Advertisements

IMG 20211228 WA0080

TSUNTSU ME WAYO PAGE 4

Posted by

TSUNTSU ME WAYO PAGE 4

 

Advertisements

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

12 -14

Advertisements

Ummi na kwace akan gado taga fatima rike da ciki arude ta diro da kafafuwan ta tace

” fatima lfy me ya sameki aciki ?

kasa magana tayi illa kuka da ta keyi.

Advertisements

ummi ce ta kamota ta kwantar da ita jikinta tana rarrashinta ,ta gayamata me yasame ta

daidai lokacin salis da taslim suka shigo dakin, salis yace sister ya haka muna ta jiran ki kuma kinki fitowa,

kallonta yayi sosai yaga ashema kuka take ya sake cewa ummi me ya sameta.

nima abinda nake tambayanta kenan taki magana.

tsugunawa yayi gaban su yace sister gayamin me ya sameki?

cikin mamaki take kallon salis azuciyar ta tace lallai wannan munafiki ne wato har yaje ya cenzo kaya dan tsabar mugun ta ahankali ta dago jajayen idonta ta harare shi sannan tace

bakai bane kasa kafar ka ka naushe ni aciki.

zaro ido yayi sannan yace ni kuma ? gaskiya bani bane ,sister toh me kikamin da zan dake ki?

ummi ta kalli salis tace haydar ya dawo ne?

Ok eh ummi sanda muka fita nida taslim naga shigowan shi.

batace komai ba ta mike ta fita adakin salis ya matsa gabanta ya kamo hannun ta yana wasa da yatsuta yace kiyi hakuri, zahara bani bane kisan mu yan biyu ne kuma muna matukar kama nan gaba kad’an zaki fara banbance mu dan akwai dan banbanci,
kallon idonta yayi sannan yayi murmushi yace ban da abinki ma sister ai shigar mu ba iri daya bace shi bakiga ya tara gashi bane saikace mahaukaci.

taslim ce ta saki dariya tace wlh brother ni yanzon ma tsoro yake bani haka ranar nan daga naje wucewa ta kusa dashi lokacin yana waya saiji nayi ya jifeni da cup wai nazo naji abinda yake cewa ne naje na gayawa ummi.

salis yace ai yana da matsala haka dai zakuita hakuri dashi.

ji sukayi anturo kofar ummi na gaba haydar na bin ta abaya zuwa yayi ya tsuguna agaban fatima kamar yadda yaga salis yayi kamar me ciwon baki yayi mgn ahankali sister kiyi hakuri na manta acemin kina gidan nan na dauka wata ce daban.

shiru tayi ko kallon shi batayi ba sai dai ko ahaka ta gane banbancin murya atsakkanin su domin kuwa muryar salis tafi na haydar sanyi.

jinda yayi tayi shiru yasa ya waiga ya kalli salis yace brother katayani bata hakuri

salis yace bakumai haydar ya wuce sai dai akiyaye gaba.

sai alokacin haydar ya kalli fatima daniyar yayi mata godiya amman yana kallon fuskarta ya kasa cewa komai sakamokon muguwar kama da tayi masa da wata yariya da yake marmarin sake kasan cewa da ita

mikewa yayi cikin sauri ya nufi kofa dukkansu binshi sukayi da kallo ummi ce tace ikon allah, Allah ka shirya wannan bawa naka

salia ko mikewa yayi daga gaban fatima yana fadin toh yanzo dai shikenan haydar ya hanamu fita.

Haydar na fita ya nufi dakin mahaifin shi kamar yadda ummi ta umarceshi ahankali ya tura kofar ya shiga neman guri yayi ya zauna sannan ya daga kai ya dubi mahaifin shi dake zaune yana karatun jarida, ahankali yace

” daddy ina yuni?

baza yayi dashi kamar ma besan da shigowar shiba zuwa cen yace a inakakwana?

kanshi akasa yace daddy mun je zaria ne muna kan hanyar mu ta dawowa motar ta lalace amman dan Allah kayi hakuri bazan….

tsawa ya daka mishi wanda yasa dole yayi shiru sannan yace Karka maidani mutumin banza haydar guda nawa kake, nine ubanka babu wani dubara da zakamin, batun yauba na kula kai mutumin banza ne, toh bari kaji daga yau kar magriba ta sake maka awaje kuma daga office ban amince ka wuce ko Ina ba kanajina ?

eh kawai ya iya furtawa domin hukuncin yayi masa tsauri.

da daddare salis ne zaune adakin su yana karatun Qur,ani yayin da haydar ke kwance akan gado sai juyi ya keyi.

zuwacen salis ya rufe Qur,anin ya iso bakin gadon ya zauna sannan yace

” brother meke damun ka ne naga sai juyi kake?

tashi yayi ya zauna sannan yace kasan matsalata brother bana iya bacci ni d’aya.

murmushin takaice salis yayi sannan yace haydar al,amarin ka yana bani mamaki kai wai bakajin tsoron Allah ne, ga hanya mafi sauki kabi kaki sai anyi amma mgn kacei Allah ne ya daura maka toh naji Allah ne ya daura maka kayi aure mana, ko mata hudu ne kana iya hadawa.

hannu haydar ya dagawa salis haba wai kai sai ka rinka cewa nayi aure duka duka guda nawa nake ko 30 years ban hadaba fah.

kulewa salis yayi cikin fada yace kananufin sai mutun yakai 30 sannan zaiyi aure wani malamin ne ya fada maka?

nidai kawai ka rufamin asiri na dan fita da suba zandawo.

cikin fada salis yace wlh bazan rufama ba kana fita zan fadawa daddy

tsaki haydar yaja ya tura kanshi cikin bargo yana fadin muna fuki kawai

naji ni munafuki ne kaikuma dan iska me lalata yaran muta ne.

hankade bargon yaye ya duro ya cefkke wuyar rigar salis nan danan dabe ya kyaure atsakanin su.

ummi da yan matanta suna falo suna kallon wani film suka farajiyu hayaniyar su aguje suka nufi dakin.

salis naganin su ya tsaya cek amman haydar be daina kaimai doka ba.

ummi ce ta fara kokarin jan haydar tana cewa haydar duk yadda akayi kana shan kayan maye ka rasa dawa zakayi fada saida dan uwanka innalillahi wa ina ilaihir raju, un.

salis ne yazo ya rike ummi yana fadin ummi jeki abinki ya wuce taslim zahra kuje ku kwanta.

ummi kuka takeyi dan haka su fatima suka fara kuka.

shiko haydar sai maida numfashi yake yana hararar salis ya koma bakin gado ya zauna.

salis ko ganin ummi tana kuka hankalin shi ya tashi, yayi daya sanin biyewa haydar yace ummi dan Allah kije ki kwanta babu abinda zai sake faruwa.
suna fita haydar ya mike ya koma kujera ya zauna hannu yasa a aljihunshi ya dauko sigari ya kunna ya fara zuka yana fesar da da hayakin

 

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *