Advertisements

IMG 20211228 WA0080

TSUNTSU ME WAYO PAGE 10

Posted by

TSUNTSU ME WAYO PAGE 10

 

Advertisements

🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
Tsuntsu Me Wayo
🕊🕊🕊🕊🕊

Storry & written
By
Fadeela Lamido

                           PAGE 10

Advertisements

Bece komai ba har yanzon kuka yake yana mamakin zinat anya kuwa ba karya suka shirya mai ba domin shi rabon daya ganta ya dade kuma ai bakai tsaye yake shigarta ba.

  kwanan haydar 2 agidan alhj yusuf zuwa yanzon ya dan saki jikin shi saidai ya dan rame gashi zama agidan ya isheshi dan alhj yusuf ba mata gareshi ba, dan haka gidan babu dadin zama.

shima alhj yusuf zaman ya isheshi Dan haka ya fara tunanin dawo da salame saidai be saniba ko haryanzo iyayen nashi nanan akan bakan su.

Advertisements

  washegari yanufi gidan dada sallama yayi ya shiga dada ta tareshi da Fara,a itako salamatu tana ganin shi ta shige daki bayan sun gaisa da dada shiru sukayi nadan wani lokaci sannan alhj yusuf ya fara fadawa dada kudurin sa.

farin cikine ya rufeta har ta kasa boye murnanta daki ta shiga cikin farin ciki amman saita tarar da salamatu tana kuka.

tana ganin dada tace dada nifa bazan koma gidan sa ba, shekarana uku da dawowa garin nan betaba lekomuba tunda ya karbi yarshi sau 1 ya barta tazo gidan nan be mason tayi alaka dani sabo da ayanzo bana gaban shi dan haka ni bazan saurareshi ba.

fada dada ta fara tana fadin wani irin tunani ne wannan da baki gabanshi aida bezo gidan nan da niyar zai maidaki dakin kiba kikasan dalilin shi nayin haka ki tunafah tunda ya rabu dake haryau beyi aure ba dayake ke butulu ce har kk wannan mgnr toh tashi maza kije ki saurareshi .

koda alhj yusuf yayiwa salamatu bayani batace a,aba aman fuskar ta adaure take tam kamar bata dariya dan haka hankalin alhj yusuf ya tashi yace salamatu kodai yanzon baki ra,ayi nane?

cikin fushi ta fara zaiyanane mishi kamar yadda ta fadawa dada.

farin ciki ne ya kamashi ashe har yanzon yana nan makale azuciyar ta yana murmushi yace Allah ya huce zuciyar ki nayi kuskure kuma ina neman afuwarki ki yafemin kuma idai fatima ce harsai kin haji da ganin ta haka alhj yusuf yayita rarrashi salamtu harta yadda ta amince sannan ya fada Mata shifa baya son abun ya dau lokaci dan haka suka tsaida akan ranar juma,a me zuwa.

yana barin gidan gidan mahaifin sa ya nufa ya fada masa kudurin sa.

murnace ta kamasu gaba daya har yadidko godiya sukayiwa Allah tare dayiwa dansu fatan alheri.

   *Ranar juma,a*

taslima da fatima zaune adakin su suna hira taslim tace wlh fatima na kosa atsaida ranar bikin ku.

  tsaki fatima tayi sannan tace

  nidai gaskiya ban kosa ba keni idan ma naji anyi maganar bikin gabana fadowa yake shima yaya kullu maganar shikenan wai ya kosa ranan nan fah har cewa yayi zai gayawa daddy, waishi hakurin shi ya fara karewa

tintserewa tayi da dariya sannan tace ai yadai fad’amiki ne amman ba iyawa zayiba , da dai yaya haydar ne, sake kallonta tayi sannan tace yauwa sister naga wani abu acikin akwatin ki acikin wani d’an karamin akwati.

“murmushi fatima tayi sannan tace eh yaya ne ya bani”

” taslim ta sake cewa menene aciki?

dafata fatima tayi sannan tace kai taslim kin cika gulma toh nima bansan menene aciki ba kuma yace karna bude sai ranar da akadaura mana aure.

cafdi ai inda nice wlh saina bude yasan……….

gud’an da ummi ke rangad’awa ne ya dakatar dasu daga hiran mikewa sukayi atare suka fito suna rige rigen tambayan ummi .

cikin farin ciki ta dafa fatima tace
fatima ki godewa Allah yanzon haka mahaifiyar ki tana gidan babanki an mayar da auren su, yazon salis yayi waya yace gashima agidan.

wani farinci ne ya kama fatima ta saki murmushi zuwacen kuma ta fashe da kuka.

ummi ce ta kamota ta rugume tana fadin haba fatima keda zaki godewa Allah kuma, meye na kuka .

  saidare salis ya dawo hannun shi rike da ledoji bayan yayi wa ummi sannu da gida ya kalli taslim yace ke Ina zahara?

kallon shi tayi sannan tace tana  daki, yaya wai meye acikin ledar?

   “yana tafiya yake fadin inaruwan ki”

washegari

salis ne ya dauki taslim da fatima zai kaisu gidan alhj yusuf murna ce ba kadan ba azuciyar fatima.

suna shiga gidan suka samu haydar kwace akan kujera yana danna wayar shi salis ne ya nufi gurin shi ya kama kafafuwan shi ya d’aga sannan ya zauna agurin tsaki haydar yaja sannan ya tashi ya zauna salis ne yace wa haydar ina mama?

  atakaice yace tana ciki.
daidai lokacin  salamatu ta fito daga daki fatima ta tashi da sauri ta nufe ta, tureta tayi ta jawo taslim dake bayanta ta rungume sannan tacewa fatima aike babu ruwana dake.

komawa tayi kusa da salis ta zauna tana turo baki.

kallonta kawai salis yayi ya sunkuwar dakai.

  mama ko tana rungume da taslim tana tambayan ta karatun ta.

alhj yusuf ne yayi sallama ya shigo zama yayi cikin su bayan sun gaisa ya tashi ya nufi d’aki

itama mama mikewa tayi sanna tacewa taslim tashi ki shiga kitchen ki debo muku abinci, tana fad’an haka tashiga d’aki

  haydar ko sai, satan hararar fatima Yake

  salis ko kallon fatima yayi yace ke wai baki iya bada hakuri bane?

kara turo baki tayi sannan ta kauda Kai, daidai lokacin taslim ta kawo abinci ta ajewa salis nashi sannan tacewa fatima sister zo muci.

  azuciye tace banzanci ba.

” har salis yakai abincin dafda bakinsa yadawo dashi sannan ya kalli fatima yace sabo dame bazakici ba?

saida ta kara turo baki sannan tace toh aini batace dani ba kuma saina kamaci sai kace mayya.

dariyace taso kubucewa haydar amman sai ya dake yaci gaba da danna wayar shi.

  salis ma dakewa yayi sannan yace toh ke wai baki iya bada hakuri bane, kitashi maza tun kafin raina ya baci kije ki bata hakuri.

   mikewa tayi ta fara kuka tana buga kafarta akasa kamar karamar yariya tana fadin nifah ba abinda na mata ni yaushe ma naganta bare na mata wani abu.

  tun salis na kallon fatima har ya gaji ya rufe idonshi dan ya lura yau fatima so take ta rud’ashi.

   shiko haydar baki ya saki yana kallon fatima tuni yanayin shi ya fara cenzawa ji yake kamar ya tashi ya rungume ta

  fatima ce ta lura haydar ita yake kallo dan haka ta tsaya cak tana mamakin shi kuma wannan me yake kallo.

  salis ko yanajin fatima ta daina kuka ya bude ido cikin bacin rai yace meyasa kike min haka ne zahara dan Allah idai baso kk kijamin fushin Allah ba toh ki dakata da irin wannan abun, kije kiyiwa mama sallama kizo mutafi.

   sumi sumi ta wuce ta tura dakin mama tana shiga haydar ya kalli salis yace wlh kai wawane d’an kauye.

murmushi salis yayi tare da mikewa yana fadin Allah ya shirye ka.

  zuwacen mama da alhj yusuf suka fito fatima na rike hannun babanta .

alhj yusuf yaga salis da taslim tseye yace kardai har zaku wuce?

  salis ne yabashi amsa eh baba zamu tafi.

  yace toh daman Ina son ganinku kaida haydar tsakanin ku wanene akace sun daidaita da fatima?

da sauri haydar ya d’akai ya kalli salis shima salis d’in kallon shi yayi

🕊🕊

8 comments

  1. Pingback: cams free tokens
  2. Pingback: cinema rule
  3. Pingback: Aviator
  4. Pingback: pg168
  5. Pingback: Sweet Bonanza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *