Advertisements
💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝
Advertisements
35- 40
Ummi kwana tayi kuka ta shiga damuwa mutuka atake tunanin iyayan ta ya fado mata haka iyaye sukeji idan suga dan su zai shiga cikin wani hali, to yanzun wani hali iyayan ta suke ciki na rashin ta da sukayi, yau she rabon ta da ganin su, tun kusan shekara goma shatara da suka wuce lokacin jalal yana karami,
bazata manta ba tun lokacin da sukazo kawayen ta na gidan tace musu suyi sauri su koma gida kar kawayan ta sugan su tanan zuwa, suka tafi cikin bacin rai, suna fadin tunda baki son agan mu a matsayin iyayenki karki kara zuwa inda muke, taso washe gari tabisu tabasu hakuri amman tana cikin shirin tafiya saiga yayarta rabi tazo cikin kuka tana gaya mata cewa jiya dasu baffa suka zo gurinki sun taho da saudatu ba aganta ba taba ce, sanadi haka baffa yana cen ba lfy mama ma ba lfy ta cika ba, yan zon nazone kizo muje nemanta ko Allah zai sa adace,
ummi kin binta tayi ta dauko kudi ta mika mata tace kije ki duba ta nima ba lfyr gareni ba, in nashiga rana ciwona zai iya tashi kije duk halin da ake ciki kizo kisanar dani.
yaya rabi batayi musu ba ta wuce , haka yaya rabi tayi ta zaga gari har tsawon kwana uku tasake dawowa gurin ummi akarshe dai ummi koran kare ta mata tun daga ranar babu wanda ya sake zuwa gidan ayanzun haka ummi bata saniba ko anga saudatu ko ba,agan ta ba, amman ita tana ganin angan ta, haka ummi taita tunanin baya, tare da ganin wautan ta da ta bari har haka ya faru, yanzun ya zatayi ta shawo kan iyayen ta kilama alhakin iyayen tane gashi yanzun har ansa ranar auren jalal dan cikinta amman ba,ayi shawara da itaba, dan ba,a dauketa abakin komai ba alhj yanuna mata iyayen sa suna da mahim manci yaje yayi shawara dasu hakadai ummi taita tunani kafin gari ya waye idon ta yayi ja sunkun bura.
koda alhaji ya shiga dakin ummi da safe yasame ta cikin wannan hali yayi tunanin kin auren ne ya dame ta, bece komi akaiba yayi mata sallama ya fito.
Advertisements
alhj da jalal ne tafe amota alhji yace jalal kasan ina zamu ,jalal yace a,a
zan kaikane kaga wani abokin ka, tafiya sikayi sosai sannan suka isa wani gida dan madai daici mai kyau, suka shiga da sallama, wata tsohowa ya gani tana shara tana ganin alhaji ta sake tsin tsiyar cikin Fara,a , ta dauko tabarma ta fara kokarin shinfidawa sannu da zuwa alhaji bari na fadawa baban Ku, bayan wasu yan mituna baffa ya fito yana fadin sanu da zuwa kai dawa kake tafe yau kuma,
yace baffa jalal ne.
cikin bacin rai baffa yace ba munyi dakai daga mahaifiyar shi har shi bazaka nuna wa kowa nan ba.
alhaji yace baffa kayi hakuri ganinayi bayi da lefi kuma be dace muyi ta tafiya ahaka ba, yanzun gashi jalal har zaiyi aure, haka alhaji yayi ta jan hankalin baffa sannan ya kalli jalal yakama hannun shi yace kodan maihaifin ka ,bana kika ba, abduljalal maifinka yamin abinda ‘yata da haifa ta kasa yi min, mahaifiyar ka kunya ma takeji ace mune muka haifeta saboda tayi kudi baffa kasa magana yayi ya fashe da kuka mama ma tana daga gefe tana share hawaye.
jalal da be gane suba dan rabon shi dasu tun yana karami sai a magan ganun sune ya fahimci kakannin shine iyayan ummi, tausayin su ya kama shi daman ba wuyar kuka gareshi ba, tuni hawaye suka fara ambaliya afuskar shi ya kama hannun tsohon ya shiga bashi hakuri sai da yaga hankalin su ya kwanta sannan yace yauwa baffa ina anty saudatu yanzu? nan danan suka kara barkewa da sabon kuka suna bawa jalal lbrn batan saudatu haka sukai ta kuka har jalal , jalal ji yayi ya tsani ummin sa kwata kwata ya dade yana tambayan ta su sai tace yabar maganar bata so.
haka sukawa su baffa wuni sai yamma suka taho bayan sun cika su da tsara ba, saidai sunce su ba wanda zaizo biki daga barayin su, saidai wata rana yakawo musu amarya su gani jalal yanata basu hakuri,
amman suka ki.
******
shirye sheryen biki nata tafiya gidan hajiya kamar cenne gidan bikin acan ake shirya komai .
ummi bata kara tada zancen auren ba illah hankalinta ba akwance yake ba, kulum cikin kuka take, tarasa yaya zatayi ta dakatar da wannan auran.
Jalal kuwa ayanzun gani yake mahaifin shi beyi dacen mata ba yakamata daddy ya kara aure dan koshi da ana cenza uwa da ya cenza ummi dan ko ganinta bayasan yi.
ana jibi daurin aure kanwar alhaji anty nusaiba da matar kanin alhaji hajiya fatima da wasu mata su hudu yan uwan hajiya, suka faka faka jibge giyar motan su a haraban gidan alhaji, rabon su da zuwa gidan sun dade, wata motar na biye da nasu,
direban motocin suka fara fito da akwatuna masu kyau daga cikin motar sukuwa matan tuni suka shiga gidan.
sunata sallama a falon har suka gaji ba,a amsa musuba suka nemi guri suka zauna , bayan anshigo da akwatunan ne , aka fara shigo da kayan abinci, anty nusaiba ce take nuna inda za,a ajiye komai, ummi dake kwance tana kuka taji mutsi yayi yawa ta share hawayen ta tafito, mutane ta gani cike da falon, nusaiba kawai ta shaida.
nusaiba ta fara mata bayani anty munshigo munata sallama gidan shiru.
eh wlh kaina ke cewo nadan kwanta.
nusaiba tace gakayan safna nan mun kawo ki duba ki gani.
ummi ta zauna suka fara budewa lallai alhaji ya kashe kudi wannan uban kayan duk na safna ne , aikowa safna bazata sasu ita daya ba,
bayan sun maida akwatin sun rufe, anty nusaiba tace mufa munzo kenan sai bayan baki.
ummi tayi yake tace ai yakamata tunda kune kirjin biki.
hajiya fatima tace ina amaryar tamu ko taje kunshi ne?
sai alokacin ummi ta tuna da wata safna, tace anya kuwa inajin tana daki.
anty nusaiba tamike tashiga dakin ta hango safna makure agado ta xata bacci take sai da ta taba ta taga ashe kuka takeyi.
itako safna ta zata ummi ce dan haka ta mike afirgece, da sauri anty nusaiba ta riketa suka kalli juna, nusaiba tace safna me yasame ki kike kuka, ko baki son auren ne? girgiza kai tayi.
to me yake damunki?
koda safna bata san anty nusaiba saita tsinci kanta da cewa tunanin iyayena nakeyi da kakata,
nusaiba ta tausaya mata tace safna ardua zakiyi musu ba kuka ba, tana buye hawayen ta sake cewa me yasa bakiyi kunshi ba, zo naga kan ki, ta bude kan taga tsohon kitsone, ta kwatar da safna akan cinyar ta tafara warware mata kitson , haye na zuba afuskar ta 😭😭😭
07014197556✍
5 comments