Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 17

MIJIN MARAINIYA PAGE 17

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 17

 

Advertisements

๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜

 

Story
&
written by
Fadeela lamido
Mmn yazeed๐Ÿ“

Advertisements

 

67-69

Sai alukacin jalal ya kalli kayan sa sun yamutse amman saiya dake ya kalli jikin shi yace muje kawai ummi.

Advertisements

Wlh bazaka fita a haka ba ,kai kadai ne me mata, ko akan ka aka fara, haka kaga sauran maza suna fita?

shiru yayi mata bece komai ba.
suna cikin haka alhaji ya fito yace me yayi ne naji kamar kina mai fada?

cinki daure fuska tace jifah kayan shi wai haka zai fita.
alhaji yace me kayan nasa sukayi?
jifa inda kayan shi suka ya mutse sai kace akan shi aka fara aure.
alhaji hada rai yayi yace jalal jaka abin ka.
da sauri jalal ya juya ya shiga dakin sa. alhaji ya kalli ummin yace wai zaliha ko hauka za kiyi ne, ina ruwan ki da kayan sa, irin wannan ai sai ya raina ki, yaya mutun da matar sa zaki saka masa ido.
alhaji bazance sa ido bane maganar gaskiya ne, ai wannan rashin kunya ce.
toh shikenan nasan maganin abin ai in da suna gidan sune baza ki saka musu ido ba, haba na menene zakibi kita kurawa yara wucewa yayi ya fita ya ta fada.

bayan jalal ya canza kaya ya fito suka dau hanya ahanya ne ummi ta kalli jalal taga fuskar shi murtuk tace jalal fushi ka keyi dan na gaya maka gaskiya .
a,a ummi ni ba fushi nake ba.
ta sake cewa jalal ni bawai ina kinka da safna bane, abinda yake damuna shine sultan ya taba neman safna kuma kasan sultan ba irin yan iskan da be nema ba, ina jin tsora kar ace ya shafa mata ciwon zamani shiya sa nake tsoron karka kusan ce ta, ta shafa maka.

jalal yace ummi dan Allah karki kara irin wannan maganar ba komai atsakanin su kuma lfyr ta kalau.

kar kace zaka shede ta dan ni na taba ganin su da ido na .
jalal yace dan Allah ummi kibar maganan nan ni bana so.
ai ina gaya maka ne dan ka kiyaye.
toh zan kiyaye eh ummi naji zan kiyaye.
ganin da tayi kamar ya shiga damuwa yasa ta murna tafara nasara.
shikuwa jalal yasan cewa shi ya fara bude matar sa a leda, amman zuciyar shi ta fara raya mishi anya kuwa sultan be lalube safna ba kuwa , dan haka ya kosa ya koma gida ya tuhu meta.

da haka suka isa kofar gidan yaya rabi , ummi ce kadai ta shiga, jalal ya tsaya a mota.

ummi ta shiga tare da sallama yaya rabi ta fito daga cikin dakin ta sukayi ido biyu da ummi.
ta fara fadin zaliha kodai gizo idona kemin.
ummi tace ba gizo bane yaya rabi nice.
aguje yaya rabi ta fada jikin ummi tana kuka, ummi ma kuka ta saka , haka sukai tayi babu mai lallashin su .
bayan sun natsu suka shiga tattauna wa akan halin da suke ciki, ummi ta kwashi duk yadda sukayi da baffa ta gayawa yaya rabi.
yaya rabi tace banga lefin baffa ba zaliha .
ummi tace nima banga lefin saba amman matakin da ya dauka yayi tsauri yanzun a ina zan nemo saudatu, kawai ina ganin bazai yafe min bane shiyasa yace saina nemo ta.
toh nidai abinda nake gani zaliha ki jaraba ki gani ko Allah zaisa adace.
toh ni yanzun ta ina zan fara, alhaji yace min wai agidin wata bishiya aka bar ta ko?
dan Allah ina son ki tambaye min su baffa wacce bishiya ce kuma awace unguwa ne.
murmushin takaici tayi sannan tace zaliha kenan ko kisan saida nayi shekara biyar ina zuwa gidin bishiyar ina zama ko Allah zai sa na ganta amman ko me kama da ita ban gani ba.
ummi nisawa tayi sannan tace kuma kin tamya agurin?
tambaya kuma ai sai da na zama kamar mahaukaciya duk wanda nagani saina tambaya.
ummi shiru tayi sannan tace yaya rabi banida saura wata dama ila kawai ki gayamin gurin inje in jaraba ingani

yaya rabi tace kusa da unguwar ku ana cewa unguwar โ€˜yan mangorori, akwai wata katuwar bishiya agurin ada amman ayanzun babu bishiyar amman akwai wata tsohowa tana kasa kayan miya.

tuni ummi ta gane kwatance domin tasan unguwar sosai sai dai unguwar talakawa ne.
jalal ne ya fara kiran ummi awaya tace au na manta nabar jalal awaje yaya rabi tace shine ya tsaya awaje sai kace bako.

mikiwa sukayi suka fito tare, jalal na zaune idon nan jawar ya kosa ya koma gida ya tambaye safna ko sultan ya taba taba mata jiki.

bayan sun gaisa da jalal suka dau hanya jalal yaso su wuce gida amman ummi tace sai sun biya yan mangorori.

suna isa ummi ta sauka ta isa gurin tsohuwa me kayan miya bayan ta gaida ta , tace dan Allah mama tambaya nake?
yar tsoha cikin murna tace Allah yasa na sani hajiya.
dan Allah mama shekaran ki nawa agarin nan?
ai ni hajiya agarin nan aka haife ni ban taba zuwa ko ina ba.
nan ummi tashiga karanto mata tambayar ta.
tsohuwa tsayawa tayi tayi shiru zuwa cen tace, nidai kamar nasan lbrn nan amman na manta tasake yin shiru
ummi kuka tashiga yi tana fadi mama ki nutsu ki tuna ahankali, ko kudi kike so zan biya ko nawa ne kowa.
tsohowa tace yarinya ki kwatar da hankalin ki insha allahu zan bincika miki kinga yanzun zan tattara kaya na gobe ki dawa kin ga gidana cen koda baki ganni anan ba sai ki shiga ciki.
haka ummi ta aje ma tsohuwa kudi masu yawa ta wuce.

Suna komawa gida jalal ya fita amotar da sauri yariga ummi shiga gida , ummi binshi tayi da kallo tazata maganar da tagaya mishi ne yake damun shi , shikuwa jalal cewan da tayi ta taba ganni su da idon ta shine abinda yake tayar mai da hankali.

yana shiga falo yaga safna kwance tana bacci besan lokacin da ya finciko taba yafara janta yana kokarin shiga dakisa da ita.
safna cikin firgita ta fara ihu dai dai lokacin ummi ta shigo , hango jalal tayi yana jan safna idon shi arufe.
ummi tarogo da gudo tana fadin jalal metayi maka.
ai jalal babu magana jan safna kawai ya keyi
[4:35PM, 12/9/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜

 

Story
&
written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed๐Ÿ“

70-72

Daker ummi ta kwaci safna ahannun jalal ta kaita dakin su .
da sauri ta juya ta nufi dakin jalal dan tana tsoron kar yagayawa alhaji dan idan yaji maganar nan kashinta ya bushi.
tana shiga ta same shi sai faman share zufa yake tace jalal kardai maganar da mukayi dazun ce tasa ka shiga cikin wannan halin ?

jalal yace ummi kefa kikace kin taba ganin su da idon ki

a,a jalal bahaka na ke nufi ba, karufa min asiri kar alhaji yaji wannan maganar, nidai nace kayi hakuri kabari ayi mata test , kuma ko safnan ban ce kagayawa waba bare baban ka.

toh ummi ai bai kamata ayi shiro ba ya kamata kowa yasani.
nidai nace karka gayawa kowa, kai wlh duk kabi karice akan safna.
jalal kallon ummi yayi cike da ta kaici wato haryan zun tana nan akan bakan ta saita raba mu , wai ita ummi bazata gyara halin taba ne, tana cikin wannan halin baza ji da abin da yake damun taba.
yace shike nan ya wuce, ummi mikewa tayi ta fita, dasauri jalal ya dauki wayar shi yakira safna bata dauka ba saida yakira sau biyar yaji shiru ya tabbatar safna fushi tayi mikewa yayi yaje kofar dakin su yaji ta kulle, yasan ko ya buga ba budewa zata yi ba haka ya koma dakin sa.

washegari 8:00 jalal ya fito cikin shiri shi na tafiya office bayan yayi wa ummi sallama ya leka dakin safna har yan zun kofar akule take, ya juya ya fita.

ummi ma guri 12:00 ta bar gida ta nufi yan mangorori, sai safna kawai ta rage agidan, dan kairat ma tana makaranta.
safna na zaune ita daya agidan dan me aikin gidan ma tayi tafiya ga yunwa ta dame ta rabonta da abinci tun jiya da rana gashi kuma yau hakanan ta tashi da son cin zogale .

mikewa tayi ta shiga kitchen ta duba bataga wani abu da ya bata Sha,aw ba bude wata roba tayi nan taci karo da garin daddawa murna ce ta kamata tun daga nan tafara lasa tana lumshe ido, da sauri ta daura miyar daddawa tana gamawa tayi tuwo ta dai dai cikin ta tafito falo ta fara ci ,saiga kairat ta dawo makaranta, zuwa tayi ta zauna zata saka hannu dan sun saba cin abinci tare.
kairat tace anty wannan miyar meye na ganshi baki.
safna tace kedai in zakici kici miyar daddawa ce.
da sauri tajanye hannun ta tana toshe hanci anty dama anayi miyar daddawa ne.
safna tace ke nidai kawai yunwa nakeji ,bayan ta gama cin towan ta dauki miyar ta fara sha kenan saiga jalal ya shigo.

safna naganin jalal ta mike da miyarta ahannun ta zata bar wajen.
da sauri jalal yasha gaban ta ya tsareta da ido sai kallonta yake, itako kasa tayi da kai.

jalal yace miye wannan kike sha?
banza tayi dashi tana kokarin aje miyar dan ta samo daman guduwa tana aje miyar kuwa ta mamaye shi ta sheka aguje ta shige daki.
jalal binta yayi da kallo yasan safna nashiga rufewa zatayi dan haka bebi taba.
tsugunawa yayi ya dauki miyar ya koma ya zauna yalli kairat dake kwance akujera yace kairat faten meye wannan?

kairata ta kwashe da dariya tace yaya ba fate bane , miyar daddawa ce.

miyar daddawa kuma a ina ta samo shi?
ita tayi da kan ta tace yinwa takeji
yunwa babu kayan abinci ne a kitchen din sai daddawa, mikewa yayi yace kairat tashi kije ki zubar da shi.

ummi bata dawo ba sai yamma jalal na zaune aharabar gidan yana shan iska , ummi ta nufoshi tun daga nesa jalal ya fahin ci babu nasara.
bayan ta zauna jalal yace ummi akwai nasara kuwa?

ummi tace ba wata nasara jalal , yau nasha bakar wahala jalal , rabon da na wahala haka na manta, munyi yawo nida tsohowar nan har mun gaji amman bamu dace ba, duk gidan wani tsoho da yake garin muje amman babu lbrn ta, ummi ta fara share hawaye jalal ina cikin wani hali banda me tausaya min duk duniyar nan sai kai, sai kuma yaya rabi dubi duk abin da na mata bata juya min baya ba, amman dubi alhaji yana shirin ya juya min baya, babu ruwan shi da damuwa ta kamar ma dadi yakeji.

ummi ki daina fadin haka kuma ki kwatar da hankalin ki insha allahu indai tana raye za,aganta
ummi fashewa tayi da kuka to yanzo jalal inta mutu ne yaya zanyi kenan su baffa bazasu yafe min ba.

jalal yace ummi insha allahu zasu yafe mike amman ummi kunje har gidan me unguwa?
ummi tace a,a
Jalal yace ummi ni gobe zanje na bin cika.

washe gari da wuri jalal ya fito yasamu ummi afalo kamar jira take ya fito , mikewa tayi tace jalal mutafi.
jalal yace a,a ummi ki zauna agida ki huta.

ummi tace nidai kawai mutafi haka suka tafi badan ran jalal yaso.

suna zuwa gidan me unguwa suka tambaya aka nuna musu bayan sun isa sun tarar da wajen cike da mutane dukkan su suka sakko suka isa gurin tare da sallama, ummi ce tayi bayanin abin dake tafe da su.

me unguwa ya nisa yace da kamar wuya ku me yasa tuntuni baku nemeta ba sai yanzun, aiko tana raye kila bata garin nan, har sun mike zasu tafi me unguwa yace amman bari akai ku gurin babana kuyi mishi bayani ko zakuci sa,a ya fahimci me kuke fada, dan ya dade kwance babu lfy.

bayan an kaisu gurin shi tsoho ne sosai ummi ta mai baya ni.
tsoho yayi shiru zuwa cen ya kira dan sa me unguwa yana magana ahankali me unguwa yasa kunne me kake cewa baba.
baba tsoho yace karaka su gidan iya me kosai.
me unguwa yace baba ai iya ta dade da rasuwa.
sai gani hawaye sukayi yana bin kuncen baba tsoho ya sake cewa kukai su gurin danta malam musa.
Me unguwa ya sake cewa baba malam musa yariga iya rasuwa sai dai matar sa
[9:31PM, 12/9/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜

Story
&
written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed๐Ÿ“

73-75

Da sauri ummi tace toh ku tai maka ku kaini gurin matar tasa.
suna fitowa ummi ta nufi mota mutumin da me unguwa ya hada su dashi yace hajiya ai mota bata shiga unguwar.
nan suka bar motar suka yanka a kafa tafiya suke tafiya taki karewa ummi ta gaji jalal yace ummi ko zaki zauna ki huta ne?

a,a jalal mu tafi kawai kafin su isa ummi taci bakar wuya takalmin ta har ya bare zufa ke yanko mata ta ko ina kafar nan futo futo kamar ba itaba, suna zuwa ya nuna musu gidan.
ummi ce ta shiga jalal yana waje
sallama tayi acikin gidan ,goggo ta taho da sauri tana fadin hajiya batan kai kikayi ne

ummi tace a,a baki ne mu , munzo gurin mijinki sai muka same lbrn rasuwar sa.
goggo tace ayya malam ai ya dade da rasuwa, shigo ki zauna dauko tabarma tayi ta shin fida.

ummi ta zauna tana fadi ba zama ma zamuyi ba muna sauri ne.

goggo tace ai ban shai da kiba hajiya kin dai yimin kama da wata wadda na sani.
cikin murna ummi ta gayawa goggo abinda yake tafe da ita.
goggo tace ikon Allah ni ko na san saudatu kishiya ta ce tunda malam ya tsunto ta shekarar ta uku babu wanda yazo neman ta dan haka malam ya aure ta amman Allah yayi mata rasuwa tare da malam sukayi hatsarin mota su rasu.
da karfi ummi tasa ka kuka , jalal dake waje yaji kukan ummi ya shigo aguje.
yana shigowa ummi ta fara cewa abduljalal saudatu ta rasu.
jalal yayi tabawa ummi hakuyi, yace tashi mutafi
sun mike zasu tafi goggo tabi ummi da kallo matar nan ta bata tausayi tana son ta kaya mata saudatu tana da yarinya amman tanajin tsoro dan bata san inda safna take ba.
sun mata sallama zasu fita kenan sai ga wata kawar goggo ta shigo gidan.
tace baki kikayi ne?
goggo tace wlh yayar saudatu ce sai yanzun Allah ya bai yana yan uwanta

matar tace Allah sarki Allah ya kara muku hakuri saukin ta ma tanada yarinya.
dasauri ummi ta sake hannun jalal tace dama saudatu tabar yarinya shine baki fada mana ba.

tuni goggo ta fara rawar baki em dama mantawa nayi dayake yarinyar ba a gurin na take ba tana cen gurin dangin kakar su shi yasa bari ma kika hotunan saudatu shiga daki tayi da fito da hoton saudatu da malam da yar karamar yarinyar su dayan kuwa saudatu ce kadai ummi ta dauki wadda suke harda yarinyar ta kurawa yarinyar ido gani tayi kamar ta taba ganin yarinyar tuni tafara share hawaye tana fadin jalal yariyar nan kyakyawa ce tafi saudatu kyau tace jalal yarinya nan saina nemota saina mantar da ita rashin mahaifiyar ta da tayi.
jalal yayi murmushi yace ummi nima naji ina matsanan cin son yariyar.

bayan goggo ta musu kwatan cen garin su iya a zaria jalal yace yasan unguwar suna zuwa da alhaji. haka suka ma goggo sallama bayan sun bata gudi masu yawa suka baro ta.

jalal ya cire takalman kafar sa ya mikawa ummi taki karba , dan haka ya tanbaya a ina ake saida ta kalmi aka nuna masa yaje ya sayo ma ummi silifas ne yama mata yawa ta karba tasa.

bayan sun isa gurin me unguwa sukayi godiya sannan abduljalal ya dauki kudi masu yawa yace akai baba asibiti.

haka suka isa gida ga farin ciki ga bakin ciki.
suna fitowa a mota suka hango safna da kairat suna zaune agurin da jalal yake zama , kairat ce ta fara mikewa ta nufu gurin su ummi, dan haka safna babu damar guduwa itama gurin su ta nufu da miyar daddawan ta ahannu tana sha da cukali.
kairat tana hango ummi ta fara sheka dariya tace yaya kalli takalmin ummi daga kan ta tayi takalli jalal taga fararan kayan shi sunyi jawur idon nan zuro zuro takara fashewa da dariya tana cewa anty safna kalle su.
safna dariya ke neman kwace mata Amman tsoran ummi ya hanata yi.
ummi tariko kairat tana fadi almura dan bamuje dake bane dasai kin fimu datti, ummi ta juya zata shiga gida jalal ya ruko safna kairat dake rike ahannun ummi tace anty safna wlh ki gudu zai shafa mike datti.
ummi ta yaigo tace jalal meye haka.
sakin safna yayi ya fara tam bayanta meye wannan kike sha, ko faten daddawan ne?

banza tayi dashi yace wai har yanzun baki huce bane?
nan ma babu amsa da haka suka isa falon, lokacin da suka shiga sun samu ummi tana nunawa kairat hoton saudatu da yar ta .
kairat ta nuna karamar tace wannan wacece?

ummi tace antyn ki ce kinga mamarta kanwata ce
kairat tace ummi yaya sunan ta?
ummi tace๐Ÿ˜ฌ na manta ban tamyi sunta ba, dai dai nan jalal ya shigo shi da safna.
ummi tace jalal yama sunan yariyar nan.
jalal yace au ummi baki tambayi sun ta bane?
ummi kasa magana tayi ta dafa kai.
Jalal yace ba komai ummi karki damu suna ba matsala bane kwanan zamu gano ta.
nisawa tayi tace Allah yasa haka jalal, Allah yayi maka albarka.
jalal yaji dadi sosai yace ameen ummi , juyawa yayi ya kalli safna sai fama shan abu take yace ummi kalli abinda yariyar nan take sha.
ummi tace menene shi?
jalal yace wani abune baki wai faten daddawa?
ummi tace faten daddawa ko dai miyar daddawa, safna kawo nagani.
safna ta mike ta nufi gurin ummi ummi ta kalla tace miyar daddawa ce bar ta taita sha kila ta saba sha akauyen su.
Safna takalli ummi ta sunkuyar da kai tunda take da ummi bata taba mata rai kamar na yau ba, ta karbi miyar ta juya zata tafi jalal ya mike ya karbi miyar yana fadin bazaki sha ba.
safna tace kabani miyata ina ruwan ka.
jalal yace akwai ruwana wlh bazaki shaba.
safna na ja jalal naja safna ta juya taga ummi tana kallon su da sauri ta sakar mishi ta wuce daki tana kuka.
jalal zuwa yayi zubar da miyar yabi bayan safna yana shiga yasa meta ta fito bayi, yace wlh karna kuma ganin kinsha wanna abin kinji ko, inkuma kinki zan gayawa daddy, barima nagayawa anty nusaiba, dauko waya yayi aljihun sa yana dannawa.
safna ta mike da gudu saboda wani amai da taji yana taso Mata .
jalal na kokarin neman anty nusaiba yafara jiyo kakarin aman safna.

5 comments

  1. Pingback: poker online
  2. Pingback: unieke reizen
  3. Pingback: Kim Jong Un

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *