Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 3

MIJIN MARAINIYA PAGE 3

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 3

 

Advertisements

 

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed

Advertisements

7-9

Itako safna bata fahimci me goggo ke nufe ba dan bata da wannan labarin , haka tai ta zaman jiran goggo har ta gaji tun tana ganin wucewan mutane daidai har ta daina gani dan haka tsoro ya shige ta, mikiwa tayi tabi hanyar da goggo tabi , tana tafiya tana dubawa ko Allah zai sa su hadu da goggo.

wata mota ce ta shigo layin tun daga nesa motar ke hasko ta, dan haka ta tsora ta , motar na zuwa kusa da ita ta tsaya, wani dake cikin motar yace yace ke ina zaki da daddaren nan, kisan ko karfe nawa kuwa?
cikin kuka me ban tau sayi ta girgiza kai wanda ke mazauni direba yace kabir ina ruwan ka da ita ne kasani ko aljana ce yanzun 12:15 pm fah ,yace yarinyar ar zikice za aganta a waje awannan lokaci, kabir yace kuma fah haka ne aboki na, motar su kaja suka mike layin.

Advertisements

Safna ko babu abin da take ban da kuka, gaba tayi kadan ta samu wani dan dutse ta zauna sautin kukan ta kawai kake ji awajan wasu samari ne suka zo wucewa su uku irin yan shaye shayen nanne sun sha sun bugu daya daga cikin su yace kai kunga wata baby danya, da sauri suka isa wajen ta suka fara ja mata dan karamin hijjabin dake jikin ta safna ko kuka take tana kokarin guduwa amman Ina sun riga sun rike ta dukkan su ukun har sun yaga mata riga dama bawani kwari ke gare suba suna kokawan kwance mata zani .

wan,nan motar ta dazun ce ta sake dawo ,mutun daya ne acikin ta sabani dazun da suke su biyu jin uhun yariyar yasa shi tsayawa ya haska su da fitalan motar yaga abinda ke faruwa da sauri ya fito yafara takawa zuwa wajen yana musu tsawa cikin fada ya daga murya sosai .

daya daga cikin su yace kai kuzo mu gudu yaya abduljalal ne da gudu suka kwasa abduljalal ya matso kusa da ita ya tsoguna ya dauko hajjabin ta ya mika mata ta karba ta saka kuka kawai take abduljalal yace yanzun ina zaki?

tace goggo nace tabar agun wata bishiya tace na jirata kuma naga ta dade bata dawo ba, sheni na biyo hanya ko zan ganta.
cikin mama jalal yace kina nufin mahaifiyar ki kece abarki a titi.

a,a kishiyar mama tace.
yace to ke ina mamar ki?
cikin kuka tace suyi hatsari har baba na sun rasu.
Jalal ya tausaya mata sai dai har yanzun be gama yar da, da yarinyar ba yana ganin kamar dai ta fito yawo ne, ya juya yace Ina yan uwan ku suke,
tace nibasan kowa daga cikin dangin muba kakata kawai na sani itama ta rasu jiya akayi bakwai, shine akace ma goggona takaini gun dangin kakata, shine ta barni tace najira ta tadawo.

hankalin jalal ya tashi ya rasa yan zun ya zai yi da yariyar nan gashi dare na dadayi , zuwa yayi yabude motar sa ya shiga da gudu safna ta biyo shi tana fadin dan Allah karkabar ni anan.
ai bazan barki a nan ba ya bude dayan gefen yace shiga mutafi , bayan tashiga ta zauna jalal yace ya sunan ki?
tace sunana safna.

Jalal ya sake maimaita sunan safna da sauri yafara neman fitilan motar haske ya baiyana yace safna bake bace shekarun baya na saya rake wajen ki, dama ke ma rainiyace.
cikin kuka tace eh.
Yace to kibar kuka safna insha Allahu zakiji dadin rayuwan ki , jan mutan yayi ya fara tafiya yana tunani yadda zasu kwashe da ummin sa.

lokacin da ya isa gida me gadi yabude mai ya shiga yarasa yadda zaiyi da safna dan yasan yanzun ummi batayi bacci ba saitaga dawowan shi , kilama yanzun tana kallon shi, dan haka dibara tafado mai yace safna inazuwa bari naje nadawo.
cikin sauri safna ta rokoshi tace dan Allah karka gudu ka barni kaima.

cikin kwatar da murya yace bazan guduba safna yanzun zan dawo ai nan gidan mune da guduwa zanyi ai bazan shigo dake cikin gidan muba, ban so ne ummi na ta ganki daddaren nan saboda kartayi wani tunani daban kuma nasan tananan tana jiran shigowa ta, sabo da haka kijirani yanzun nan zan dawo.
Gyada mishi kai kawai tayi amman bata son ya bar ta anan.

yana shiga ya samu ummi sai zagaye falon take da sauri shi yaje ya rungume ta, hannu ta tasa ta tukude shi.
abinda kuma zaka fara kenan yawon dare Ina ka tsaya har 1:30 shiyasa babanka yake cewa ninake sangarta ka.
tsugunawa yayi ya kama kafar ta yace immi kiyi hakuri kabir ne be fito da motar saba sai da nakaishi gida kuma ummi kisan gidan su da nisa amman ummi dan Allah kiyi hakuri bazan kara ba.
hannun ta tasa ta dago shi ta rungume tace jalal dole hankali na ya tashi kaikadai nake kallo naji farin ciki ya lulubeni nazaci kai kadai ne kwaina a duniya sai daga baya Allah ya kawo mana Kairat alokacin dana cire tsanmani kuma har yanzun baji sonka ya ragu azuciya taba, jalal nakosa naga matarka zataga gatan da babu wacce ta taba samu a gurin sirikar ta, balle kuma naga yaran ka.

dukar dakai yayi yana murmushi , ummi tasake cewa jalal baka fara tunanin aure bane har yanzun.
da da durkusar dakanshi kasa yayi yana sosa keya.
ummi tace yau kuma kunya ta kakeji , hmmm jalal mayan kasan, abin da nake so dakai in katashi nemu mata kasamo mana yar manyan mutane kar ka sake kawo mana yar matsiya ta.

 

7 comments

  1. Pingback: my profile
  2. Pingback: special offers
  3. Pingback: free chat
  4. Pingback: Shop Now

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *