Advertisements
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
Tsuntsu Me Wayo
🕊🕊🕊🕊🕊
Storry & written
By
Fadeela Lamiɗo
PAGE 7
Advertisements
Zama yayi nesa da salis kanshi akasa dan duk abin shi yana tsoron daddy shi ahankali yace gani.
daddy ya dago ya kalleshi yasa hannu ya cire gilas din dake idon shi sannan yace me ya had’a ku ?
d’ago kai yayi ya kalli salis ya sake mayar da kanshi kasa yayi shiru.
Advertisements
ummi tace wai ba dakai ake mgn ba ne
bece komai ba kuma har yanzo kansa na kasa.
daddy yace kyale su tun da bazasu fada ba ai sunfi kusa, amman nasan haydar ne baidan gsky wata kila ka kule shi ne amman ni araina banason kuraba daki nafiso sai kunyi aure kowa ya samu abokiyar zama ko ya kuka gani?
haydar ne ya fara magana daddy ai ko munyi aure gida daya zamu zauna.
cikin sauri salis yace dawa dakai Allah ya kiyaye wlh ba zan zauna dakai ba.
sakin baki haydar yayi yana kallon salis sannan yace salis nine fah.
fuskar salis adaure yace kaidin fah ina hauka ne zan zauna dakai.
daga daddy har ummi basuji dadin maganar salis ba,
ummi ta juyo da kallon ta gurin salis tace
” ni bansan ka da fushi haka ba banji dadin mgnr ka ba idan baka zauna da dan uwan kaba dawa zaka zauna banajin dadin ganin ku cikin wannan halin dan Allah ku zauna lfy.
juyawa tayi gurin haydar ta harareshi sannan tace kai kuma kabashi hakuri dan nasan kaine mara gaskiya.
ahankali yace kayi hakuri in Allah ya yarda bazan kara ba.
har yanzon fuskar salis adaure take dan haka daddy ya kira su gaban shi kama hannun su yayi ya hada yace ya wuce kutashi ku tafi.
suna rike da hannun juna suka fita.
ummi ta dawo da kallonta gurin daddy sannan tace
” salis akwai hakuri amman idan ransa ya baci be iya fushi ba shiko haydar idan be nemi fitana ba bayajin dadi.
ajiyar zuciya daddy yayi sannan yace Allah ya shirye su.
haka rayuwa taci gaba da kasancewa agidan alhj kasim tsakanin salis da haydar yau ayi fada gobe ashirya zuwa anjjima kaga kamar basune suka yi ba.
kwanci tashi ba wuya wajan Allah dan yanzon kusan shekara fatima uku aku agidan, zuwa wannan lokacin shakuwa ce me karfe tsakanin fatima da salis.
yayin da haydar ya hura wutar kiyayar fatima azuciyar shi dan ko mgn bata hadasu da ita
duk da cewa ayanzon idan ka kalli fatima baza taba cewa tayi zaman kauye ba
acin wad’an nan shekarun so daya babanta ya kaita gurin mahaifiyar ta yanzon fatima tana ajin karshi na secondary sakamakon kwanya da Allah ya bata.
ta bangaren ummi kuwa wato mahaifiyar su haydar bata nunawa fatima wani banbanci tsakanin ta dasu haydar dan haka tana cikin kwanciyar hankali matsalar ta daya haydar.
ayanzun dai fatima ta zama cikekiyar budurwa komai na jikin ta ya fito sosai
fatima ce kwace jikin kakarta yadidko tana danna waya yayin da taslim tana gefe tana cin abinci suna fira da taslim.
sallaman alhj yusuf ya katsa musu hira, bayan yazaunaya kalli fatima dake jikin mahaifiyar shi yace ke ashe baki da hankali katuwarki dake zaki kwanta mata ajiki, yajuya ya kalli taslim sannan yace ke kuma bakiyi mata fada.
murmushi taslim tayi sannan tace baba tausa fah take mata.
hararanta yayi sannan yace wai ma me kukeyi agidan nan yau kusan 3 days kenan inaganin ku anan ku koma gidan ku mana.
taslim ce ta amasa munzo tayata zama ne ai yauma zamu wuce.
yace gara dai kutafi hira sukaci gaba dayi shi da yadidko.
zuwa cen su fatima suka fito cikin shirin ta fiya alhj yusuf ne ya kawosu har gida bayan sun gaisa da ummi ya wuce.
washegari fatima nata zuba ido taga shigowar salis har wan 12 na rana bata ganshi ba dan haka ta shiga neman layin shi saida ta kira su uku ba adauka ba dan haka tashiga damuwa.
lokacin da taslim ta kawo musu abincin rana kasa ci tayi tana juya cukalin.
taslim tace sister wai meke damun ki tun jiya naga duk kinyi wani iri.
meko ni bawani abunda yake damu na.
taslim shiru tayi taci gaba da cin abincin ta.
bayan sungama dakin ummi suka nufa suna shiga fatima tace
ummi wai yaya salis baya nanne?
eh bayanan bakuyi waya bane halan?
tace nakirashi yaki dagawa.
ummi tayi murmushi tace kila baya kusa da wayar ne, munyi waya danzon yace min suna hanya.
dariya taslim tayi tace dama shi yasa kika ki cin abinci wai ku soyayya kuke ne?
fatima ce ta harari taslim sannan tace wani irin soyayya.
ummi tace ke rabu da ita neman mgn ne da ita.
dariya taslim ta sakeyi sannan tace wlh ummi soyayya sukeyi.
daure fuska ummi tayi sannan tace wai taslim ina wasa dake ne nace kibar mgnr ina ruwanki da su.
hannu tasa ta rufe bakinta sannan tace na bari ummi.
daidai lokacin salis da haydar suka shigo bayan sun gaisa da ummi fatima gaida su haydar kadai ne ya amsa shima dan yaga ummi ne hakalin fatima ya kara tashi idonta ya cika da hawaye
ummi ta lura da halin da fatima take ciki bata dai ce komai ba dan bata faye son shiga tsakanin su ba
basu dade ba suka fita zuwa dakin su, fatima ko na gefe tayi tagumi.
ummi ta juya ta kalleta tace
fatima cire tagumin nan tashi maza ki kai musu abinci.
har ta dauki abincin ta tuna salis beson ya ganta babu hijjab dan haka ta koma dakin ummi ta dauki hijjab ta fita.
samun su tayi zaune haydar na nunawa salis wani abu acikin wayar shi sunata dariya aje abincin tayi tajuya har takai kofa haydar yace ke dauki ledar cen ki kaiwa ummi.
dawowa tayi ta dauka ta fita, kafin takai dakin ummi hayawaye ya fara zubo mata saida ta share hawayen ta shiga dakin ummi ta aje ledar ta koma kusa da taslim ta zauna ummi ta bita da kallo batace komai ba ta mike ta fita.
dakin su haydar ta shiga cikin mamaki
suke kallonta.
kallon salis tayi sannan tace waikai yaushe aka daura maka aure da fatima ne bansani ba
da mamaki yace ummi bangane me kk nufiba.
aidama bazaka gane ba kawai dan fatima ta tafi gidan hajiya bata fada makaba kk wannan fushin, matarka ce?
da sauri ya girgiza Kai.
ummi ta sake cewa toh karage wadan nan dokokin takasa mata suyi yawa kuma kazo ka rarasheta
adakin su ya sameta tana kwance tayi rufda ciki ahankali ya kira sunan ta amsawa tayi batare data waigo ba ya sake cewa toh tashin mana.
kintashi tayi dan batason yaga idon ta
gaban gadon yaje ya zauna yace zahara tashi mana kosai nakira ummi ne?
tanajin ya kira sunan ummi ta miki ta fara sakkowa daga gadon binta yayi da kallo dan rabon da ya ganta babu hijjabi ya manta sai yaga ta kara kyau bayan ta zauna ya kalleta yace wato abin harda su kuka?
cikin muryan kuka tace toh bakai bane kake fushi dani.
cikin sauri yace nabari indai nine banason nasake ganin hawayen ki
daidai lokacin haydar ya shigo dakin abakin kofa ya tsa dan haka salis ne kawai yaga shigowan shi
juyawa yayi barayin fatima yace tashi muje gurin ummi.
tana mikewa yace toh kisa hijjab mana.
buga kafa ta fara kamar karamar yarinya cikkin shagwaba tace ni gaskiya a,a nan da dakin ummi saina saka hiijjbi.
binta yayi da kallo zuwacen yayi murmushi yace ji abinda kikeyi saikace wata karamar yarinya
kara shagwabewa tayi
haydar ko dake bakin kofa tuni ya Fara rikicewa dan babu abinda yafi tayar mai da hankali kamar yaga mace tana wannan shagwaban, idon shi nakan kirjinta
salis kuwa ji yake kamar ya rungumita dan betabajin irin yanayin da yaji yau ba, juyawa yayi ya kalli haydar yace waikai wani gulman ne ya kawoka
sai alokacin fatima tasan da shigowan haydar juyar da kallonta tayi gareshi
yace ke dena kallona munafuka kawai me suffar aljanu
salis yakalleshi ya karasa gaban shi sannan yace muje
*******
da daddare duk yan gidan ne suka hadu a falon daddy suna hira zuwa cen daddy yace mun kusa shan biki agidan nan.
Ummita tace dama kuwa inason nama magana tunda su sunki yi .
cikin sauri salis yamike zaibar wajen. alhj yace inakuma zaka dawo ka zauna
bayan yazauna daddy yace yakamata kuyi aure salis kaida nake ma ganin ka kamar me hankali.
ummi tace alhaji ai haydar zakawa mgn shi yariga ya kama tashi gatanan kusa da kai duk da dai ba fada sukayi ba amman duk me hakali yasan sun amice da juna
murna ce ta kama daddy yace toh shine ni baki sanar min ba
dawai inajira ne su fada da bakin su gatanan ansa mata takunkumi zama da hijjab saikace matar liman
taslima ta kwashe da dariya shikuwa salis tunda ya dukar da kansa ya kasa dagowa fatima ma tana kudun dune cikin hajjabin ta
daddy yajuyar da kallon shi ga haydar yace kaifah
Sosa keya yayi sannan yace daddy ni ba yanzon ba.
sai yaushe?
daddy idan na shirya zanyi mgn
cikin fada daddy yace baka isaba rana daya zakuyi aure KO kaki KO kaso kanajina?
daga kai yayi sannan yace daddy inason zamuyi mgn amman su taslim su fita tukum
🕊🕊
Mmn Yazeed
2 comments