Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 12

MIJIN MARAINIYA PAGE 12

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 12

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

 

Story
&
Written
Fadeela Lamido
MmnyazeedðŸ―ņ‡Š

Advertisements

46-50

Nusaiba bata ci gaba da sauraren suba ta wuce dakin safna, anan ta samu su hajiya fatima, tace ya naga kun dawo nan kuma. hajiya fatima tace to me gidan tace mushiga daga ciki zatayi baki, shiyasa muka yo nan.

anty nusaiba nisawa tayi tace anya kuwa zamu zauna agidan nan har agama biki, kodai zamu koma gidan hajiya ne muyi namu acen, dan nifa gaskiya bazan dauki wula kanciba .
Hajiya fatima tace nima nayi tunanin haka amman saina tuna hajiya fah da zamu taho tana ta gargadin kar muce zamuyi fushi muyi hakuri da duk abin da muka tarar dan haka gara mu hakura mu zauna ko dan kan ran hajiya ya baci.
nusaiba tace bari na kira hajiya muyi shawara, ta daga waya ta kira hajiya ta gaya mata halin da ake ciki har fadan da alhaji yayi mata, ran hajiya ya baci tace kark taho ku zauna nima gobe zan taho da Jama,a ta,

Advertisements

washe gari kuwa saiga hajiya ta dira agidan dan nata, da misalin 10:12 am rabonta da gidan tunda tazo barkan abduljalal.
jalal na zaune shida wasu abokan sa, ya hango hajiya na fitowa daga muta da sauri ya karaso yana cewa hajiya lfy kuwa?
hajiya na murmushi tace nazo bikin mijina ne.
Jalal yace hajiya kodan kishin nan bakiyi ne kama hannuta yayi, ya waiga gurin da abokan sa suke yace faisal kuzo ga amaryar ta iso, dariya sukayi suka matsu suka gaida hajiya sannan sufara diban kayan da sukazo dasu suna shiga dashi cikin gida.

ummi na zaune ta fara ganin ana shigo da wasu kaya tace wannan kayan fa daga ina?
daidai lokacin jalal yashigo yana rike da hannun Hajiya, ummi ta mike tana fadin sannu da zuwa, hajiya ta amsa Mata ba yabo ba fallasa, sannan tace ina su nusaiba ban gansu afalon ba, ko basukai su zauna anan bane.
ummi tace a,a ba haka bane naga dai sun fita tun safe, ina sukaje?
basu gayamin inda za suje ba.
hajiya ta sake cewa me gidan fa baya nanne, ummi tace yana ciki bari na kira shi
da saurin shi ya fito yana fadin hajiya da kanki, Allah yasa dai lfy, lfy nazo ne ayi komai akan idona dan ni bana son tashin hankali, nidai na gargadi iya laina kaima inason ka gargadi matar ka bama son tashin hakali.
alhaji yace hajiya ki kwantar da hankalin ki babu wani abunda zai baru.
tace toh nima ai nafi son haka.
wayar alhaji ce tayi kara ya dauka bayan ya sauke wayar yace ina nusaiba cikin sauri ummi tace bata nan ta fita.
alhji yace kash gashi kuma kamafani da zasu kawa kayan safna sun isa gidan.
Hajiya tace ka Kira ta awaya mana.
kafin hajiya ta rufe baki, ummi tace alhji key na wajan tane.
a,a gashi agurina nusaiba tace ya kamata mace ta tsaya agurin.
ummi tace hakane alhji toni ai da nasan gidan da naje, alhji dadi yaji sosai yace ai jalal nannan awaje sai ya kaiki.
hajiya taso ta hana sai kuma taga karta cika takura masu dan haka tayi shiru.
itako ummi dadi taji dan dama jira take afadi gidan da jalal zaizauna su cika kudurin su ita da kawar ta madina.

bayan sun dauki hanya dukkan su gaba suka zauna ummi ta daga waya zuwa cen tace dona madina tama bayani ko ? , jalal beji amsan me aka bataba, ta kashe wayar tana murmushi Kara kiran wayar tayi tace madina har yanzun baku zoba, nagaji da jira gani ma zantafi gidan danki za a zuba kaya agidan , bayan ummi ta gama waya jalal yace ummi naga kina shashshare bikin nan ne.
tace ba haka bane jalal aini babu wadda yakaini farin ciki ayanzun na fahimci kana son safna da yawa dan haka nima na fara jin Ina sonta , saidai abu daya yake damu na , ban so ka aure yariyar da sultan yayi soyayya da ita ba, saboda sultan fa dan duniya ne.
Jalal be gane inda ummi ta dosaba yace ummi ki daina tuna wannan yariga ya wuce kuma sultan ai babu abinda ya isa yayi min, nidai burina kawai adaura auren.

ummi ma ta gane jalal be fahimce taba, da wannan tunani suka isa gidan, kan kace meye har angama gyara gidan, ummi tsayawa tayi tana kallon dukiyar da aka zuba agidan, alhaji ya kashe kudi saikace kairat zai aurar, badan madina tace tabi komai ahankali ba toh da yau saisun kwashi rigima da alhaji, haka suka kamo hanya ita da jalal amota jalal sai santin gidan yake.
gani inda yake ta murna ummi tace gaskiya jalal guri yayi kyau.
cikin murmushi ya waigo yace ummi ai bakiga kyauba sai safna ta shiga gidan, zakiga yadda zai kara haske.
kulewa tayi sosai amman bata bari ya gane ba tayi mai murmushi kawai.
Jalal kuwa dadi yaji ummi ta fara son safna tuni ya nemi haushin ta da yakeji da ya rasa, dan haka yashiga zuba mata shagwaba, ummi kinsan menene?
tace a,a yaro sai ka fada.
yace safna fah sai kin dan mata fada bata sakin jikinta dani, kamar ma tsorona takeji kuma dacen ba haka take minba, cikin shagwaba ya fadi maganar.

ummi daurewa tayi tayi murmushi tace jalal manya, kabari mana adaura aure duk zata Bari
da haka suka isa gida lakacin yamma tayi sosai, tana shiga falon sukayi ido hudu da safna tana kusa da hajiya a zaune ganin tayi ta kara kyau da sheki gawani zanen filawa wadan tunda take zuwa bikin yaran kawayen ta bata taba ganin wada yakwai haduwar wannan ba, sai satar kallota take , tare da kara jin haushin anty nusaiba tasan tayi ne dan jalal ya rikice, bayan ta gaida hajiya ta shige dakin ta.
hajiya ta kalli safna tace me yasa baki gaishe da ummin ku ba, maza ki bita daki ki gaida ta.
safna tashi ga da sallama ummi ta dago ta kalle ta, tace yaushe kuka dowa?
tace bamu dade da shigowa ba.
tasake cewa jalal yasan kundawo? nima basan ko yasani ba, tabe baki tayi tace fita kibani waje.

da daddare gidan ya kaceme gidan biki sosai sai haya niya ake aharabar gidan kuwa su jalal ne da abokan sa sai hayaniya sukeyi.
zuwa cen kawayen ummi suka fara shigowa wannan karon basu tsaya a falo ba barayin ummi suka shiga, zuwa cen suka saki sauti.

bayan ansaka safna alalle tana ta kuka yau itace za,ama aure ba dangin ta ko guda daya ita da zata samo ko goggo ce tagani agurin bikin nan da zatayi farin ciki da haka da ace babu kowa nata kasa bacci tayi sai juye take babu wadda tafi fado mata arai kamar iya taso Allah ya bar mata iya, haka taita share hawaye dan bata son anty nusaiba ta juwota, daga cen ta fara jiyo muryar alhji yana fadin innalillahi wa,ina ilaihir raju,un sai maimaitawa yakeyi mikewa tayi ta zauna ,tana kallon su hajiya suka fita akabarta ita kaidai adakin, dan haka tabiyo bayan su, gani tayi duk sun tsaya sunyi cirko cirko, alhaji ko sai share zuba ya keyi jalal na gefe daga shi sai gajeren wando, ummi kuwa sai rusa kuka take, cikin rudu safna tace me yafaru?
anty nusaiba tace karku gaya mata saida safe.
ummi tace ai gara agaya mata tunda kowa yasani, safna gidan da zaku zauna ya kone babu abinda aka dauka acikin sa.
safna neman kujera tayi ta zauna ta rufe ido bata sam ma me zata ceba.
jalal kuwa kansa akasa yake, yaki dagowa.
alhji yace bakomai kowa ya koma ya kwata saida safe Allah yasa haka shine mafi alheri.
ummi tace ai alhji bamuga ta barciba munfah gaiyata muta ne gashi gobe ne daurin aure, yaka mata asan abinyi, ni ina ganin kawai adaga bikin kawai hankali kwance.
bata gama rufe baki ba jalal yace ni gaskiya ban yaddaba ummi, ni dai kawai ayi.
cikin fada alhaji yace kai jalal baka da kunya ko ya manya suna magana zaka saka baki, ai biki yazama dole adaga shi, wuce kaba mutane waje.
da sauri yabar wajen ya shige dakin shi ya bogo kofar.
hajiya tace toh yanzun kayanke hukunci ne kabamu umarni mu watse koko shawara kake nema.
sai lokacin ya tuna mahaifiyar shifa tana wajen dan haka yace hajiya kiyi hakuri nayi kuskure, shawara nake nema yanzun yaya kamata ayi.
hajiya tace toh nidai ban yadda adaga ba kowa yaci gaba da abinda yake biki nanan babu fashi

07014197556…..✍