Advertisements
Advertisements
Advertisements
💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
Story
&
writte by
Fadeela Lamido
Mmn yazeed📝
61-63
Alhaji ya kalli jalal yace, duba nan jalal tashi ka zauna, kasan yazun yaya za’ayi, tashi zakayi kaje ka lallashi matar ka, koma me ka mata kaje ka bata hakuri zata saurare ka.
Shiru yayi ya ya mutsa fuska, ni dai daddy ka tai make ni ka bata hakuri.
Alhaji juyawa yayi ya kalli ummi yace, zaliha ke kika lalata yaron nan shagwaba tama sa yawa kuma yanzun ke kin zame kinbar ni dashi.
Dariya tayi wani irin na zame nima fah yana min.
Alhaji juya ya kalli jalal ya kwashi da dariya yace zaliha maza Kira min safna naga abin babba ne .
Ummi waya ta daga ta kira safna daure wa kawai take tana yashe baki dan bin shawarar kawar ta madina.
Safna tashigo tare da sallah ma da sauri ummi tace zonan ‘yata safna ta karasa kusa da ummi, ummi tasa hannuta ta jawota ta daurata akan cinyar ta , tace safna me jalal yayi miki da zafi haka ne ?
Ummi ni baiyin min komai ba.
Jalal yace a,a safna namiki laifi kedai kawai bazaki fada bane.
Alhaji yace zonan safna ,sauka tayi ta koma gaban alhaji kusa da jalal ta zauna.
yace koma me jalal yayi miki kiyi hakuri ki yafe mishi kinji, yasan cewa yayi laifi kiji ko?
Daga kai tayi ,alhaji yace yauwa safna haka akeso jalal kuwa bin safna kawai yake da kallo
Alhaji yace to jalal tashi ka dauki matar ku kutafi shi besan cewa ummi ta raba musu daki ba.
Bayan sun fita ummi nata sauri tabi bayan su alhaji ya dakatar da ita.
zaliha ina da magana dake , ta koma ta zauna .
Yace kina zuwa gurin su baffa kuwa?
A,a kwana ki naje akace sun tashi alhaji wani abune ya faru?
A,a ba abinda ya faru, amman me yasa baki neme inda suke ba .
Mike wa tayi zata bar wajan.
alhaji yace saboda basu da kudi ko.
komawa tayi ta zauna tace aini dama tunda naga yan uwan ka sunzu bikin nan nasan sai su kulla min wani sharrin.
alhaji yace basu suka fada ba baffa da kanshi ya fada haka.
mikewa tayi alhaji aina kaga baffa?
aini tunni nasan inda suke tun bayan koran ron su da kikayi kokaci bananan baya sati biyu na dawo tun kafin nashigo gida jalal ya gaya min baffa yazo kin kore su, abin ya bani mamaki amman bayi miki magana ba na nufi gidan nasa me su cikin ma wuyacin hali bafffa ba lfy mama haka , sai yaya rabi ce akan su itama kuka take.anan take gaya min saudatu ta bata wanda har yau ba,a ganta ba.
bayan nakai su asibiti kwan su uku aka sallame su.
tunda ranar nakai su wani gida na dana saya baffa kin shiga gidan yayi, wai bai son abinda zai sake hadaki dashi da ke👉🏻 dan haka namai alkawarin bazan gaya miki inda suke ba, san nan ya yarda.
duk wata nake zuwa ina kai musu kayan abin ci, in takaice miki har daurin auran jalal baffa yazo, inata jira inga ranar da hakalin ki zai karka gare su amman sai naji shiru kamar an shuka dusa dan haka naga innabar ki ahaka banyi miki adalci ba, amfanin zaman tare kenan in kaga wanda yake kusa dakai zai bata kasa shi ahanya dan haka idai bakibi iyayen ki ba toh matakin da zan dauka bazai yi miki dadi ba.
********
kafin ya gama magana hawaye ya wanke wa ummi fusku yanzun dama tuntuni ba,aga saudatu ba, amman basu nemi ni ba lalai su bafffa suyi matukar fushi dani.
tsuguna wa tayi ta fara wa alhaji magiyar ya rakata ta nemi gafarar su.
alhaji yace indai nine bazan taba kaiki ba kije ki nema da kan ki.
shiko jalal bayan sun fita dakin sa ya nufa da safna ya kara kwasan gara bayan tayi wanka jalal ya shiga , kamar jira take tana ganin ya shiga wanka tamike ta leko bataga kowa ba ahanyar ta fito saf saf ta shige dakin su.
jalal ya fito bega safna ba dan haka yana saka kaya ya fito, daidai lokacin ummi ta leka dakin dakin safna tagani ko jalal ya wuce da da ita dakin sa.
tana ganin safna hankalin ta ya kwanta juyawa tayi dai lokacin suka ci karo da ummi.
ganin ummi yayi abirkice yace ummi lfy kuwa?
wucewa tayi zuwa dakin ta ta fada gado tasaki kuka, jalal ya shigo dakin yace ummi me ya faru ne.
mikiwa tayi cikin kuka ta kwashe duk abinda yake faruwa ta gaya mishi.
dadi ya kama jalal Allah ya karbi Andu,ar shi ummi ta fara tunanin iyayen ta.
yace ummi ki kwatar da hankalin ki ,ni nasan gidan zan rakaki.
ummi cikin sauri ta dauki gyale tace muje jalal.
jalal yace ummi ki bari sai gobe mana.
eh ai kana tare da uwarka da ubanka dole kace na bari sai gobe.
Jalal yace Allah ya baki hakuri ummi muje, sun fito kenan saiga safna da kairat zasu fita jalal yace ina zaku ?
kairat tace waje zamu muga gari safna ko shiru tayi jalal yace koma gida.
kairat kuka ta fara toh ni ummi zanbi.
ummi tace zo muje yar auta ta.
safna na kallo suka shiga mota sai daga musu hannu take.
bayan sun isa jalal ne ya fara shiga gidan sunata murna baffa har yana tam bayan jalal ya baka taho da amaryar ba, ko kana tsoron karta ganin tace ni take so.
jalal dariya yayi yace baffa ni da baki ne fah, nabar su a mota.
a,a banda abinka ya zaka baro so akofar gida jekace su shugo.
waya ya dauka yace shi go.
shigowa tayi da sallama rike da hannun kairat idon ta hawaye ne kawai ke zuba.
baffa ya mike ya nuna ummi yace zaliha mama dake tsugune tana zubawa jalal abinci ta sake kwanan ta dau ko itacen dake cikin murhun ta fito tana fadin ina zalihar take.
baffa ya nuna zaliha yace kinzo ki koremu ne daga gidan da mijinki ya bamu?
tsugu nawa tayi ta fashe da kuka tana fadin baffa nazo neman gafarar kune dan Allah ku yafe min.
bata rufe baki ba ta fara jin saukan itace ajikin ta.
jalal saifaman ba baffa hakuri ya keyi, yaju ya yaga anata jabgar ummi mikewa yayi yazo ya karbi icen yana bawa mama hakuyi.
baffa yace ta fita karta kara nufo inda muke, shi ya dade da cireta acikin ‘ya’yan shi.
wani makocin baffa ne yaji hayaniya tayi yawa ya zagayo.
me yake faruwa ne?
baffa ne ya fara gayawa makocin shi, malam buba yace kinyi kuskure yarinya, nan ya shiga bawa baffa hakuri amman baffa ya kekashe kasa yaki hakura ummi sai man share hawaye take, ahankali mutane sai taruwa suke anyi anyi su hakura suki.
jalal ya tsuguna ya rike kafar bafffa yana rokon shi.
baffa yace mike abduljalal idan ina kallon ka gani nake kamar mahaifin ka ne zan yafewa mahaifiyar ka amman da sharadi.
sharadin kuwa shine karta kara zuwa inda nake har sai ta nemo min ‘yata saudatu.
ummi saka hannu tayi aka, yanzun a ina zata nemo wadda tayi wajen shekara 20 da bata
One comment