Advertisements
WATA FITSARA🤔
By
Fadeela Lamido
Page 1
Advertisements
Bismillahir Rahamanir Rahim
……”Madaidaiciyar yariya ce zaune karkashin wasu bishiyoyi da aka kawata gidan dasu, duk da ciwo bata gama cika buduwarba amman sosai alamomin girma suka fara bayyana ajikinta, farace tas zaune kawai take ta zubawa katafaran gidan mahaifin nata ido, daga nesa take hangen gidan domin bishiyoyin sun danyi nisa da gidan, hawaye ne kawai yake zubo mata tana sharewa yayin data rasa yadda za’ayi ta tsaidasu”
“Ummee!! Ummee!!! Ina kika shiga??
Advertisements
“Jin muryan wadda ke kiran yasata saurin mikewa, cak kukan nata ya dauke tare da saurin share hawayen ta fara takowa jikin ta amatukar sanyaye”
“Tsaye tayi agabansa tana wasa da yatsunta tare da Satan kallon fuskan sa”
“Matsaikaicin mutum ne agabanta fari tas, dogo wadda yake ji da gayu, da alama bazai wuce shekaru 40 ba aduniya”
” Ido ya zubamata nawasu tsayon lokaci sannan yace, Ummee kin fara ko??
” Cikin sauri ta girgiza Kai tare da fadin a’a
” Idonsa ya kawar gafe ya tsurawa guri daya ido na tsayon lokaci sannan yace”
‘Kinajin dadin zama da ita kuwa?
“Cikin sauri tace, eh Abba tana da kirki sosai…..
“Toh meye matsalar Ummina kinsan hankalina natashi idan nasameki ahaka??
“Wasa ta shigayi da hannunta, kallon hannun yayi tare da saurin mika hannu ya rokota yana kallon hannun yace”
“Mamana gayamin, meye damuwar ki? duk abun da kike so indai inada ikon samu shi zan nemoshi, koda kuwa duk abun dana mallaka zai kare, nafison koda yaushe inga kina fara’a, kina nishadi kitamin shagwaba nikuma inta dariya har Allah ya kaimu lokacin da zaki girma ki Kai cikakkiyar budurwa na aurar dake ga mijin da yafi kowanne namiji sa’a aduniya
“Murmushi ta saki tare da fadawa jikin sa shikuma ya rungumeta yana me sunbatan goshinta tare da lumshe ido, ahankali ya fara takawa ya nufi hanyar da zata sadasa da gidan”
“Wata suka samu akofar falon zatakai kimanin shekara 26 cikin shiga ta alfarma tace”
” Baban Ummee Ina ka ganota??
“Tukan ya bude baki tace iskan nake sha Aunty”
“Lumshe ido Aunty tayi haba Ummee kin daga min hankali, irin wannan ai saiki fada min, karki karayin irin haka kinji……
“Hannu mutumin yai saurin daga mata, “Hade fuska yayi harya bude baki saikuma ya girgiza kansa tare da sakin murmushi yace, ai tace iska take sha, Mamana ce, kuma batason hayaniya”
“Sanyi jikin Aunty yayi, ahankali tace nagane Abban Ummee”
“Shikuwa Ummee ya kallah muje ki kwanta Mamana”
“Murmushi ta sakarwa Aunty harta fara takawa tace Aunty zan kwanta”
“Bayansu tabi da kallo Saida ta tattaro dauriyarta gaba daya tace atashi lafiya
“Misalin 10:30pm Ummee na kwance tsakiyar gadonta wannan karon ma kuke take harda shashsheka yayin da hawaye yake zubo mata sosai, ta dauki tsayon 1 hour sannan taji an turo kofarta ahankali”
” Zabura tayi ta Mike tare da saurin share hawayen”
“Kallo yabita dashi, jikinsa sanyi sosai ya karaso ya zauna abakin gadon hannun sa yasa ya tallabe kansa yayin da ya mika daya hannun sa ya rike hannun Ummee”
“Duk da cewa yabata baya tasan ya shiga cikin damuwa ne, tasan irin hukuncin da yake yankewa da zaran yazo ya sameta ta kasa bacci Dan haka tai saurin zamowa ta taba shi Abba kasan nayi baccin yamma shiyasa bacci yaki zuwa min”
“Ummee, nataba nuna miki baccin raina kuwa???
Girgiza Kai tayi da sauri sannan tace a’a
” ‘Dagowa yayi ya kalli kwayar idonta yace”
“Gaya min gaskiya meke damun ki”
“Wasa ta fara da yatsunta tare da satan kallon sa, ganin inda ya zuba mata idonsa ta tabbatar babu hanyar kaucewa bakinta ta fara motsawa cikin ‘yar siririyar muryarta tace”
Mamana”
“Wani irin kallo yaimata babu mamaki afuskansa, shiru yayi, yayin da itama ta kasa dago kanta, zuwa can ya dago ya kalleta yace”
“Maman ki?
“Kasa amsawa tayi ganin haka yasashi sake fadin, ya mukayi dake??
“Ahankali tace nace idan kayi aure bazan sake maganarta ba😢
” Dakau, yanzun meyasa kika yi???
“Cikin sanyin jiki tace, tunata kawai nake Abba”
“Hmmm kidaice bakyajin dadin zama da aunty, idan muna zaune mu biyu kita kuke kuke kina matsamin nayi aure dazaran nayi aure kuma saiki ce Maman ki?
“Wasa Ummee take da hannunta, ta kasa cewa komai” ganin haka Abban nata ya mike afusace harya Kai tsakiyar dakin tabishi da sauri ta rikesa”
“Abba karka saki Aunty, wlh tana da kirki sosai, komai nakeso tanai min, tafi duk sauran kirki”
“Ummee idan har zakici gaba da cewa Maman ki toh lallai zan rabo da ita dan banga amfaninta ba”
“Hawayene suka sakko mata tai saurin sharewa, Abba kayi hakuri dan Allah, rabon dana ganta fah Abba 3years kenan😭
“Waigowa yayi afusace, jin saukan zazzafan mari taji akumatun ta”
“Dafewa tayi wasu hawaye masu dumi suka sauko, cikin fada da hargowa yace”
,Akwai abun da kika nema kika rasa ne???, nasha gaya miki zan kashe duk abun Dana mallaka domin inga kina farin ciki amman baki da mgn sai Mamana, Mamana? Mamarki din banza, zaki damu mutane, kishiga hankalin ki kinji ko?
” Shigowan Aunty yasashi waigawa tare da komawa bakin gadon Ummee yazauna yana huci sosai”
“Alhaji Usman kayi hakuri, rike Ummee tayi tare da fadin, ke kuma Ummee ki guje bacin ransa kinji ko?, Abban ki nason ki sosai nasan haka tunkan in shigo gidan nan, share mata hawayen ta soma, yayin da Abban Ummee ya mike ransa bace yabar dakin”
Mikewa Aunty tayi ta rufe dakin, sannan ta dawo gurin Ummee dake kuka, har yanzun tace, Ummee?, Baya kaiki wajenta ne??
Kaita daga mata da sauri”
Shiru Aunty tayi zuwa can tace shekara nawa da rabuwan su ne yanzun??
Nima bansani ba amman tun Ina karama ne, da yana sawa akaini daga baya kuma ya bari”
“Kash😬 bazai yiyuba kuwa yakamata yana barin ki kiganta, ki kwantar da hankalin ki, zan shawo kansa ahankali domin yana da tsauri sosai”
“Dadi sosai Ummee taji cikin ranta hawayenta tafara sharewa ahankali tace nagode aunty”
********
“Wata matashiya ce zaune cikin daki, ‘yar kimanin shekaru 35 kwalliya take da alama Shirin fitane take, domin hannunta sunsha awarwaraye da zabunan gwalagwalai, duk da cewa gidane na talaka wadda keda rufin asiri saidai gwalagwalain jikin ta sun girmi gidan, shigar mutunci tayi, cikin buban leshi tare da katun mayafi, bazanyi mamaki ba idan akace bata taba aure ba, saidai ince andade ba’aiba, kyakyawa ce ta gaske, fara tas tare da dogon hancin ta da Dan madaidaicin bakin ta, takalmi take kokarin sakawa wata tazo aguje ta hankadeta ta shige dakin batare data waiwayo ba, bata gama rufe baki ba ta hango wasu tawagar maza da mata yaran gidan aguje yayin da kowa ke nemar maboya, basai ta tsaya tambaya ba Sarai ta gane gudunwa suke yi, zame gyalenta tayi tare da murmushi ta cire takalmin ta cikin gudu gudu ta shige sasan dake kusa da nasu”
A’a lafiyan ki kuwa Hadiza?, gotai gotai dake yara na gudu kema kinayi?,🤔 Kardai kema tsoron nasa kike?🤔
“Tana waiwayen bayanta ta zube takalmin ta kasa, warware gyalen tayi ta yafa sannan ta kalli tsohowar dake gabanta tace”
“Inna mutumin naki shu’umine, niba tsoronsa nake ba, kinsan sa ba kumya garaiba, zai iya cewa bazan fita ba narasa yadda akayi ya rainani haka”
” Tabe baki tsohuwar tayi, sannan tace, in dai Ahmad ne basai yagamar daga kansa ya kalle ba?
“Lallai Inna baki san halinsa bane, tafiya ta fara tare da fadin saidai na dawo kawai inna”
“Fita tayi gidan batare data waiwayi bayan ta ba, duk acikin gudun karta hadu dashi, gyaran murya taji bayanta nan gabanta yai saurin tsinkewa bude hancin ta tayi domin tabbatar da kamshin turaren sa”
” Duk da cewa ta gama tabbatarwa kanta shine din kebin bayanta taki waigawa tare da tattaro duk wata jarumta tata ta hade fuskanta”
” Ke!!!, Ina zaki??
” Batare da ta juyoba tace, inda ka aikini”
” Karki sake ki fita cikin layin nan nagaya miki, nabaki minti 5 ki dawo gida”
“Jin takunsa yasata waiwayawa cikin isa da takama yake takawa hannun sa zube cikin aljihun sa”
Tsaye tayi hartaga shigarsa gidan sannan tace”
Lallai yaron nan ya raina ni🤔
“Yatsanta tasa abaki ta ciza, wai yaron nan dame yake takama ne?, Ina zuwa yau dai zan warware rainin nan da yamin, wai ni yakecewa yabani 5 minute na koma gida?🤔🤔
“Juyawa tayi afusace batabi ta kofar data fitoba, ta babban kofar gidan ta shiga, tare da nufar falon Baba, dan ta tabbatar yana ciki yanzon”
*********
“Hadiza lafiyarki kuwa jifa inda kika fado babu sallama”
” Yi hakuri Baba, Ahmad ne yabani haushi Baba, karansa na kawo maka”
“Toh Bismillah meye ya faru”
” Sai alokacin ya dago sukayi ido biyu da Hadiza, kyakyawan saurayine ajin karshe kallon sa yasa kyaun Hadiza dishashewa cikin muryarsa me sanyi yace”
Ke!! Khadija?, koma kimana sallama…..
” Bazan koma ba, Baba kagani ko?, narasa yadda akayi ya rainani, wai ya ganni ahanya yake cemin yabani 5 minute na koma gida, ubanane Kai din ?
Dariya Baban nasu yayi sosai, yayin da wadda take mgn kansa ya tamke fuska kamar besan me take cewa ba, yadda ya cure fuska saika rantse baya dariya”
” Babba dan Allah karabani dashi, wlh ya takura min, ka gaya mishi niba sa’arshi bace ba Baba”
” Dariya Baba yasake yi sannan yace, kinaji Hadiza martabar gidan nan yake karewa, kuma banda abunki ai yayan ki ne, wata uku cur fa yabaki”
“Baba dan Allah ka bari zakasa ya dada rainani, wata uku aiba girma bane, shekaran mu daya ai”
“Hadiza ko rana daya aka haifeku ai yarigaki shan iskan duniya, Baba ya fadi yana kallon fuskan *Ahmad*…..
” Baba ka gaya mata har aurenta zan iya”
“Kwarai kuwa shima yafi komai sauki”
” Kallonsa tayi kamar bashi ne yai mgnr ba, cike da haushin shi tace
*Ahmad* zanci ubanka wlh”
Wani irin kallo yai mata cikin dibara ya kalli Baba sannan ya lumshe idonsa adaidai lukacin Hadiza ke fadin”
Baba nifa zuwa nayi ka ramani dashi, dan yana ganin yaban wata 3 kuma sai ya raina ni, wlh lokacin da akamin aure be wuce in aikeshi cefane ba, kuma nayi aure harna haihu shikuwa har yanzun beyi aure ba”
Murmushi Mahaifin nasu yayi Hadiza wannan shirmen naku baya karewa wuce kubamu guri mgn muke”
Fita tayi cike da baccin rai, saboda takaici dakinta ta koma ta kwanta”
Hawaye kawai taji yana zubo mata wadda daker ta iya tsaidasu”
Bayan kusan 3 hour da kwanciyarta taji an turo kofarta cikin sauri ta tashi zaune domin ko tantama Babu *Ahmad* ne”
Jikin bango ya jingina bayansa sannan dauki kafarsa daya ya daura jikin bangon tare da zuba hannunsa cikin aljihun sa yana kallonta yana lumshe ido tare da dan lasan lebensa ahankali”
Itama cikin sauri ta kawar da kanta aranta take fadin baka fini iya miskilanci ba”
Kusan 15 minute ya dauka ahaka sannan taji yace”
Khadija?, kikece zakici ubana ko??
Dagowa tayi ta kallesa amman ta kasa furta komai”
Hmmm, ubana yafi karfinki Khadija, saidai koni, kisameni akan gadona anjima da daddare sai mugani ko zaki iya cina”
“Innalillahi wa Inna ilaihir raju’un Ahmad dama wai har abin naka yakai haka?
Na wuce haka, ki daina mamaki ko tantama, idan kin biyoni daki zaki tabbatar da haka”
“Ficewa yayi, yayin da Hadiza ta tashi ta zauna, zufa taji yana tsatsafo mata lokaci guda”
Gaba daya ta rasa inda zata saka kanta mikewa kawai tayi tabi bayansa, hangosa tayi yayi nisa da alama sasan Inna ya nufa dan haka taita bin bayansa”
Kansa akasa ta samesa yana gaisawa da Inna, tsaye tayi bayansa idan ka gama zanyi mgn dakai Ahmad”
Nace miki ki sameni adaki anjima”
Mgn fa nace maka nake da ita ba wancen shirmen naka ba”
Ke kike shirmen ai”
Shikenan naji, kayi hakuri toh, haba Yayana ka fito muyi mgn dan Allah’
Jirani waje”
Fita bakin kofar tayi ta tsaya be jimaba ya fito, Ina jinki”
Kwalkwal tayi da ido cike da hawaye tare da hadiye wasu yawu masu dumi”
Khadija Ina Jin ki meya faru?, Kinason wani abu ne?, duk abun da yake damunki ki fada min, indai kudi nayi zan miki koda zan rasa duk abun Dana mallaka ne, Khadija inajin ki?
Samha ta fada ahankali”
Kanne idonsa daya yayi ya kalleta sosai sannan yace”
Samha??, ai kinfi kowa sanin halin da ake ciki, meye kike son nayi yanzun?
Kamar yadda muka saba adah…..
Yazun da da ba daya bane bazan iya wannan shirmen ba, da bana kasar wa kike takurawa???
Hakura nayi”
Kansa ya kyauda tare da fadin yanzon ma ai saiki yi hakurin”
Bazan iyaba Ahmad ka daure kaje”
Khadija yanzun bazan ganetaba, lokacin sunja itama nasan ta manceni”
Kacedai Bazaka ba kawai, banyi mamaiki ba daman naga duk idon ka ya soye banda fitara babu abonda ka koya”
Ai bakigama fitsara ba Khadija saina saki agadona kiga yadda zan dake”
Sosai gabanta ya fadi, wai Ahmad meyasa kake min irin wannan mgnr banza?
Saboda kinki aure shekara da shekaru”
Kai kayine dan ubanka?, garani nayi harna haihu kaikuwa fah?, Ko mutuwa nayi inada me min addu’a kai fah??
Hannunsa yasa cikin aljihun sa tare da fadin”
Aini ban dandana najiba”
Sosai Khadija ta kulle idonta jawur tace”
Duk iskancin dan iska zai gama yabarni Dan ni ba tsarar ka bace ba, wlh baka da kunya”
Ko zaki tsammin naki???😉
Sama da kasa ta kallesa tace kazo ka kwata”
Nakwata ko?, zakigani mara kunya kawai, idan har bani da kunya kema baki da ita, zaki gane haka daga ranar da kikai kunya”
Sannan inajan kunnen ki kiyi hankali idan ba hakaba ni zan aure ki”
Baki takama zuwa can tace laifina ne wlh dama abun da ya rage baka fada ba kenan, yau ka fada, nasan da wadda zan hadaka wlh daga yau bani baka”
Murmushi yayi sannan ya juya cikin takunsa na takama yabarta anan wajen”
*******
Washegari da safe Ahmad cikin shigar fararen kaya riga da wando da sukayi daidai da jikinsa bakar hula ya daura tare da bakin agogo sosai yaikyau kayan suka dace da jikinsa, farin fatarsa Kara fitowa tayi yayin da hularsa da sajensa kadaine baki ajikin sa, sai agogon sa, fuskan sa babu fara’a kamar yadda yasaba koda yaushe, bayan ya fito barayinsa ya rufe yayin dayai gyaran muryar wadda ta zame masa jiki”
Yayin da duk wani yaro dake gidan dazaran yaji gyaran muryansa yake shiga hankalin sa”
Ficewa yayi agidan batare da yaiwa kowa sallama ba, wata rantsatsiyar mota aka bude masa gidan baya ya shiga sannan sukabar unguwar”
Gaban wata tankasheshiyar makaranta suka tsaya driver ne ya fito tare da fadin ya sunanta??
*Fatima Usman*
Bejiba ya sake dawowa yace Oga wanne class?
Lumshe idon yayi yana lissafi cikin ransa zuwa can yace, S s 1
Bejima ba ya dawo wata yariya nabin bayansa da alama tsoro take, domin burin ta kawai taga wadda kenemanta”
Tundaga nesa ya hangota Masha Allah ya fada cikin ransa kammaninta nanan saima Dan Karan kyaudata Kara, fitowa yayi ya nufita”
Itako yariyar tsayawa tayi cak tare da zuba masa ido, zuwa can ta daga tsalle tare da fadin”
Uncle💃🏻💃🏻💃🏻
Murmushi yayi sannan ya karasa gabanta yayin data daka tsalle ta fada jikinsa”
Banda murmushi babu abun da Ahmad keyi sama ya nufi dagata tare da fadin wash😬
Cikin dariya tace”
Nayi nauyi ko uncle?
Sosaima kuwa Samha ba kadan ba haka kika girma🤔
Ban girma ba uncle kar Abbana yaji kasa yamin aure”
Auren lafiya Samha zomuje muyi hira”
Cikin motar suka kona yayin datai matshi da jikin sa shiko babu abun da yake sai shafa kanta yana fadin”
Ya karatu”
Lfy lau uncle, Ina Mamana??
Jimmm yayi sannan yace mamaki tana gida”
Ya bakazo da ita ba??
Zan wuce aiki daganan shiyasa amman wata rana zamuzo tare, Ina Babanki fah yana lfy??
Lafiya lau, amman uncle yaushe kadawo tunda ka tafi ban sake ganin Mama ba”
Wata rana Zaki ganta Samha yanzun muyi hira bani lbr shekaran ki nawa yanzun”
15years kawai uncle”
Lallai kin girma, Abban ki ya fara miki zancen aure ne??
A’a cewa dai yake inkara girma yamin aure, kasan me???
A’a fada min kawai”
Yace haddeden miji zan aura, dan gayu”
Eyeee, kice dan gaye zaki aura toh nikuma barin Gaya miki wani abu duk wani miji da zaki aura duk haduwarsa bazai kaiki kyauba kuma duk gayun sa bazai kaiki gayu ba”
Shiru tayi tana nazari zuwa can tace toh aini nafi son mekyau, kana nufin bazan samu wadda yakaika kyau ba??
Cikin ido ya kalleta sannan yace”
Ni?, Ina da kyau ne?
Eh mana uncle baka sani ba?, Sosai ma”
Bantabaji ba Samha, amman ma ko idashi bankaiki ba danni bantaba ganin kyau irin naki ba”
Kyalkyalewa tayi da dariya nasan Ina da kyau Abbana ma yace nafi Mama kyau”
Dan Allah?
Da gaske”
Kallonta Ahmad yaitayi na tsayon wani lokaci zuwa can yace”
Ingaya miki wani abu?
Eh Gaya min”
Tunda na tafi kullum sainayi mafarkin ki, wataran ingaki kwance kusa dani kina bacci wata rana inga kina bani abinci abaki ke wata rana ma har sai ingan……. Shiru yayi tare da shafa kansa sannan ya kyauda kansa gefe tare da fadin”
Fatima kefa kinyi mafarkina tunda na tafi?
Toh aini uncle idan nai mafarki kafin safiya na manta, kawai dai na Mamana ne ban mancewa amman Ina yawan tunaka har hawaye su zubo min”
Rungumeta yayi ajikinsa tare da sakin ajiyar Zuciya yana lumshe idonsa zuwa can ya dago ya sunbaceta agoshi tare da fadin”
Kije kicegaba da karatunki yanzun nasan an kusa tashi, idan nasake samun dama zan dawo”
Batarai tayi sosai uncle katafi dani ingaidata inason ganinta sosai”
Ina zanje dake Samha?, Kinason Babanki ya daureni ko?, Kiyi hakuri akai akai zan dinga lekowa, hawaye ya share mata sannan ya kwantar da ita kan kirjinsa ya saita wayarsa yana fadin, Oya yi murmushi”
Daker tayii yasamu yai masu selfie guda uku, sauka tayi yayin da take daga masa hannu hawaye naxubowa kumatunta”
Ahmad kuwa ji yayi duk zuciyarsa babu Dadi Fatima tayi girma sosai gwanin birgewa pic din dayai masu tare shida ita yaita kallo yana maimaitawa hakanan yaji yashiga wani irin yanayi wadda besan meye shiba, kawai dai yakasa daina kallon pic din dan hakama yacewa driver sa ya mayar dashi gida”
Kwanciya yayi wani irin sanyi yaitaji haka ya wuni adaki sallah kadai ke fitar dashi waje, washegari da safe yaji dan dama wayar Khadija ya Kira, nan danan ta dauka”
Jiya najiraki najiraki bakizo ba?, Yanzun ma gani na shirya ke kadai nake jira, gadona agyare yake, nikuma ashirye nake, kema kizo min ashirye dan mu banbance”
Jimmm tayi tama rasa me zatace masa, zuwa can ta kashe wayarta tana fadin”
Nashiga uku, Ahmad bashi da kuny….. Karan wayar dataji ya katseta, agabanta na faduwa ta dauka tare da fadin”
Kai Ahmad yanzun baka da kunya ko???
Eh, banda ita, kozaki ‘yan min naki??
Hmmm da ana tsammarwa dana tsammaka kodan in huta daga rashin kunyar ka”
Kingane kenan🤷🏽♂️ yanzun zakizo ne koni inzo??
Banson iskanci Ahmad ka shiga hankalin ka”
Kema ki shiga hankalin ki tsaki yaja sannan ya katse Kiran ya mike afusace ya fice ya nufi hanyar da zata sadashi da dakinta……..
One comment