Advertisements

MIJIN MARAINIYA PAGE 7

MIJIN MARAINIYA PAGE 7

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 7

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝

19-21

Advertisements

Bude murfin motar tayi ta fito, ta zagayo ta rike safna tana tura ta cikin motar, jalal ma riketa yayi yace ummi ki dai na irin wannan babu kyau fah, cikin tamke fuska tace sake ta jalal idai ba kana son ranka ya baci bane.
ummi dan Allah kibari ,ta canxa kaya sai ku tafi.

zuwa tayi gaban shi tace wlh wlh in baka sake yarinyar nan ba ranka zaiyi mummunan baci, kasake ta kawai.
dukar dakai yayi ya kara rike gefen rigar safna ciki tashin hankali ya dago ya kalli ummi ya sake dukar da kai.
Safna na tsaye tsakiyar su tayi tsuro tsuro, ummi ta sake cewa ba dakai nake magana ba, gani tayi ko motsi ba yayi dan haka ta taho gadan gadan ta kwashe shi da mari.

da sauri jalal ya saki safna ya dafe wajen dan shi atunani shi babu wanda ya taba dukan shi.

Advertisements

jalal kallon ummi yayi cike da mamaki, yace ummi nine fah, jalal dinki ne fah.
ummi bata saurari me jalal yake fada ba ta tura safna mota suka bar wajen.
binsu yayi da kallo yana bakin cikin wai mahaifiyar shice take wannan dabi,a wai yaushe ummi ta canza , shi dai yasan ummi na son farin cikin shi.

Yana nan tsaye drive ya dawo da kairat daga makaranta, tana fitowa ta hango jalal da gudu ta karaso ta rikeshi, gani hawaye tayi yana bin kuncin sa tace yaya waye ya dake ka.

Jalal da besan hawaye na fita ba yasa hanu ya shafa idon sa yace idona ne yake ciwo, riko hannuta yayi suka shiga gida, kairat taso ta bishi dakinsa yace mata bacci yake ji.

tunda jalal ya shiga daki yasa key, yau dau ki waya ya kira mahaifin sa har ta katse be dauka ba, ya ajiye wayar ya kwanta ,da matsa nan cin bacin rai yau da ummi ba mahaifiyar shi bace da sai ya dauki mumunan mataki akanta, shi bema san me yake damun saba illa dai kawai yasan yana matukar kishin safna wanda ko mace yar uwanta baya son yaga ta cika kallon ta da yawa, bare kuma na miji.

su ummi basu dawo ba sai wajan 9:00 shiko jalal tun yamma zazzabi ya rufe shi dan ko sallah ma a daki yayi ta.

ummi na shigowa hara bar gidan taga motar alhj tace wai nikam me yasa alhj yake min haka, inzai dawo bazai sanar dani ba saidai na ganshi kwatsam.

da sauri ta fito safna ma ta fito ummi tace ke dakata duba cikin ledan cen ki dau hijjab ki sanya, safna ta juya ta dauko wani zumbulelen hijjab har kasa ta sanya.

suna shiga alhj na zaune afalo ya rufeta da fada, kwantar da kai tayi tai ta bashi hakuri, safna kuwa sumi sumi ta shige daki.

sai da yagama zazzaga bata sannan yace ina abduljalal tare kuka fita?
a,a mun barshi gida.
toh ina yaje kuma sunce kwata kwata yau beje office ba wai me yasa yaron nan yanzun duk yabi ya rikice ne, shifa ya matsa sai na bude mai kamfani kuma dan me yanzun zai sanya wasa, dazun nakira shi wayar shi kashe take, wai me yaron nan yake nufi ne.

ummi tace haba alhaji sai faman fada kakeyi kayi hakuri duk ma inda yake nasan hankalin sa na gida.

*********

barin zancen sukayi suka kama wata hirar, kairat ce ta fito tana dari daddy daman kadawo shine baka kirani ba.

cikin murmushi ya rike ta yace kairat na rude ne har yanzun abduljalal be tadawo gida gashi wayar shi kashe take.
cikin sauri tace daddy dazunfa an daki yaya jalal a office din su yana ta kuku, amman sai yayi min wayau yace wai idon shi ke ciwo kuma yaki bari na bishi daki wai shi barci yake ji, cikin shagwaba ta karasa zance ta.

ummi kuwa
Cikin ta kara ya fara dan bata zaci zai dau abin da zafi haka ba.
alhj ko kallon ummi beyi ba yatashi ya nufi dakin jalal ya tura kofar yajita kulle , juyowa yayi ya kira ummi yaron nanfah bashi gidan nan, cikin rudewa tazo ta wuce alhj ta isa kofar ta fara Kira yaro yaro shiru, jalal jalal nanma shiru kuka ta saka tana fadin nashiga uku, alhj ya daga murya yace abduljalal, da sauri ya amsa
na am daddy.
yace zoka bade min kofa.

yana rawan sanyi yazo ya bude kofar rige rige suka fara kowa na kokarin kai hannun shi jikin jalal komawa gado yayi ya kwanta .

alhj ya dafa jalal yace me ya same ka, waye ya tabaka dan waye agarin nan, ka gaya min waye uban sa.

ummi ce ta kawo hannu zata tabashi, yace daddy kace mata karta tabani daddy kace ta fitan min adaki.
alhj yace jalal ummin kace fah wai baka cikin hankalin kane.

ina sane daddy cikin hakali na nake kawai bana son ganin ta ne.
tsawa alhaji yayi wa jalal mahaifiyar ta ka kake cewa baka son gani kar na kara jin wannan kalman abakin ka.

shuru jalal yayi yana kuka kasa kasa ummi na makure jikin bango , alhj ya dago yace to ya isa dai na kuka sai kace ba namiji ba lallai ummin ka tayi laifi, abduljalal gayamin me ummin ka tamaka da zafi haka har kake zubar da hawaye.

Jalal juyar da kansa gefe yayi sannan yace daddy ummi nasa safna nayin shigan banza tana fita waje, kuma nayi magana ummi ta mareni.
mari ? zaliha ke kika mari jalal akan me, alhj mikewa yayi ya daki kirjin shi yace dana kika Mara

5 comments

  1. Pingback: huaysod
  2. Pingback: 1win apk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *