Advertisements
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
page 11
Advertisements
Karfe 9 bakin gate din makarantar tai Mata, saidai ko shiga makarantar ba’a barta tayi ba duk yadda taso data shiga ya gagareta”
Gefe ta koma ta tsaya tana hangen makarantar yayin da ranta ya Kara bacci sunsha zuwa da Ahmad kuma soda yawa turawa yake azoda ita, jimm tayi bayan ta tuna cewa yana mikawa driver sa kudi saidai bazata iya sanin ko nawa bane dan haka ta sake dawowa akaro na biyu ta samu wadda ke tsaye bakin gate din, hannunta tasa cikin jaka ta ciro 5k tace ga wannan inason naga yariyar ne sosai kuma ba dadewa zanyi ba minti 15 yayi yawa”
Beko miko miko hannu ba yace”
Advertisements
Ranki shi dade dokane bani da wannan ikon ne, shikenan tam barin jira har atashi”
Hmmm ai Hajiya Babu yariyar da take fitowa nan wajen da kafarta ko wacce aciki ake daukanta”
Jimmm tayi sannan tace shikenan, matsawa tayi ta kasa barin wajen sosai take son ganin Samha ko Ahmad kiransa ta sakeyi wannan karon ya bude waya Amman be dauka ba har sau biyu”
Tsallaka titin tayi ta samu wani Dan guri ta zauna tana kallon Makarantar, kasancewar wajen babu mutane shuke shuke ne sai kuma motacin dake wucewa jefi jefi, tsintan kanta tayi da zubar da hawaye tana sharewa wani na sakkowa zuciyarta tai Mata zafi sosai, adaidai wannan lokacin Kiran Alhaji Kabiru ne ya shigo wayarta, tana ganin sunansa taja tsaki tare da fadin”
Nika rabu dani malam hankalina ba akwance yake ba, kanta rufe baki kiransa ya sake shigowa, wannan karon dauka tayi zuciyarta cike da damuwa tayi sallama”
Bayan ya amsa ta gaidasa sannan tace zan kiraka anjima akwai abun da nake”
Ok lafiya dai ko”
Lafiya lau anjima dai zan Kira ka”
Ok tam ba damuwa sai anjima kenan?
Ummm tace tare da katse waya ta sake kallon Makarantar”
Abun Mamaki🤔, motar Ahmad ne tsaya wajen yanzun nan, cikin sauri ta mike, wani tunani ne yazo Mata dan haka ta koma ta zauna”
Driver sa taga ya sakko, kudi taga ya mika masa sannan ya juya ya nufi makarantar
Sosai ta bude idonta tana kallo, abun Mamaki sallama taga yayi masu sannan ya shige abun sa”
******
Idon Ahmad akan gate din yayin da yake ta faman sauke ijiyan zuciya, kusan miti 12 sannan ya hango driver shikadai yana tahowa”
Ina take ?, Ahmad ya tambaya bayan ya iso gareshi”
Oga wlh taki zuwa”
Zaro ido Ahmad yayi sannan ya danyi murmushi yace’
Kanaji, kace mata tayi hakuri tazo taji wata mgn Ina sauri ne zan wuce Office”
Juyawa yayi bejima ba ya dawo tana bin bayansa saidai bata da walwala”
Bayan motar ta nufa yayin da Ahmad yai saurin budewa daga ciki sukai ido 4, cikin murmushi yake kallonta yayin data bata ranta kamar zatai kuka”
Shigo mana”
Ni anan zan tsaya”
Kallonta yayi sosai har yanzun fuskansa ciki da murmushi yace”
Baki huce ba har yanzun?, Daure ki shigo kiji wata mgn”
Kara matsowa tayi dan haka Ahmad yace, ni shigowa nace kiyi”
Bakinta a zunbure ta shigo”
Shiga tayi yayin daya matsa Mata ta zauna sosai sanan yace”
Na dade bangankin ba, sai naga kin kara kyau”
Fararen idanun ta ta bude ta kallesa cikin sigar harara”
Kawar dakai yayi cikin murmushi sannan yace”
Him’um irin wannan harara haka, mutum yana harara yai muni ke kyau kika kara”
Allah Uncle?
Da gaske Fatima”
Cewa fa kayi kyau na Kara, toh bakace bani da kyau ba???😔
Toh ke yadda kikayi??
Ai haka ka fada”
Aini zulayan ki nake, daman inaso ne inga yaya zakiyi kuma nagani, fushi da Uncle, da kin yi masa mgn”
Kanta tasa akasa, cikin wasa da hannunta Uncle to ni bana sone ace bani da Kyau”
Yanzun ke bakisan kina da kyau ba harsai kizauna kina bata ranki?, Yakamata kisan Wasa nake miki, domin ke kyanki a bayyane yake, da anganki anga kyau, basai an kura ido ba”
Cikin dariya tace Allah Uncle?
Sosai ma kuwa”
Toh Amman dai nafi Momy na kyau ko??
Wacece Momyn ki??
Mamana mana”
Mamanki ba Umma kike ce Mata ba?
Dukka Ina fada Uncle, ni Abbana yace nafita kyau”
Inama za’a hada Fatima, nesama”
Sakin jikinta tayi gaba daya sannan tace”
Toh Uncle Amman dai kaima Ina burgeka ko?
Kansa ya daga mata sosai ma kuwa Fatima, nifa Ina burgeki?
Matsowa tayi daf dashi eh man, aini daman burgeni kake’ kana da kyau Uncle?
Dan Allah?
Eh man, toh Uncle nuna min kyauna”
Dariya yayi kadan sannan yace”
Kice dai in nuna miki abun dayafi burge ni ko, kinga na farko dai bakin ki”
Taba bakin tayi”
Idon Ahmad akanta yace”
Sannan idon ki, sai kuma hanci”
Kai🙄 Uncle kumatuna fah?
Eh shima yana da kyau Amman ai nagama zanu kyau ?, Toh yanzun nima ki fada min nawa”
Cikin sauri takai hannun ta Kan sajen sa ta shafa tare da fadin”
Wannan ne”
Kallonta yayi sosai yace”
Kina nufin ni bani dakyau, ki rasa abun da zakice ya burgeki sai saje??
Toh Uncle ba gaskiya kake son na fada ba?
Hade fuska yayi sosai yace”
Yanzun ke baki, ido, hanci duk baya burgeki sai wannan abin, hannunsa yasa ya taba gemun sa cikin sigan tambaya yana me tsareta da idonsa”
Itama hannunta tasa tana bin sajen tana tabawa take fadin”
Eh man yafi kyau”
Aiko Zaki gani, haske shi zanyi kwatakwal”
Cikin dariya dariya kuka kuka tace”
Uncle karka aske wlh bazakai kyau ba”
Hannunsa yasa ya ruko hannuwanta yana fadin”
Bar tabani hakanan”
Hannunta tamaida Kan cinyarta tare da cigaba da kallon sa”
Dauke kansa yayi akanta tare da fadin”
Fatima yau baxo miki da komai ba, idan zan dawo me zan taho miki dashi?
Ni Uncle komai ma ka kawo min”
Shikenan zan wuce ki koma kici gaba da karatun ki”
Cikin karyar dakai tace”
Wlh Uncle kamar karka tafi”
Dan Allah?
Allah kuwan”
Hannunta ya rike kinaji kije kiyi karatun ki zan dawo, kinji”
Tam amman Uncle karka dade”
Bazan dade ba nima ai Ina son ganin ki”
Bude motar tayi ta fita yayin da take waiwayen sa, cikin murmushi yake daga Mata hannun harta kusa shiga makaranta taji ance Samha”
Da saurinta ta juyo ta rungume Khadija, Umma daman tare da Uncle kuke?🤔
A’a, ruko hannunta tayi zuwa gurin motar Ahmad wadda ganin Khadija ya dakata, Ahmad inason mgn dakai”
Yana kallon cikin idonta yace”
Toh Amman ki sallameta ta shiga ciki tukuna”
Batai musu ba matsawa tayi can gefe rike da Hannun Samha sannan tace”
Kullum Ahmad yake zuwa gurin ki?
A’a yana dai zuwa duk sanda yaga dama”
Ok tam ko yatava miki wata mgn??
Wacce mgnr Momy?
Eh inanufin yabaki lbrn zaiyi aure??
A’a ni bece min ba”
Toh me yace miki yau??
Jimmm Fatima tayi zuwa can tace”
Kawai cemin yayi inada kyau harna fiki”
Shiru Khadija tayi tsayon wani lokaci sannan tace”
Kinsan abun da nakeso dake?, Ki tsaya kiyi karatun ki da kyau ki daina sauraran sa, ko yazo karki sake zuwa”
Kai!!🙄 Mommy Uncle dinane fah”
Uncle din naki fah, ko kinason rayuwarki ta lalace abanza awofi ne?, Kunneta ta kama ta rike sosai harta saki Kara kinji abun da nace miki ko bakiji ba?
Dirowa Ahmad yayi cikin sauri daidai lokacin da Khadija da saki kunnen tare da fadin”
Maxa ki wuce kiban guri”
Kafin Ahmad ya karaso wajen Fatima ta shige dan haka ya daga Mata hannu, itama Fatima ranta bace cikin share hawaye ta dago masa hannun sannan ya juya ya shiga motar ya zauna”
Bakin motar Khadija ta tsaya tace”
Kai kuma Ahmad inason zamyi mgn dakai”
Inajin Khadija”
Kallon gabansa yake kawai yayin da Khadija ke tsaye abakin motar”
Ahmad wannan wanni irin iskanci ne, daren jiya ka hanani bacci, kasani adamuwa, komai yazama bayai min dadi nayi kuka harna gode Allah, Ahmad dan Allah kabarni mana hankalina ya kwanta, sabo da Allah inakai Inna Samha, tayi yaya dakai dan Allah?
Batare daya kalletaba yace”
Kibari Zaki gani, me kikeci nabaka nazuba?
Ahmad dan Allah narokeka kabari, kaiko kunya bakaji, kadubi Samha ka dubeka fah haba Ahmad”
Shiru yayi yana kallon gaban sa kawai zuwa can ta sake cewa”
Har wani shiru kake min yanzun, Ina mgn kana shareni, tayaya ma aure zai kasance tsakanin ka da Samha, kana matsayin ubanta tana ‘yarka, wannan ai abun kunya ne, asama Kai din karamin yaro ne wlh kalaman ka sun girmi Samha, ka iya batsa iri iri, akalamin ka wacce kalmace bansani ba, duk wata sabun rashin kunya abakin ka akejin sa, tsakani da Allah yaya zatayi dakai?
Zamansa ya gyara kawai cikin motar bece Mata komai ba”
Ahmad indai kanason azauna lfy kabar zancen nan bazai taba yiyuwa ba nagaya maka”
toh inbanda ma kanajin iskanci kace ni kake sona rana daya ka dawo kace Samha?, ta yi yaya dakai, tsoron ka nakeji Ahmad karka lalata min yariya😭
Ajiyan zuciya yayi sannan ya kalleta yace shikenan naji korafin ki zan kiyaye kalamaina, ko ince miki zan adanasu har sai an daura mana aure”
Jimmm tayi cikin zubar da hawaye😭😭 Ahmad ni so nake ka janye kwata kwata”
Yawu ya hadiye sannan yace”
Kije gida zamuyi mgn”
Anan zamuyi, gani gaka nasan bazakazo ba”
Jimmm yayi sannan yace yanzun me kike son akarshe”
Inason kabar zancen Samha”
Lumshe idonsa yayi sannan ya bude so akanta yace”
Khadija karki kureni nagaya miki kalaman da suke bakina”
Ka gayamin Ahmad duk wata kalama ta Fitsarar ka saidai ka maimaita min”
Ya isa haka Khadija, wadda kikaji sun isa sauran kibarsu na adawa Fatima”
Kagani ko Ahmad, yanzun Ina sauran wani mutunci anan gurin?, Hakan ne kake cewa zaka aure ‘yata kana min fitsara, Ina wani mutunci Inan wani darajawa?
Hmmm, kibari ki gani mana Wai me kikeci nabaka na zuba, badai girma kike so ba insha Allahu zan girmamaki fiye da Yadda kike tunani”
Ahmad bafa zai taba yiyuba, kamata girma bazata iya dakai ba”
Wai injiwa ya gaya miki???, Karkisa na fadi abun da bashikenan ba, koma me kike tunani kibari ai zaki gani a aikace ko?”
Zuciyata namin zafi Ahmad, Dana kalleka raina ke bacci, wanni Irinn fitsarace wannan Samha fah Ahmad, wadda tazomu yarka kaxam ubanta, takaika Ina????
Cikin kawar dakai yace kinata nanata mgn daya ne Khadija, kibar komai har bayan auren Zaki gani, banason nacika mgn yanzun saboda kina korafi akan kalamaina, dan Allah na rokeki waddan kalaman nawa kibarni na adawa Fatima, kowa ya tsaya iya hurumin sa”
Cikin tsananin tashin hankali tace Allah ya isa tsakanina dakai Ahmad dukan motar tayi tare da fashewa da kuka”
Murmushi yayi sannan ya sakko ya riketa ya bude dayan gefen yasata aciki ya rufe motar ya zagaya ya shiga”
Kuka takeyi sosai yayin da Ahmad keta kallon ta tare dajin nutsuwa na shigarsa”
Kofar gidan su ya tsaya sannan ya fita ya shiga ciki ganin inda yake abunsa cikin gadara ya Kara bawa Khadija haushi sosai”
Afusace ta bisa dakin Inna ta riskeshi cikin sauri ta dauki kujerar dake kusa da ita ta jefeshi yayin dayai saurin kaucewa ya daki kasa”
Afirgice Inna Yalwa tace Khadija kina dakai kuwa me yayi zafi?
Inna kubarni natsani Ahmad wlh, Inna natsane shi”
Subuhallahi me yayi zafi Khadija?
Ahmad tsaye yayi bayan Inna yana kallon inda Khadija ke hankoro ana tareta”
Cikin kuka take fadin”
Wai sabida tsabar rashin mutunci Inna yace yana Sona yanzun kuma Yadawo yace Wai Samha yake so?😭 Dan iska kawai gantalalle”‘
Mari Inna takai Mata sannan tace ki shiga hankalin ki Khadija, Ahmad din kike wulakantawa meya shiga tsakanin ku haka, nadauka zakifi kowa farin ciki da wannan abun?
Inna bana farin ciki, bakin ciki nake ji, kuma indai Ina numfashi baxa’ayi wannan auren ba, nasan Usman bazai taba baka ‘yarsaba Inna Ahmad wulakantani yake son yi saboda nace bazan aure shi ba”
Waigawa Inna tayi ta kalli Ahmad tace tokai Ahmad ya zakayi haka??
Inna kin yadda da zancen tane Wai, inda inason Khadija da tuni nasanar wa Daddy kamar yadda nayi wannan karon, ni bansan wannan lbrn nataba”
Kwarai kuwa toh Khadija meyasa haka?, Aiko bakiyiwa Ahmad hallarci ba, kishiga hankalin ki kikama mutuncin ki, juyawa Inna tayi ta kalli Ahmad tace jeka abun ka Ahmad zata ma sakko ne”
Yana fita Inna ta fita tabarta ita da Inna yalwa adakin tana fadin”
Kekuma sainaci mutuncin ki”
Dakin ya rage daga Inna Yalwa sai Khadija dake kuka kallonta innar tayi tace”
Kedai Khadija har yanzun baki da wayau, Ahmad ya gama dake, ji inda ya watsawa idonsa tuka yace besan zancen ba, Ina baki shawara ki fita sabgarsa kiyi auren ki kibarshi yagama abun daya tsara”
Cikin matsancin kuka tace”
Inna bazan iyaba, ni ayanzun bana kyaunar ganin Ahmad da Fatima kalaman sa basu da dadi, dan iskane lalata kawai zaiyi”
A’a Sam bazaiyi hakaba, Ina tabbatar miki tunda ya furta bazai bamu kunya ba wlh tunda ya furta da Gaske yake yi”
Aiko Inna indai Ina numfashi bazai auri Fatima ba”
Zaki aure shi ne??
Dana shiga uku Inna, dan Allah kibar wannan mgnr haramun ne “
Gudu yake kwararawa cikin matar
Yana fadin”
Nine gantalalle nine take Kira gantalalle, wayar Galadima ya Kira bayan ya dauka Ahmad sai huci yake”
Ahmad me yake faruwa”
Ina zamu hadu Galadima, waini Khadija take cewa gantalalle, nakasa hakuri Galadima…….
Mmn Yazeed
9 comments