Advertisements
💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
story
&
written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝
4-6
Advertisements
Jalal yace haba ummi ai ba taba ta zanyi ba, bata kawai zan yi.
ummi tace ashe tsaftar ka ta banza ce , idai ka bawa yarinyar nan da hannun ka kuwa.
juyawa yayi ya ajewa safna kudin akasa, da saurin ta ta tsuguna ta dauka tana ma jalal godiya, ummi ko hararar ta kawai take.
bayan sun dawo gida ummi ta lura jalal fushi yake da ita, dan haka ta bishj har dakin sa, tace jalal me ya same ka, kake ta fushi?
abduljalal be iya boye wa ummi komai dan haka yace ummi yarinyar nan ce take bani tausayi, ummi da,a kwai yadda zanyi dana tai make ta.
ummi hada rai tayi tace yaro halin ka yana bani mamaki in banda abinka ina ruwan ka da yayan talakawa da har zaka damu kan ka, akan wata banza yarinya kazama, da kikiya.
ummi bazaki gane ba nasan da dady ne zai fahimce ni, ummi raken nera dari ne fa akanta, ummi kuma gashi yarinyar kyakyawa da ita.
zoro ido ummi tayi tace yaro kai ne kuwa, kaga yarinya mumuna kace kyakyawa ko dai gamu kayi ne, to naji kyakyawa ce me kake nufi yan zon.
ummi ni ba abinda nake nufi kawai dai inason ki tai maka mata ne.
kaga jalal karna kuma jin manar yarinyar nan abakin ka, ta mike da sauri tabar wajan.
Advertisements
itako safna zuwa tayi gurin wasu almajirai tana raba musu, iya na daga gefe tana kallon safna, saida ta gama ta juya zata tafi iya ta kwala mata kira , ai tana ganin iya ta roga da gudu ta kamkame ta, cikin rudu iya ta daga kan safna tace a ina kika samu rake kike rabawa Jama,a? Safna ta kwashe labari kaf ta fadawa iya, salati iya ta shiga yi, tana fadin ina can zaune za,a lalata min jika, wanne dan iskan ne, yabaki kudi?
iya nima ban san shi ba kawai gannin su nayi amota.
be miki komai ba dai ko?
ba abinda yayi min, iya tasa keyar safna tayi tace muje na samu goggon taki, in kaskiya ne ta daurawa salma mana.
suna shiga iya ta fara fada taita fada tundaga ranar rokon safna yadawo hannun iya, safna dadi takeji sosai agurin iya babu ta kura, iya duk ta. hada dan kudin da take da shi ta mai da safna makaran ta, haka iya tai ta wahala da safna ana haka safna ta gama primary schools, gashi iya nason safna ta ci gaba da karatu kuma bata da kudi Dan haka ta fara toya kosai a kofar gida, iya bata barin safna tazo gurin tuyan kosan ta sai dai aikace aikacen cikin gida duk da cewa iya ba wani karfi gareta ba, amman safna ta murje tayi kyau kamar ba ita ba.
a yanzun safna tana J S2 dan haka iya ta fara tunanin aurar da safna dan duk da cewa safna bata wuce sha bakwai ba, itako safna babban burin ta shine ta tayi karatu me zurfi.
ana cikin haka rashin lafyya ya kama iya dan kosan da take yi ya gagara, safna ta rasa ya zatayi , tana kuka ta nufi gidan goggo, ta gaya mata iya babu lafiya.
fada ta fara tana fadin aiga irin ta nan, kina nan muna neman kudi tazo ta dau ke ki, sai yanzun da ciwo yakama zaki taho to bamu da kudi, wacce ki bani waje karna kara ganin ki gidan nan, haka safna ta juya tana tafe tana kuka.
haka safna ta dawo ta samu iya kwance cikin amai, ta shiga gyara wajan bayan ta gama ta fara tunani yadda zata samo ma iya abincin da zata ci, tashi tayi ta fita ta gama bulayin ta bata somo komai ba ba yadda zatayi dole ta koma wurin goggo sai da ta gama zagin ta sannan ta bata ragowar tuwan jiya da sauri ta nufi gida tana ta sauri , tun kafin ta isa kofar gidan ta hango muta ne tana shiga gidan kara kamkame tuwan ta tayi ta sheka da gudu tana shiga taga an lulube ta da zani, safna fadawa tayi jikin ta tana kuka.
Wata makociyar su iya ta taho ta dafa safna tace kiyi hakuri safna ki daina mata kuka Allah ya karbi abinsa kuma ya fimu santa dan haka sai muraka ta da.ardu,a haka safana taita kuka har aka kai iya makwanci ta safna bata bar kuka ba.
bayan anyi bakwai da yamma goggo ta hada kayan ta ko salama batawa safna ba ta wuce gida, gidan iya kuwa safna ce ka dai aciki sai ta tsince kanta cikin matsanan cin tashin hankali, haka safna ta kwana ita kadai acikin gidan, safna na tashi hankalin ta kara tashi yayi musamman da ta leka dakin iya taga wayam dan haka ta tsoguna abakin kofar iya ta saki Kara.
makociyar iya baba dije taji kukan safna aguje ta zagawo tace Ina goggonki .
safna tace ta tafi tunjiya
au yanzu nan nufinta baza ta rike kiba, lalai abin nata babba ne, tashi ki hada kayanki na rakaki .
cikin tashin hankali safna ke hada kayan ta tana ganin ita meye amfanin ta tuda ba iyayen ta iyar ma da take takama da ita ta tafi ta bar ta itama da mutuwar kawai tayi.
suna shiga gidan goggo suka same ta tana tankadan garin tuwo, tana ganin safna ta hada rai, bayan sun gaisa tace yazaki tafi kibar yarinya ita daya acin gida.
cin sauri goggo ta fara rantse rantsan ita sam bazata rike safna, baba dije ta fahimci da gaske ta keyi tace to naji to me zai hana ki kaita gun dangin iya.
cinkin sauri goggo tace ina naga kudin motan da zan kai ta.
kwance haban zanin ta tayi takwaso gudin wajan duk ta mikawa goggo ta sannu ta karba harda fadin yauyau zan kai ta.
goggo bata tashi kai safna ba sai gaf da mangariba tace dauko kayanki mutafi , safna ta dauki kullin kayanta suka kama hanya, motar cikin gari suka hau , safna tace azuciyar ta dama motar garin su iya acikin gari ake hawa ,take farin ciki ya rufeta ko banza yau zataga gidaje masu dan banan kyau .
suna isa aka sauke su garin kamar rana saboda fitilun da suke haka ko,ina gidaje kuwa fadan kyansu bata lokaci.
suna ta tafiya taki karewa ita dai safna bin goggo kawai take suna zuwa gurin wata katuwar bishiya, goggo tace safna zoki zauna anan naje na dawo , haka banzayen kakannin ki sukama uwarki har ta mutu bata kara saka su a idon taba.
3 comments