Advertisements
A Zamantakewar Soyayya: Shin Wace Ce Mace Tagari?
Masu salon Magana suna cewa, kowa yana son mai kyau sai dai idan bai samu ba.
Burin kowane namiji shi ne ya samu mace tagari.
Sai dai ga dukkan alamu wasu basu san ma wace ce mace tagari ba.
Advertisements
Idan ba ka san yanayi da halayen mace tagari ba.
Mace tagari, ita ce wacce ta mallaki wadannan halaye guda goma sha daya, kamar haka:
Advertisements
1-Idan mijinta ya kale ta zai ji farin ciki ya lullube shi.
2-Ita ce wacce take gaggawa wajen cika umurnin mijinta.
3-Ita ce wacce take matukar kiyaye duk abin da zai bata wa mijinta rai.
4-Ita ce wacce take dagewa wajen bautar Ubangijin ta.
5-Ita ce wacce ba ta wasa da duk wani hakki na mijinta.
6-Ita ce wacce duk lokacin da mijinta ya yi fushi, ba ta samun kwanciyar hankali har sai ta yardar da shi.
7-Ita ce wacce take kiyaye duk wani sirrin mijinta.
8-Ita ce wacce idan mijinta ba ya nan take kiyaye mutuncin kanta, da kuma dukiyar da ya bari a gida.
9-Ita ce wacce take kulawa da tarbiyyar mijinta da ’ya’yansa koda ba ita ce ta haife su ba.
10-Ita ce wacce take matukar girmama iyayen mijinta, kamar yadda take girmama nata iyayen kuma take kyautata wa ’yan uwansa ba tare da tsangwama ba.
11-Ita ce wacce take zama da makwabtanta da kishiyoyinta cikin tsoron Allah da kyautatawa, ko da su suna munana mata.
Wai-wai-wai! Garin dadi na nesa wai angulu ta leka masai! Duk macen da ta mallaki wadannan halaye, babu shakka ta mallaki halayen ’yan Aljanna. Allah Ka sanya mu kasance nagari a halayya da dabi’a, mazanmu da matanmu. Amin.
5 comments