka tafi.

Bayan shekara daya sai gashi Allah ya Albarkace su da da namiji sun yi farin ciki sosai da samun wannan kyauta ranar suna mahaifin yaro ya yi dan karamin kwarya kwaryar walima.

Da ikon Allah suka kuma samun diya mace, wannan karo ba karamin farin ciki mahafin wannan yara ya shiga ba tunda jaririyar nan ta diro duniya.

kullum akan cinyarshi take wuni ko ‘yan barka saidai ankarbo ta suke samun damar ganinta.

Ranar suna kuwa liyafa da kyautukan da ya rabar ba’a magana.

Abin har ya sanya mahaifiyar yaran yin mamaki sosai da sosai, saboda tun haihuwar yarinyar zuwa suna abubuwan da yake har tsoro yake bata.

Cikin mamaki da al’ajabi ta tambayesa da cewa, my dear lokacin da na haifi yaro namiji banga ka yi Murna da farin ciki ba, kamar yadda kake nuna Murna da farin cikin samun diya mace.

duk da cewa, Ku maza akasari kunfi son ganin ana haifa muku yara maza.

Buden bakinshi ya ce, ina sonta ne saboda ita za ta budemun kofa idan na je gidanta.

Kin koyamun hankali kuma kin fahimtar da ni jinkai da tausayin da ke tattare da ɗiya mace.

Sai a wannan lokacin ta tuno da abin da ya faru a farkon ranakun amarcin su.

Mace kenan haka take, kowane lokaci zuciyar ta ya na ga mahaifan ta.

Ya ɗan Uwa, ‘Yar Uwa Ku tarbiyartar da ita, Ku bata ingataccen ilmi,domin itama diya mace ta na da hakki akan ka, na ilmintar da ita kamar yadda za ka baiwa ɗan ka namiji, sannan kaji ƙan iyayen ka, ka tausaya masu, domin kaima ka samu hakan daga gurin ƴaƴan

Uwa ita ce farkon makarantar yaran ta.

 

 

9 comments

  1. Pingback: phuket diving
  2. Pingback: balayeuse
  3. Pingback: Lowara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *