Advertisements
Abubuwan Da Ake Bukata
Taliya
Tumatir
Advertisements
Nama
Kaza
Karas
Advertisements
Koren
Wake
Peas
Magi
Kori
Tafarnuwa
Citta
Albasa
Hadi
A dora ruwa a wuta, bayan ya tafasa sannan a zuba taliya da gishiri kadan, Idan ya tafasa daya sai a tsame a dora man gyada a wuta sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da jajjagaggen attarugu,
A tafasa nama sannan a yayyanka shi kanana sannan a zuba.
Azuba magi, kori da garin tafarnuwa da citta sannan a dauko wannan taliyar a zuba ta a ciki a gauraya. A zuba ruwa kadan sannan a rufe bayan mintuna biyar a sauke.
A tafasa kaza ta yi laushi hade da magi da kayan kanshi sannan a soya da man gyada. A soya tumatir da attarugu da albasa.
Azuba magi da citta da tafarnuwa. Bayan sun soyu sannan a dauko kazan a cakuda shi a ciki sannan a dora a kan wannan soyayyar taliyar.
3 comments