Advertisements

MIJI MARAINIYA PAGE 5

MIJI MARAINIYA PAGE 5

Posted by

MIJI MARAINIYA PAGE 5

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed

13-15

Advertisements

ummi kuka ta fara ta fita adakin da sauri ta shige nata dakin.

alhj ya kalli abduljalal yace akan wannan har kake zubar da hawayan ka, meyasa tunda kaji kana son ka tai maketa baka kirani awaya ka gaya min ba, kar ka kara zubar da hawayen ka, bama wannan yariyar ba duk wanda kake son ka tai maka ma kamin magana kabar biyewa ummin ka kaje ko.

jalal kwanciya ya da da yi ajikin daddy yana murmushi.
alhj ya sake cewa jalal zamu zauna tare da yarinyar nan zan sata makaranta zan riketa kamar yarda na hai fa idai har zakai farin ciki da hakan, amma da sharadi guda daya, sai nayi binkece na tabbatar maganar da yarinyar nan ta fada gaskiya ne.

Advertisements

Jalal tsuguna wa yayi yana ma alhj godiya tare da amicewa da maganar alhj.

har alhj ya fita ya dawo ,yace jalal raka yarinyar nan dakin kairat, kar na sake ganinta a barayin ka.
cikin sauri jalal ya amsa , haka yakai safna har dakin kairat ,kairat batayi bacci ba dan haka taji dadin ganin anty safna a dakinta.

bayan alhj ya shiga dakin ummi ya same ta tana zaune bakin gado tana share hawaye, kusa da ita yaje ya zauna ya dafata yace zaliha meye kuma abin kuka.
dole nayi kuka alhj naga kana neman ka tona min asiri agaban dana har da wata bare, wadda bamusan asalinta ba, kuma ni din da kake neman wulakantani ai a gaban iyaye na gaje ka aure ni, kuma duk gorin da zaka min nasan be wuce kace ka ganni ne lokacin da nake kora shanon mahaifina ruga ba har kaji kana sona , ai baza a hada da wannan banzan yarinyar ba, kuma ni abinda yafi damu na kar fa jalal yace son yarinyar nan yake dan nikam ko zanyi yawo tsirara bazan bari yaro ya aure taba.

alhj ya gama sauraran ummi cike da mamaki yace zaliha kina bani mamaki to meye a ciki dan yace yana son ta, ni dai na dauki alkawarin zan riketa kamar sauran yarana, kuma kema inason kireta kamar yar da kika haifa.

ummi tace naji zan riketa amman sai dai in jalal yayi min alkawarin ba aure tsakanin shi da ita.
Hmmm zaliha kinan dai akan bakan ki kenan yanzun kuma amiki magana kice ammiki gori, to shi jalal din da kikace sai yayi miki alkawari bazai ce zai aure ta ba, yasan gaibu ne, be saurari me zata sake cewa ba ya fita adakin afusace.

ummi kasa bacci tayi dan haka washe gari da safe ta nufi dakin jalal ta same shi kwance akan gado ya najin shigowan ta ya miki, kusa dashi taje ta zauna yace ummi dama yanzun nake shirin nazo na ganki nasan kina fushi dani ummi safna abin tausayi ne , tausayin ta ya kamani.
cikin dibara ummi tace na fahimceka jalal komai ya wuce safna zata zauna tare damu amman da sharadin nan gaba baza kace zaka aure taba

dariya sosai jalal keyi cikin dariyar yake fadin haba ummi dama akan haka kike tada hakalin ki , idai wannan ne ki kwantar da hakalin ki , ummi me zanyi da safna ga haddadu babys a gari haba ummi ni wlh ummi kin ma bani mamaki yama za ai haka ta faru.

ummi ji tayi zuciyar ta fes tundaga ranar ta fara jan safna ajikin ta, hakalin safna ya kwan ta ta koma makaranta ita da Kairat suke ta fiya .

akwana atashi gashi yau safna kusan shekaran ta daya da wani abu agidan jikin ta yayi kyau ya murje tayi fes in kasan safna ada kagan ta yanzun zaiyi wuya ka iya shai da ta, fari tayi sosai har nema take ta wuce ummi a fari ga gashin har gadon baya ga cikar halitta ummi ayanzun inta kalli safna har mamaki abin yake bata saika rantse yar wani hamshakin mai kudi ce.

shiko jalal rabon shi da ganin safna yama manta dan tunda ya lura ummi bata son ya rabeta ya rege shiga barayin su gaba daya saidai jefi jefi yakan shiga amman allah besa sunci karo da safna ba, sai dai yana samun sakon gai suwata agun kairat dan kulum sai taje dakin sa kuma tana shiga zata ce yaya anty safna na gai da kai hakan na mishi dadi.

itako ummi tunda ta lura safna kyakyawa ce murna ta kamata lallai ta samu jari dan haka tafara hada ta har ka da yayan manyan mutane dan acewan ummi safna matar manya ce.

yaran masu kudi ne ke zuwa gun safna duk da cewa SS 2 safna take ayanzun amma ita ummi barin ta kudi.

yauma kamar kulum safna na zaune ita dawani saurayin ta a harabar gidan ,halal ya faka motar sa bayan yafito yakalli gurin da su safna ke zaune, sultan ya gani zaune agefe sai dai yarinyar be gane ko wacece ba amma fah Allah yayi halitta agurin nan, azuciyar shi yake tunani me ya kawo sultan da budurwar sa tadi gidan su, inda wani shashi na zuciyar shi kecewa Ina ma ace ya mallake yarinyar nan, dawan nan tunani ya shiga gida, yana shiga ya samu ummi zaune a falo , zuwa yayi ya kwanta ajikin ta.
ummi tace yaya dai yaro, lfy naga jikin ka a sanyaye?
ummi wata yarinya nagani ita da sultan awaje.
murmushi ummi tayi tace jalal safna ce baka gane ba.
jalal tashi yayi ya zauna yace ummi kina nufin safna ce ke tadi da sultan?

ita ce mana ai safnar tamu ta waye sultan ya rikice akanta, ummi bata gama fadan maganar bakin taba taga jalal ya mike cikin fusatan da bata taba ganin shi cikin saba, itama mikewa tayi tana fadin me ya tada maka hankali ne jalal.
waje yayi da sauri ummi bayan sa tabi tana kiran jalal jalal.
amman ina besan ma tayi ba sai da ya isa gurin ya kare mata kallo riga da wando ne jikinta sun kamata sosai tabas kamanin ta basu bace masa ba, cikin fada yace da sultan malam tashi ka fita agidan nan.
sultan cike da mamaki yace ban gane na fitaba ai ba gurinka nazo ba.
eh koma gurin wa kazo karna kara ganin ka gidan nan, cikin tsawa yace ke tashi kishiga gida.
cikin sauri tamike zata bar wajen, sultan ya tashi ya rike safna yana fadin babu inda zata sai mungama maganar da muke.

duk abinda suke ummi na daga kofa tana kallon su, jalal ji yayi ya kara kulewa waton sultan ya saba rike safna kenan, jalal jiki na rawa ya fara kaiwa sultan naushi

105 comments

  1. Я конечно, прошу прощения, но этот ответ мне не подходит. Кто еще, что может подсказать?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *