Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 1

MIJIN MARAINIYA PAGE 1

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 1

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed📝

Bismillahir rahmanir rahim

Advertisements

1-3

Zaune take a dan ma tsakaicin gidan su tana ta faman share hawaye wata dattijuwan mata ce ta fito daga daki tana fadin , kin fara ko, dama ke idan tsohon munafunci ki ya tashi ba mutunci gareki ba, wlh uwarki ta bar miki mugun gado, ki zauna kiyi ta kuka salon iya ta ce ana miki wani abu, matsuwa tayi ta rike mata kunne tace ai baki ga komai ba safna sai rada na koreki gidan nan , zakiyi kuka, yadda uwar ki tasani kuka ta tura min bakin ciki kema sai na tura miki bakin cikin da zai kashe ki .

Safna taji zafin wannan ruko, fitsari ne yake bin kafafun ta, tace goggo dan allah kiyi hakuri , indai kuka ne na daina.
Kar ma ki daina dan jakar ubanki, tashi maza ki wanke kafafunki ki dauki rake , kuma karki dawo gidan nan sai ya kare.

Advertisements

Jiki na rawa safna ta mike ta dauki bukiti taja ruwa a rijiya ta shiga bayi, cikin sauri safna ke wanka dan gudun fadan goggo.

goggo na tsaye safna ta fito da bukitin wanka a hannun ta goggo ta bita da harara , da sauri tashiga dakin ma haifiyar ta, wanda a yanzun ita kadai take kwana acikin sa, cikin sauri ta jawo ledan kayan ta, ta fara cirowa tana dubawa duk tsun mukara ne , masu dan kyan goggo ta kwashe tayi kyauta dasu, haka dai ta dauki daya daga ciki ta saka, tadauki raken goggo ta kama hanya.

tafe take tana hada hanya domi ita bata iya tallah ba sai dai idan mutun ne yakira ta ,haka tai ta tafiya ko nera ba tayi ba, ta gaji ta koma gida.

goggo na zaune a tabarma ita da yaran ta guda biyu iro da salma, safna ta shigo , goggo ta mike yanzun nan dawo min da raken nan kikayi , iro tashi kaba yarinyar nan kashi rashin duka ke damun ta.

Kamar jira yake yamike da sauri ya fara kai mata duka daga kar she ma dukkan su suka taron mata wannan na duka wannan nayi , sai da suka ga bata iya motsi suka bar ta

WAIWAYE
malam musa mutumin kirki ne matan sa biyu goggo itace uwar gida, sai mahaifiyar safna wanda suke kira Inna, tunda malam musa ya auri goggo ta haifi iro bata kara haihuwa ba dan haka iya mahaifiyar malam musa ta matsamai ya kara aure, duk inda malam musa yaje neman aure ba a bashi saboda masifar matar shi, wata rana malam musa na cikin tafiya akan tsuhuwar mashin dinsa yaci karo da wata bafulatana batafi shekara sha biyar ba tana tafiya tana kuka, tsayawa yayi ya tam baye ta lfy take kuka, sai da ta share hawaye sannan tace wata yaya tace tayi aure a binni tunda mijin ya tafi da ita har yau bamu sake ganin ta ba, shine muka fito neman ta su baffah suka ce na jira su karkashin wata bishiya tunjiya har yanzun basu dawo ba, malam yace ina ne garinku , kame kame takama malam dai yagane bata san sunan garin su ba, goya ta yayi abayan mashin din sa dan su kara duba wajan ko iyayan ta sun dawo, suna zuwa suka duba babu kowa awajan , dan haka malam musa yace ma wani abukin sa dake zaune a waja bayanin cewa ko da iyayan ta sun dawo ya kawo su gidan shi.

malam musa gidan iya ya wuce da yar fillo saudatu dan yasan halin matar sa, iya ta kar beta hannu biyu tare da mamakin wauta irin na filani, sai da saudatu tayi shekara biyu awajan iya ba labarin iyayan ta ,dan haka iya ta matsawa malam musa ya auri saudatu, malam musa yabi umarnin ma haifiyar shi dan shima yafara tunanin haka.
bayan an daura musu aure da wata uku goggo ta sake haihuwan salma itako amarya saudatu sai da ta shekara biyu sannan ta haifi safna , saudatu tasha wahala a gun goggo dan ma tana samun kariya agun malam safna nada shekara sha hudu tafiya ta kama malam zuwa kauyen su iya dan kai masu ziyara, iya tace atafi da saudatu tunda bata taba zuwa ba.

lokacin safna nazuwa makarantar primary tana aji shidda dan haka suka barta gun goggo, bayan wani dan lokaci da tafiyan su labari ya same su, motar da suka shiga ta kone kurmus babu wanda yayi rai, haka su kai ta kuka a yanzun haka shekaran su daya da rasuwa inda goggo tahana safna makaranta sai tallan rake.

Abduljalal
wani matshin yaro ne me ji da kanshi daka ganshi kaga dan gata bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba, dogo ne sosai yanayin tsawan shi sai ka zaci ya wuce shekarun shi haka fari ne tas, bashi da yawan fara,a.

Idan kaga jalal na dariya to da ummin sa ne , ko kuma cikin abokan sa, zuwa yayi ya samu ummin sa zaune a falo, yaje ya fada jikin ta yana fadin ummi yinwa nake ji.

ummi tace jalal karfa ka karya ni, wai kai baka san ka girma bane.
haba ummi wanni girma nayi ne, kodan kinga kin samu wata.
tace ba haka bane jalal ya kamata ka fahimci cewa ka girma yanxun fan ba da bane, ga abinci nan kaci , karani gida hajiya sahura.
cokali daya ya kai bakin sa yace ummi na gaji zo ki bani abaki.
gargiza kai ummi tayi ta matso ta fara bashi abaki sai da ya koshi yace ummi bar shi haka na koshi.
sai da ummi ta shiga ta gama gyara wa sannan ta fito, ta samu jalal na zaune a falo kanan kaya ne a jikin shi yayi kyau sosai, idan kaga jalal da ummin sa sai ka rantse yayar sa ce, jalal ne ke jan motan ba, suna tafiya suna hira .
sunyi nisa sosai sun shiga unguwan su hajiya saratu abduljalal ya hango wata yarinya tana tafe tana kuka ga kuma rake akan ta, yace ummi ji wata yarinya yar karama an daura mata talla, yanzu dan Allah ummi wa zai sha wannan raken kofa kan kare shi ba,ayi ba.
ummi tace kai kake ganin haka jalal kazamai yan uwan ta zasu sha.
jalal na kawowa kusa da yarinyar ya tsaya ya kira ta da gudu ta karaso, yace me yasa meki kike kuka?
tace idan na koma gida raken nan be kare ba duka, duka za,ayi min, jalal ya tausaya mata ya kalli jikin ta yaga shedan bulala, yace ummi zan saya raken nan.

da sauri ummi tace amman dai ba a mota ta zaka zuba wannan kazamin raken ba.
yace sai ta bawa almajirai , ya sunan ki ya tam baye tace safna sai da ya maimaita sunan sannan yace raken na nawa ne?
tace nera dari, dari biyu ya ciro ya mika mata, tamiko hannu zata karba , ummi ta daka mata tsawa taja baya da sauri, jalal yace ummi me tayi ?
yaro ban yadda ku hada hannun da yarinyar nan ba ka aje mata akasa sai ta dauka

4 comments

  1. Pingback: ezh-ik.ru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *