Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 18

MIJIN MARAINIYA PAGE 18

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 18

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

Story
&
written by
Fadila Lamido
Mmn Yazeed📝

 

Advertisements

DEDICATE
dis page to
*Husaina Faji*
_( Faji Rilwan)_​

*Gaisuwa agare ku*
*zulehat mohd njidda*
*hjy wasila dan sanwai, deeje oga*
*fatima bello ahmad*
*rashida ummar*
_da duk sauran da ban fada ba, ina gaisuwa agare ku_

76-78

Advertisements

Da sauri jalal yabi bayan safna ya kamata haka taita amai jalal na mata sannu, bayan ta gama da kansa ya wanke mata ya kamo ta suna kokarin fita kairat ta shigo tace yaya ummi na kiran ka .

to yace da ita ya wuce da safna kan gado ya kwatar da ita , sannan yace toh yanzun me zakici nasan kina jin yinwa.
da saurinta tace miyata zaka bani.
au bazaki bar zancen miyar bako baya gashinan ya lalata miki ciki, amma bazaki bar shan taba.
wlh ni ita kawai nake son sha dan Allah ka dauko min.
jalal yace ai nagaya miki baza ki sha shiba ni nama zubar da shi.
safna najin ya zubar mata da miya ta fara kuka.
jalal mikewa yayi yana fadi abin naki babba ne , yasa kai ya fita.
yana zuwa falo ya samu ummi har tayi wanka ta fito tace jalal memakon kaje kayi wanka ka hota .
ummi safna ce wannan abun da take sha ya lalata mata ciki sai faman amai take.
wuce kaje kayi wanka karabu da ita ita tasa ni.
cikin mamaki jalal ya wuce dakin sa yana mamakin wanne irin tsana ummi tayiwa safna
yana cikin wanka ya jiyo kairat tana yiwa daddy oyoyo sauri ya kara dan dama ya kosa dady ya dawo .
yana gamawa kuwa yafito kananan kaya ne ajikin sa, kayan sun amshe shi yayi kyau matuka.
yana shiga ya nufi daddy, tun daga nesa daddy yace jalal karka karaso nan dan bazaka haumin jiki ba mutun sai girma yake amman shi be saniba

jalal be tsaya ba dariya ya fara yana fadin daddy nafa dade ban ganka ba, yana isa ya zauna daf da daddy ya daura kashi akafadar daddy yace ina wuni daddy.
lfy lau jalal, ya safna?
ai daddy mun kusa batawa da safna, bata jin magana ta.
meya faro kuma kaida safnar taka?
daddy wai daddawa take dafawa tana ci, nayi nayi ta bari taki bari.
murmushi daddy yayi sannan yace jalal karka kara hanata ka bar ta taci, wata kila Sha,awa take.
daddy yau fa ya lalata mata ciki amai tai tayi fah dazun, yanzun ma tana cen kwance,

bayan sun fito safna har lokacin bacci take, gidan hajiya suka wuce suna isa alhaji ya shiga yana fadi , jalal tashi yariyar nan ta kwanta sosai.
jalal na taba safna ta mike ta fito amman jiri sai dibanta yake, jalal ya riketa, ahaka suka shiga ciki, wannan shine zuwan humaira na farko gidan hajiya, saidai kuma jikinta babu kwari.
folo suka same su har anty nusaiba suna shiga hajiya tace kawo ta nan kusa dani ta kwanta, anti nusaiba ce ta dafa safna tace safna meya sameki, duk kinbi kin lalace sai kace ba amarya ba.
sai alokaci safna ta sake kuka, anty ni yunwa nakeji , kuma nasha wahala nayi miyata yaya ya zubar min wai bazan shaba.
da sauri anty ta juya barayi jalal tace me yasa ka zubar mata, kana hauka ne?
jalal yace anty kisan abinda ta mayar abincin ta, daddawa fa take tafawa taita faman sha , kamar wata mahaukaciya.
daddy na daga gefe yana jinsu.
hajiya tace wata kila kaine mahaukacin banda abinka jalal dacen tana ci ne, tunda kaga tana ci ai saika tuhume ta, amman ba laifin ka bane, zaliha ce babban me lefi.
jalal har yanzun bai gane me suke nufiba.
hajiya ta sake cewa safna sai ki fada wani abun da kike so adafa miki .
safna kasa tayi da murya tace ni irin miyata nake so.
da sauri anty tashi ta shiga kitchen.
jalal matsawa yayi kusa da safna yace wai ke lafiyar ki kuwa.
be gama rufe bakiba yaji ta kwaro mai amai ajiki, jalal be damu da aman dake jikin shi ba yaje ya rike safna.
hajiya ta mike tarike safna tace jalal jeka ka gyara jikinka, jalal fita yayi arude alhaji ya bishi da kallo.
jalal na fita aman ya tsaya toilet ta wuce da ita tahada mata ruwan wanka, fitowa tayi ta wanke kayan safna ta shanya, safna nafitowa anty nusaiba tayi daki da ita, zanin hajiya ta bata ta daura ta hada mata da karamar riga, tace to muje ga miyar cen na gama.

suna fitowa suka samu hajiya suna ta fira da alhaji, jalal kuwa ya kwanta akan kujera, babu riga ajikin sa sai faman danna waya yake.
safna ko tana shigowa ta toshe hancinta.
anty nusaiba ta kalli safna tace meye kuma?
daurewa kawai tayi tace babu komai anty ni daki zan zauna.
anty tace a,a ki zauna cikin mutane zakifi jin dadin jikin ki.
haka safna ta zauna badan ranta ya soba dan ita kusa da jalal ne bata son zama saboda wani irin wari yake mata.
karban miyar tayi ta fara sha, dadi sosai ya mata domin anty har hanta ta zuba aciki, daddy kuwa kalon safna kawai yake yana murmushi, shikuwa jalal gani yake be kamata su biye mata taita shaba.
zuwa cen safna tace anty kicewa yaya jalal yaje waje.
anty tace akan me zai fita?
Jalal ma tashi yayi ya zauna yana jira yaji me zata ce.
safna tace anty wlh wani irin wari yake min, zai sani amai.
da sauri jalal ya nufo safna Ina wasa dake ne , dan kin rainani zakice ina wari.

07014197556
[9:34PM, 12/11/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

 

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝

 

79-81

Alhaji ne ya da katar da jalal kar ka taba yariyar nan kabar ta taji da abin da yake damun ta.
daddy bakajin abin da take cewa ne wai nine nake wari.
eh naji zo muje gida gobe kazo ka duba ta.
daddy to safna fa anan zamu bar ta?
alhaji yace eh, ke nusaiba gobe ki tam yi mijinki in yabar ki kizo ki kaita asibiti, nusaiba ta amsa, alhaji ya juya yana fadin jalal zomu tafi.
jalal kuwa ya kulu iya kuluwa yana gani daddy ya fita yace wlh zaki sani bakin ga suna goyan bayanki ba har kike cewa ina wari ko, yana gama fadan haka ya fita da sauri.

ahan yar su ta zuwa gida ne alhaji yace meye naka na damuwa dan ance kana wari, kasani ko ciki gareta.
jalal yayi shiro cen yace daddy cikin haihuwa?
eh mana ko baka sone?
sai alokacin kunya ta kama jalal ya dukar da kai.
alhaji yasa ke cewa dakai fa nake magana.
jalal yayi kasa da murya yace ina so.
kana so amman kake ta mata fada?
jalal ya sake cewa daddy ai ni ban kawo tuna nin haka ba, nadauka kawai kwadayi ne.

alhaji yayi dariya yace wa yaga jalal da d’a
jalal ma dariya yayi, ya shiga tunanin yanzo in ummi ta sani yaya zata yi, gaskiya be so ciki yanzon ba yaso sai sun tare agidan su.

sun kusa gida gaban jalal sai faduwa yake kar fa daddy ya fadawa ummi dan yaga daddy marna yake sosai bakin shi yaki rufowa.
jalal ya fara sosa kai, alhaji yace jalal akwai magana kenan, gaya min me yake damun ka.
daddy dama zan ce ne karka gayawa ummi.

tuni murmushin dake kan fuskar sa ya gushe yace saboda me?
rasa abun da zaice yayi sai cen yace ina ganin kamar bazata so bane.

fada alhaji ya fara kada Allah yasa taso, abon kunya kayi, ko cikin shege ne?
da sauri jalal yace a,a

bayan sun shiga gida ummi ta tare su da murna jalal ya wuce dakin sa.
bayan wucewan jalal
ummi duk ta kwashe yadda akayi zuwan su gidan goggota gaya mai, alhaji nisawa yayi sannan yace ya kamata agayawa baffa domin su tabbatar ta mutu hankalin su ya kwanta kuma suyi mata ardu,a.
ummi tace alhaji bazan iya tunkaran su da wannan maganar ba, da dai ace na samo yariyar ne sai naje.
alhaji yace kibani hotan na tafi dashi sai nayi musu bayani.

bayan subar wannan zancen alhaji yace zaliha wai yaya kike ganin yaran nan jalal da matar sa suna dai zaune lafiya ko?

ummi ta tabe baki tace nidai alhaji a inda nake ganin su kamar basa zaune lfy, shima da yake rawar kai naga ba kamar da ba.
alhaji yace nikuma sai naga kamar yarinyar ciki ne da ita.
haba dai alhaji wani irin ciki kuma.
alhaji yace ban gane haba dai ba, sai kace wadda bata da miji.

da sauri ummi tasha kwana a,a alhaji ai dama ba cewa nayi bata da miji ba, nidai banga alamun ciki bane, atare da ita.
ai dama bazaki gani ba saboda ba kula kike da itaba, da jalal ne bayi da lfy har yake amai bazaki ce baki sani ba.
eh alhaji jalal ya gayamin safna tana amai amman alhaji ai ba lallai sai ciki ba ne ake amai.

alhaji yace toh yariya dai tana ce babu lfy.
mikewa tayi bari na gan ta.
alhaji yace ai gidan hajiya muka baro ta, ummi ji tayi babu dadi.
washe gari jalal ya fito da safe zai tafi gidan hajiya.
ummi tana ganin shi tace ina zakaje da sasafen nan bayan yau babu aiki.
ummi zanje gidan hajiya ne, in duba safna.
zonan ka zauna babu inda zakaje.
ummi bata fah da lafiya ne.
eh naji zoka zauna bayan jalal ya sauna ummi tace wai me yake damun safna?

jalal yace nima ban sani ba.
ummi ta sake cewa toh waye yace wa alhaji safna tana da ciki?
gaban jalal ya fadi da saurin sa yace ummi ban sani ba.
ummi ta sake cewa jalal ina fatan dai babu abinda ya shiga tsakanin ka da safna?
shiro yayi kan shi akasa, gaban shi kuwa sai faman faduwa yake dan gaskiya yana matukar jin kunyar ummi sa, kartaga yaki jin magarta.
cikin fada ummi tace dan ubanka bada kai nake magana ba.
sai alokacin jalal yace ummi babu komai kasa ka rasawa yayi dai dai lokacin alhaji ya fito.

alhaji yana fitowa yace jalal kana nufin cikin da safna take dauke dashi ba na ka bane??
jalal mikewa yayi yace nawa ne daddy.
mikewa ummi tayi tace wlh alhaji karya yake zai dai rufa mata asiri ne , amman bata taba kwana dakin sa ba.

alhaji ya juya yace haka ne jalal, ka fada min gaskiya?

jalal ji yayi kamar ya tsaga kasa ya shige ayau zai kar yata mahaifiyar shi kuma in yayi shiru beyiwa safna adalci ba.
alhaji ya sake cewa jalal dakai nake magana, dama baka taba kwana daki daya da safna ba??
dukar da kai yayi hawaye na zuba afuskar shi yace mun taba daddy sau biyu

One comment

  1. Pingback: chat with models

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *