Advertisements
Ni Ce Nasan Sirrin Bestie Fiye Da Kowacce Mace.
Marubuciya Rasheedah Bintul Islam ta bayyana yadda tasan sirrin bestie.
Advertisements
“Shi fa bestie babban masifa ce ga yarinya da kuma iyayenta har mijinta, mutum na da budurwarshi ka kai ko hannu ba ka taba riƙe mata ba amma bestie shi….. Al’amarin bestie Babu kyau, sa’annan bestie yana iya yiwuwa har yarinya tayi aure duk wani sirrin gidan aurenta yana a hannun bestie, ko kyauta kayi mata sai ta raba da bestie, yarinyar kirki ba ta yin bestie, da yawa fa da za’a yi DNA da bestie ya shiga uku, wannan bestie da aka maida wasa ba abun wasa ba ne, wai yarinya tana da bestie babu aikinsa sai koya mata ayyukan lalata”.
“Amma yanzu an maida abun wasa bestie zai rungumi bestie normal ce wurinta, bestie zai riƙe hannun bestie, bestie ya fi ka sanin sirrin budurwarka ko matar ka, dss”. Inji Rasheedah Bintul Islam
Saide duk da haka, munyi nasarar kiran Malam Nura ‘Yar adua Assalafiy, a wayar salula, wanda malamin Addinin Musulinci ne, inda wakilinmu Zaharaddeen Gandu ya ce shin malam ya dace mace ta yi bestie? Malamin ya bayyana mana cewa:
Advertisements
“Gaskiyar magama bai halarta ba mace tai aboki, ko bestie, ko wani boyfriend ko da batai aure ba, barema mai aure wadda zatai bestie ko wani babban abokinta alhalin tana da aure, wanda tayi aure amma bata iya rabuwa da shi, wanda zasu rinƙa chat da waya da shi, har ma ya rinƙa rakata anguwa, to wannan ba karantawar Manzon Allah SAW ce ba, Musulinci bai bada umarnin haka ba. Bestie ko wani aboki bai daga cikin muharramai”.
“A cikin Suratul Nurr an bayyana cewa, “kada mata su bayyana ƙawarsu sai ga mazajensu, ko mahaifansu”, duk a cikin mutane 13 da Allah SWT ya faɗa bai faɗi aboki ba, saboda aboki bai cikin muharramai, duk wanda ba muharramin mace na jini ba, ko na sha-ga-mama, to sunansa Ajanabiyyi, wato manisancin mace”.
“Manzon Allah SAW yace, “kada wani mutum ya kaɗaita da wata mata idan ba matarshi ba”. A cikin Hadith ɗin da Bukhari ya ruwaito, wanda musulinci ya hana duk wani namiji ya kaɗaita da macen da ba muharramarsa ba”.
“Sannan shi bestie ko wani aboki musulinci ko al’adar Malam Bahaushe duk bata yarda da irin halayyarsa ba, domin a iya sanina bestie ya kashe aure da dama, wanda bansan adadi ba, sannan yana ci gaba da haɗa faɗa tsakanin ma’aurata”. Inji Malam Nura Assalafiy Katsina.
4 comments